Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 24

" Lapia kike kuwa? yanaga kamar arazane kike ko mafarki kikayine? girgiza Kai Nisha tayi tana fadi'n

"Aa"

"kode bakijin dadine because tunsafe nake ganinki so silent " Reeda tajefo mata tambaya, gyada Kai Nisha tayi tana fadi'n

"kaima ked'an ciyo" Nisha ta bawa fareeda amsa cikin kosawa da magana,

"Sorry kijira mu a motar bari muje muyi shopping din mudawo but bari na sauke miki glass din motar saboda iska yadinga shigo miki" gyada Kai Nisha takuma yimusu daga nan Reeda ta sauke mata glass din motar because dama itace ke driving dinsu daga suka fice daga motar suka nufi cikin babban plazan suka bar Nisha cikin morta wacce take ta faman sauke ajiyar zuciya idanunta suncika tab da k'walla karo na farko da tayi mafarkin umma wanda ya bata tsoro yakuma farkar da ita daga shagalan da tayi dan haka takudiri aniyar fita daga motar tagudu tashiga duniya neman mahaifinta, fitowa tayi daga motar tareda handbag dinta da phone din ta tasuma tafiya,

harta danyi nesa da plaza sekuma taja ta tsaya ganin wani mutum dake tin karota yana gudu yana haki, yana sanye cikin manyan kaya riga da wando but sede kayan sunci ubansu da dotti shikanshi mutumin yayi kura yayi futu futu dashi fiskarshi tayi baki sosai gashin kanshima tayi kura gakuma tacika akansa cunkus ga gemanya gaba daya de kallon daya zaka masa yuwa kaga tsohon mahaukaci , nanfa Nisha cikin tsoro tafarayin baya jikinta har rawa take nan tashaga waige waige da neman inda zatayi tunda da alamar gurin wannan mahaukacin yake yiyuwa, harta juya da gudu zata koma gun motarsu saitaji sautin wannan mutumin yana ihun neman agaji

"taimako! taimako jama'!! dan Allah a taimakamu suna bina zasu kamani sucutar dani dan Allah a taimakeni, cak Nisha tatsaya daga kokarin guduwan da take tamaida hankalinta ga mutum dan ganin ina yanufa still gurinta yanufu gadan gadan hakan yasa tarintsa ido gam jiki se bari yake, jin shiru yasa tabude ido bata ganshiba nan tashiga waige waige seda tajuyo bayanta tanganshi ya dukunkune face kanshi da hand dinshi jikinsa se kyarma yake nan tamaida kallonta daga hanyar dataga yafito nan made bakowa bakuma wanda yake binnashi 'to taimakon mai yake nema' jiyuwa tayi takalleshi tashiga tambayan shi,"

" malam suwaye ke binka bacin banga kowa dake biye dakai ba "?

"gasu can suna kuma biyoni" mutumin yabata amsa ba tareda ya dago face dinshiba sake duba hanyar tayi da kyau still de ba k'yallin kowa dan haka Nisha tasauke ajiyar zuciya takalli mutumin ciki da murmushi tace,

dago fiskarka ka kalli bakowa dake binka duba kagani, jin abunda tafad'i yasa mutumin cire hand din shiga face dinshi yashiga kyalla ido yana dube dube kafin ya sauke ajiyar zuciya yana dariya yana fadi'n,"

" Alhamdulillah wallahi natsira sundaina biyoni kasan cewan yanayin gari da hadari sosai nan take ruwa mai karfi ya sakko ganin haka yasa gaba kidayansu suka shiga neman mafaka nan taga mutumin ya watsa da gudu yanufi wata runfa ya shige domin fakewa Nisha itama cikin sauri tabi bayanshi tashige tana rawan sanyi tsayawa tayi tana kallon mutumin yasanya hanu yana taran ruwan yana kaiea baki da alamar yaji k'ishin ruwa seda yasha yakoshi sannan yashiga wanke fiskarshi datayi baki abar tsoro seda ya wanke face dinsa sannan yajiyu yakalli Nisha wacce ke gefe ta zuba masa na mujiya tana kallonshi, kauda kaiyayi yacigaba da wanke gabban jikinshi but jin motsin mutum kusa dashi yasa ya dakata ya kallo inda take idonta cika tab da kallo amma bakinta se murmushi yake yana barin cewa wani abin daker bakinta ya iya furta

"Abba?abbana kaine haka" Allah nagode maka Nisha tafad'i yayinda take matsowa gareshi da sauri yaja baya yana kallonta cike da mamaki amma bai iya cewa kalaba ganin haka yasa Nisha sake fadi'n,"

"Abba baka ganeni bane yarkacefa Nisha"tafad'i tana kuma tinkaroshi da kokarin fadawa jikinsa cikin murna but seyaga yasake ja dabaya 'to ko ta canzane bai iya ganetaba' tashiga tambayan kanta "

" Abba fa nice Nisha dinka ka kalleni da kyau nice , gamamakinta setaga ya watsa aguje yashigayin gudu itama cikin sauri tashiga bin bayanshi duk da ruwandq ake gudu yake sosai tamakar yaga wani abin tsoron itama Nishi se karayin saurin take but yamata nisa sosai , wata tsadaddiyar motane taga yaz o yasha gaban Abba aka bude murfin kofar motar aka kutsa abbanta ciki bataga ko suwayeba suka jashi csuka maidakofar suka rufe sukaja motar sukatafi dashi,

"Innalilahi wa'ina ilaihi rajuun"
Firgit Nisha ta tashi daga mafarkan da tashigayi tana kuma maimaita" inna lillahi wa'ina ilaihi rajuun abbanaaaaaaa!" bedroom din tashiga bi da kallo nan ta ganta wance kan gadon Aheel wanda tun kawoshi yakwanta yashiga rigimar sede su kwanta tare dalilin dayasa ta kwanata a domin ta samu yayi bacci seta sulale ta tafi but se bacci mai nauyi ya dauketa hardasu markin umma da Abba gaskiya mafarkin da tayi da Abbanata da irin halinda takaganshi ba karamin daga mata hankali yayiba, duk da sassanyan AC dake aiko cikin bedroom din but zuba take sosai kallon Aheel tayi wanda ya yabaje yanata sharan baccinsa wayarta tazaro tashiga duba time 4 na asuba zaro ido tayi tasakko daga bed din tanufi downstairs cikin sauri

ahanzarce take sakkowa daga benen koda ta karisa sakkowa se tsayawa tayi jinin jikinta yatsaya cak yabar aiki ganin Ajmal kwance saman duguwar sofa yana sanye cikin kyakykyawan jallabiyar shi yana karatun Qur'an tacikin phone dinshi , saka makon jiya da takawo Aheel basu ganshi a parlourn ba shima kuma Aheel bai nemi papan nashiba ya nace mata sede sukwana tare harda yar kukanshi karta tafi tabarshi atsorace tajuya cikin sauri zata koma atunaninta bai lura da itaba but setaji yace

"You! come back here, "nan Nisha tashiga mis mis da ido tana Shirin kuka ita tarasa wani tsautsayim bacci mai dugun zango ya kamata cikin side din Ajmal ahankali tashiga takowa, jikinta sai rawa yake gaba kidaya bata hayyacinta saboda mafarkin da tayi gaba daya hankalinta atashe take kuma tana cikin tsoro sosai hankalin takarisa inda yake tadurkusa saman carpet kanta na kasa gaba daya zufa yagama wanketa tas gashin kanta duk ya manne jikin face dinta yayinda da idonta kuwa hawayene fal ciki suna kokarin gangaruwa kumatunta sosai take sunkuyar dakai saboda hawayen dake kokarin zubu mata, kallo Ajmal ya tsareta dashi sosai yake bin sumar kanta da kallo baki wuluk dashi se wani shainin take

jin shiru baice komai ya tusata agaba yasa ta dago kai ahankali ta kai kallon ta gareshi daidai time din da sirarun hawaye suka sauka kuncinta ganin kallon da ya kafeta dashi kamar mai Shirin ganu wani abu a face dinta yasa tamaida kanta kasa tarasa shirun me Ajmal yayi yana kallonta ko wani irin kallone yake mata haka takasa ganewa kode kallon tuhuma yake mata na kasan cewa da tayi a side din shi,

"Aheel ne ya bukaci na tayashi kwana bayaso natafi nabarshi shine..,,, dakatar da ita yayi da ga surutan da kefaman jero masa because ba a bunda yakeda bukatan tambayar taba kenan dama yasan Aheel da fitina ayanda ya kwallafa rai da Auntynsa dayake fad'i wataran cewa zai ta dawo side din ma gabaki daya yasan halin d'ansa Ajmal yanason d'ansa sosai yanda Aheel keson Nisha yake kaunar kasancewa da ita da kuma kulawar da Nisha take bawa Aheel yasa Nisha tasamu sassauci daga tsana dakuma ki dayake mata abaya , shiyasama yanzu bai cika fargaban halinda Aheel yake ciki ba because yasan akoda yaushe tana kasancewa da shi kulawar da take bashi ko uwar data haifaishi Heelah bata bashi ,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.