Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 24
Wanka tayi sosai daga bisani ta fito ta naimi duguwar gown sannan ta sanya hijab tare da shinfida sallah tashiga jera salloli, karan ringin din wayar Fadeelah wata sai ta arlam na asuba shine ya tashesu daga nan nauyan baccin da suke, koda suka tashi idanuwan su ne ya sauka kan Nisha wacce ke zaune bisa sallaya bayan idar da sallolin ta tashiga yin lazumi ko waccen su mikewa tayi tasakko daga bed daya bayan daya sukayi alwala suka fito suma suka ta da sallah gefen Nisha, koda suka idar da sallah sukayi addu'a daga bisani suka mike Fadeelah tanufi bakin bed ta zauna yayin da Reeda ta ne mi saman sofa ta zauna gaba daya suka tusa Nisha a gaba suna kallo wacce kanta ke sun ku ye gaba daya yinin jiya bai musu dadi ba du ba da ya nayin da y'ar uwarsu ta kasance a ciki na rashin jin dadi ta wani ban ga re kuma ba karamin farin ciki suke da kasan cewar wannan lamari ba ko ba komai alak'a ya kara karfi tsakaninsu.
Jin shirun ko wannen su ya sa Nisha juyawo suka hada ido da su Fadeelah wanda ya sa su ka yi saurin sakar mata murmushi, itama Nisha murmushin ta mayar musu hade da jawo alqur'ani mai girma ta shiga karanta ko damuwar da ke zuciyarta zai kawo , tayi nisa cikin karatun yayinda kakejin yar siriruwar muryanta wanda ka ke ji kamar ana busa sarewa tsabar zakin muryar ahankali ta ke karatun saboda gudun shiga hakki, sai guraren 7:30 kafin ta samu daman tsagai tawa time din har su Reeda bacci ya sake kwashesu daga inda suka k'ishin gid'a ita Fadeelah ta G'yara kwanciyar saman bed itakuwa Reeda ta mike saman sofa sunata baccin su, ajiye alqur'ani Nisha tayi tare da ninke sallayan ta ya ye hijab din da tarufu ta nemi ma ya fi ta sanya bisa kanta tanufi hanyar fita daga bedroom din direct kitchen ta nufa ko zata tarar da barka cikin kitchen din but sai ta tarar ba ta ciki kamar bata fito ba kenan sometimes zaka iya tarar da ita guraren 6: ta na aikace aikace
Harta wu ce za ta koma sai kuma taji kamar shashshekar kuka ana jan akanci da surutai kasa kasa da ya ke kofar Barka yana gefe da kitchen shi ya sa Nisha ta jiyo sautin, ba da wani jin kiri ba Nisha ta matsa jikin door din Barka tare da murda handle din kofar ahankali bakin ta dauke da sallama ta tura kofar ta shiga, ko da Nisha ta shiga bedroom Barka a zaune ta sa me ta bisa sallaya tana addu'a yayin da ta daga hannuwa sama tana rokon Allah jin motsin shigowar mutum ya sa Barka saurin shafa addu'a tare da mutstsike hawayen face d'in ta tashiga k'irk'iro murmushi tana kallon Nisha yayin da ta kariso gefenta ta t'suguna
"Baba barka lapia kuwa mai yafaru?" Nisha ta tambaya tana kallon Barka wacce ta ke mammatse ido cikin damuwa,
"Bakomai y'ar nan lapia qalau na ke ya yau baki koma baccin ba kenan ya jikin naki ashe bakiji dadi ba Barka tashiga jero mata tambaya ta na murmushi da nuna ba wani da muwa da ke damun ta,
"I'm okay but sai na ke ga kamar kinada damuwa because ga face din ki ya nuna hakan"
"Lah ke kuwa y'ar nan mai zai da me ni a duniyar nan da ya wuce tsofa da tunanin mutuwa yau ko gobai" girgiza Kai kawai no Nisha tayi dan ba wai ta gamsu bane dan yanayin da taga Barka ciki ba ta saba ganin ta haka ba infact ma bata taba ganinta cikin damuwa ba balle harta kaiga zubar hawaye kullum cikin walwala da raha tareda wasa da dariya ta ke, d'a n numfasa wa Nisha tayi tana fadi'n
"Shikenan daman naje kitchen ne ban sa me ki ba shine nace bari na duba ki a bedroom din ki muje na ta ya ki aikin kafin Ammi ta fito idan kuma bakijin dadine sai na karba miki aikin
"Tab rufamin asiri y'ar nan kin gani qalau na ke yanda baki da koshin lapia ko aikin ban isa ki ta yani ba kije kiyi kwanciyar ki kihuta" tura baki Nisha tayi tare da b'ata fiska tana fad'in
"Nifa lapia ta kalau muje kawai Nisha tafad'i tare da juyawa tayi gaba Barka nabin bayanta tana murmushi hade da girgiza kai tana tunanin halin kirki irin na Nisha, karfe 8:30 Ammi tazo kitchen d'in ta tadadda Barka tare da Nisha sunyi nisa cikin aiki daga bakin door din kitchen din ta tsaya tana kallonsu ba k'aramin jin dadi ta yi ba kuma hankalinta ya k'ara kwanciyar ganin yanda Nisha ta sa ke sosai kai ka ce ba abunda ya faru hankali kwance su ke hiransu da Barka suna raha,
"Sannun ku da aiki" Ammi tafad'i time din da ta karisa shiga kitchen din duk juyo sukayi suna kallon Ammi wacce ta ke ta zuba murmushi kamar gonar auduga, cikin nishadi Barka tashiga dagawa Ammi gaisuwa sai da suka gaisa kafin Nisha tashiga mika nata gaisuwan
"Ina kwana antashi lapia"
"lapia qalau kyakykyawan y'ata ya kwarin jikin? ashe har kinfito kuma kika shiga wahalar da kanki"
"Wallahi kinga nima sai da na ce ta bari taje tayi kwanciyar ta ta huta amma taki kinsan mutumiyar ta ki akwai son aiki" Barka ta karbi maganar murmushi Ammi tayi gamida shafo gefen face d'in Nisha tana fadi'n
"Allah dai yamiki albarka but tafi wayance shashashon da basu da aiki sai bacci da danna phone zanga ya zasu kare da mazajen nasu idan basa bukatan y'an aiki kamar yayansu" dariya Barka tayi tana fad'in
"Aiko dai"
Nisha dai shiru tayi tana murmushi wanda bai kai zuwaci ba because yanzu bata da aikin da ya wuce murmushi yak'e ko dariyan dole saboda k'wata k'wata hankalinta ba akwance ya ke ba kwai dai danne zuciyarta ne karta nuna damuwarta afili tasasu cikin damuwar su ma, Ammi kallon Barka tayi tana fadi'n
"So fatan breakfast ya zama ready? but zanje nayi wanka na shirya asamar min da breakfast please"
"To ba damuwa yanzu kuwa" Barka ta amsa cikin b'arin jiki irina karb'an umar nin nan, daga haka Ammi ta juya ta fice daga kitchen d'in, ba bata lokaci Nisha da Barka suka shiga gabatar wa da Ammi breakfast d'in ta bisa dining table guraren 9 Nisha ta zame daga kitchen d'in ta fito tanufi hanyar fita daga parlourn.
Side din Ajmal ta nufa security da ke can gefe ganin Nisha na karisowa yasa ya mike da sauri ya shiga kiciniyar bude mata door din parlourn sai da tayi masa sannu kafin ta sa kafa tashige, shi kuwa security sai zuba murmushi yake harda na sayarwa kafin ya maida kofar ya rufe, bakowa cikin parlourn shiru kakeji kamar ba masu rayuwa ciki, direct kitchen ta nufa yau ta ci sa'a bubu uban tarkacen wanke wanke da Heelah ta saba tarawa cikin kitchen d'in da alamar jiya bata musu mahaukacin girkin da ta sa ba ba da yanzu kaga kitchen kaca kaca da tarin wanke wanke, ba tare da bata lokaci ba tashiga gyara kitchen d'in ta tsaftace shi daga bisani tashiga daurawa Ajmal breakfast mai dan sauki because ta gaji sosai,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.