Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 24

"Ki sha mana kin tsaya kina ta kallona kamar ba ki sanni ba "Nabilah ta fad'i gamida murmushi ta cigaba da shan coffee d'inta kafin itama Nisha ta kai bakinta jikin cup ta suma sha. dan kadan Nisha ta shaa ta sauke cup d'in ta sa ke Kai kallonta ga Nabilah ta na son jin dalilin da yasa ta jawo ta nan da kuma maganan da ta ce zasu tattauna, Nisha muryan Nabilah taji ta suma magana da cewa

" Tun bayan da naji tsakaniku da da ya Kamal na ji duk ki yai yan da na ke miki ya kau infact ma ko auranki ya bijiro da shi bazan wani damu sosai ba duk da kasan cewa ta macece mai kishi sosai especially akan abunda nakeso kuma nake matukar kauna ranar. farko da na fara ganinku tare a guest house d'in Daddy naji kishi sosai raina kuma ya baci harma nayi tsammanin wani abu tsakanin ku wanda kuma bai kamata nayi wani zargiba but time din idona yarufe naita fadan maganganun da bai da ce na fa de su ba akan zargin da ban da hujja ko tabbaci, Sam awance lokacin banason ya Kamal fada cikin yanayinda ya Kb yayi nisa aciki duk da abaya ya dauki wani ban gare irin na rayuwar Kb,.

Juyowa Nabilah tayi tana fiskanta Nisha ta cigaba da fadi'n

Kasan cewa na taba rayuwa cikin gida nan wanda shine sana diyar haduwata da Kamal time din da ya dawo daga American HAJIA ta sa aka shirya kayataccen waliman taron dawowar jikokinta dakuma murnar haduwar ahalinta, Kamal da KB makaranta daya suke karatu but ba wanda ya San Dan uwansa ko ya taba ganin hoton dan uwansa balle su shaida junansu.sai bayan haduwarsu aliyafar ne sannan ne suka shai da juna nima sannan ne na ga ya Kamal mukayi amanna da juna kasan cewa ina rayuwa cikin gidan su shiyasa muka shaku alakarmu ta kara karfi sosai wanda kowa ya fahimci hakan.

Kamal mutum ne mai fara'a sosai da sun wasa tsokana da ban nishadi wanda shiyasa na kara sa ke sosai na fara mance duk wata damuwa na Kamal ba kamar babban yayansu Wanda ke da fiskar fusatattu sam bayi da fara'a sai mutum ya ci sa'a yake iya tuzali da murmushi ko da dariyansa ballai ma ba na zaton yana murmushi balle wani dariya shiru yake maganan bata da mai Shi ba infact ma duk inda yake da hayaniya ko ake surutu wajan tofa baya zama yafi kadai tuwa shi ka dai Sam ba yi da son ha yaniya ni tsoronsa na ke ji sosai ko ido ba na yarda muhada da shi time d'in da nake rayuwa gidan nan but karfin hali irin na Aunty Heelah haka ta dinga cusa kanta cikin rayuwarsa da nuna sha'awar soyayyarta gare shi amma shi sam baya bata fiska ita kuwa Aunty Heelah sam babu kunya cikin idonuwanta zaman turai ya ba ta ta duk wata kunya da akasan ya mace na dashi to ga Aunty Heelah kam babu infact ma ba ta sanshiba.

Dabi'un da Aunty Heelah ke yi cusa kai ba kwarjini kiri kiri ba kunya haka take binshi wani sa'in abun har kunya ya ke bani ,ba ni kadai ba ma kusan kowa yana hankalce da tarkon da ta fad'a duk da sunsan wannan cusa kai da shige masa da ta ke baya waiwayarta ballai yasan halin da ta ke ciki because ba yida lokacinta harkan gabanshi kawai yake kamar baisan da lamarin ta ba amma Hajj mama duk ba ta yi la"akari da ta ban garansa ba yana da ra'ayinta ko aa hajia ta sa aka shirya bai konsu duba da yanda Aunty Heelah ta k'walla fa rai da shi ta nuna sha'awar so da kaunarta gareshi,.

Ya Ajmal duk da bai nuna interested akan Aunty Heelah ba but bai nuna ya na da ja ko musu a kan abunda HAJIA ke kokarin yi ba time d'in da Aunty Heelah ta kammala karatunta a kasar England aka tsaida ranar auransu already ya Ajmal ya Kammala masters d'in shi dan haka aka tsaida ranar auran tare da na Aunty Hafsatu kanwar ammi acewar hajia tunda har mahaifina zai iya cin amanarta yayi wani auran har asamu karuwa amma ace bai iya fada ma ta ba kuma bataji labari ba to yanzu bashida ikon da zai da katar da ita daga hukunci da tayanke na auran Aunty Hafsatu koya amince ko bai amince ba yana so ko baya so duk da abaya ya bijirewa hakan ba da son rantaba, bayanda da Aunty Hafsatu ta kuma gidanmu da zama amatsayin matar Abu to bayan wasu lokaci jima na koma gida na cigaba da da Auntynsa hafsatu.

Aunty Hafsatu tana da dadin zama sosai ta rike ni bisa amana tana kula Dani sosai tamkar wacce na fito daga cikinta kulawar da take ba ni ko mahaifiyata tana raye iya kulawar da zata ban kenan, ba kamar sanda na ke hanun mommy ba time d'in jinke gidan kamar ba na mahaifina ba kamar ba cikin gidan na girma ba gidan ya zam ta tamkar akan k'aya na ke saboda ita time din ko yan aiki hana mahifina tayi ya kawosu ninake komai a gidan ga tsan g'wama da kyara na zama tamkar bora acikin gidan, wanda kuwa ba haka ta kewa su Aunty Heelah da yaya KB ba duk da nayi farin ciki da ban kasance ta bani irin tarbiyan da ta taso da yayanta ciki ba gaba daya ta ga ma sangartasu ba ta k'wab'ansu duk abunda suke so shi sukeyi walau mai kyau ko mara kyau .

Sun kuyar da kai Nabilah tayi saboda wani hawayen da ke kokarin zubu mata na tuna wahalar da ta sha ahanun mommy gaba daya Nisha jikinta sai ya kara yin sanyi gaba daya tausayin Nabilah ya kamata wato kowa da yanda ake jarabashi arayuwa, parlourn ne ya dau shiru ba wanda ya yi magana cikin su jim kadan Nabilah takuma dagowa ta kalli Nisha tana fadi'n

Kiyi hakuri bana kiraki Dan na baki labari ko surutu abunda ya shafi rayuwa ta bane sai d'an kinzama daya daga cikin family gidan nan kina da right din kisan wani ban garai da yashafi ahalin nan da kuma yanda rayuwar familyn ke gudana, because Kamal ya bani labarin komai daran jiya ganin yanda hankalinsa ya tashi sosai ya kasa nitsuwa wanda nima yasa nakasa nitsuwar hankalina ya kasa kwanciya har sai da ya labar ta min abunda ke faruwa matsayinsa na mijina kwantar masa da hankali tare da bashi shawarwarin da zai Kara matar dashi damuwarsa ya manta da ya cireki daga zuciyarsa ya manta ya ta bata jin wani abunda ya Dan ganci soyayya da ke because ke ba rabunsa bace ke matar yayansa ne yanzu alkar ku zaima yanzu yan uwan ta ka ne kawai ba batun so ko wani kauna ba.

Sannan ke ma ina mai baki shawara ki mance da Kamal ki fiskanci rayuwa auran da zaki fara da wanda zai zama shine jigo yanzu cikin rayuwarki duk da kin tsinci rayuwar auranki ta wani siga da ban kuma ina tayiki alhinin hakan ina kuma taya ki bankincikin kasan cewar Aunty Heelah amatsayin wacce zaki zauna da mijin ta ku zama kishiyoyin juna.,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.