Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 24

_______Nasan halin yar uwata sosai tamakar yanda nasan yunwa cikina ina mai baki shawara ki dage da addu'a sosai har lokacin da Allah yasa ta fahimci ma tsayinki awajan mijinta , ina fatan Allah ya yayyafawa lamarin ruwan sanye komai ya tafi daidai cikin kwanciyar hankali because nasan Aunty Heelah da kuma hali irin na ta, akarshe nima zan sanyaki cikin addu'ata kuma ina rokonki da kidaina guduna haka nan nima ki dauke tamkar yanda kika dauki su Reeda nima ki daukine daya daga cikinsu because muriga munzama daya yanzu Nabilah ta fad'i ta na riko hannayen Nisha,.

jiki a sanyaye Nisha g'yada kai tare da sunnar da kai kasa maganganun Nabilah duk ya sa ke kashe mata jiki tsoron ta ya k'araru matuk'a bata san ya zata fara fiskantar wannan k'addaran auran ba sam ji ta ke ina ma duk wanda nan abubuwan da ke faruwa da ita ya kasan ce mafarkine ba gaskiya ba da kuwa inta farka bazata sake komawa wannan baccin ba girjinta sai bugun goma goma yake da ga Heelah har mijin nata tsoron su ta ke ballai kuma yanzu da ta ke kokarin fara rayuwa cikinsu wani irin yanayin zata tsinci kanta a tare da su a tuna ninta dukansu babu mai rang'wamen fiskar da zataji saukin mu'amala dashi. rintsa ido idanu Nisha tayi tana furzar da wani irin zazzafan ajiyar zuciya ta shiga karanto wasu addu'oi a hankali tana jin zuciyarta dan sanyi kadan kad'an kamar ana yayyafa mata ruwan sanyi,

ganin halinda da ta shiga yasa Nisha ta bawa Nabilah tausayi nan ta cigaba da tausan ta tare da bata shawarwari masu kyau wadan da zasu amfane ta, haka wunin yau Nisha ta yi shi cikin sanyin jiki har wani zazzabi zazzabi ta ke ji ya dawo mata, da dare bayan sun kammala dinner sun zauna bisa parlour suna fira kamar yanda suka saba, wanda nan Ammi ke shaida wa su fareeda ce wa Saturday and Sunday suna da private class na koyan girke-girken zamani kasancewar bikinsu yana ta karatuwa kuma ba abunda suka iya na ciman zamani ballai na gargajiya wacce zasu nishadantar da mazajensu Dan haka ta yanke shawaran kaisu akoya musu delicious kala kala saboda afita kunya shi ya sa ta ware wadan nan kuwanakin because sauran lokutan basu da lokaci saboda karatunsu, ranar murana gurin su Fadeelah ba a cewa komai.

Suna tsaka da firanne wayar Nisha ta shi ga k'ara alamar kira nan Nisha ta kalli screen d'in wayar salma ce ke kira duk duk da kasan cewar tun safiyar ranar ta ke ganin k'iran ta but takasa dagawa because bazata iya magana dan ta San da ta fara magana zata fashe da kuka shi ya sa ta ke gudun ta d'aga mata hankali ana tsaka da shirin bikinta dan ta san duk wani damuwarta damuwar salma ne haka duk damuwar salma da muwarta ne sun d'auki juna tamkar jini d'aya sam basu yi tsammanin rabuwa haka lokaci daya ba, abaya da suke rayuwa tare basa kwana d'aya ba su ga junansu ba ba tare da dalili mai karfi ba amma gashi yanzu sun rabu sai ayi wata basu ga junaba sai awaya kawai suke haduwa , yan zunma kifa wayar ta yi gefenta kanta kasa ta ci gaba da murza Dan ya tsanta tana ta karatun zuci

"Ba kiran ki ake awayar bane?" Hajia ta tambaya tana kallon Nisha, Nisha dagowa tayi ahankali ta kalli Hajia gamida g'yada mata kai tana fadi'n

"Eh kirane "

"Waye ya ke kira ki ? d'auka ki je bedroom ki amsa kiran mana kar mu da meki da ha yaniyar mu" ba musu Nisha ta dauki phone d'inta ta nufi bedroom tareda neman guri ta zauna ta shiga kiran salma time d'in idanunta haar sun kawo ruwa, ba wani dugun rigin carab salma ta dauki wayar ta suma magana.

"Haba Nisha why ba kya picking call d'in sai kinga dama duk kinsa hankalina ya tashi wai mai take faruwane "salma ta shiga jerowa da Nisha tambayoyi dan ko sallama ba tayi ba.

"Bakomai" Nisha ta amsa mata can kasan ma koshinta,

"Ko bazaki samu zuwa bikin nawa bane kika kasa fad'a min"

"Eh " Nisha ta ce time d'in da ta ke dab da fashewa da kuka

shiru salma tayi na Dan wani lokaci ba wanda yace kala acikinsu.

"Nisha kodai dunyar tayi miki dad'in da zaki iya watsi danine haka daga jiya zuwa yau na kiraki ya fi akirga but ba kya picking yanzu koma naji yanzu kuma da muke magana sai na fahimci kamar baki son magana na da meki , ko dai wani laifin na miki duk da nasan yanzu munyi nisa da juna bana tunanin hakan, dan wani abune ya ke faruwa da ke ya kamata ki fad'a min because ni abokiyar fad'a wa matsalar ki da damuwarki ne ko abunda ya shafeki please ki fad'a min in wani abunne ke da munki" nan fa taji Nisha saki wani kuka waiwai kamar karamar yarinya, ba k'aramin ta shin hankali salma ta shiga ba jin yanda Nisha komai ta ke kuka kamar wata k'araman baby nan Salma ta rude ta shiga tambayarta ba sanin kukan but ba amsa, tambayar duniyar nan salma tayiwa Nisha amma ta ki kulata, nan Salma ta ka tse wayar daga haka Nisha ta kwanta saman bed d'in ta ci gaba da koke koken nata a hankali ba tare da sautin ya fito anlura da halinda ta ke ciki ba.

Sai da ta yi kukan ya isheta kafin ta g'yara kwanciya dan ko kayan jikinta ba tasamu daman canzawa ba taja blanket ta rintsa ido tana sauke ajiyar zuciya kanta harya suma ciyo saboda kukan da ta sha yau ko tunanin kiran Ajmal taji ko yana da bukatan wani abin duk da tasan bai cika bukatan wani abin da dare ba infact ma bai cika dawowa da wuri ba koma ba dan hakan ba bazata bi ta kanshi ba, ta masa na Allah duk da ba wani koshin lapia garai ta ba, da safen nan ba k'abisa da aramin gajiya tayi ba ga kuma haushinda ya kuma bata tana cikin wannan yanayin har bacci b'arawo ya sace ta, washe gari karfe gusan 10 Nisha ta kammala ta shiga jerawa dining table kamar yanda ta sa ba parlourn shiru sai karan TV da ya ke ta aiki sai kuma ita da ta ke ta faman Kai kawo tsakanin kitchen da dining area tana shirya breakfast ,.

Nisha harta gama komai ta kimtsa ko ina ba kwalkiyan ko mutum daya da taji duk da tayi tsammanin tun shigowa ta zata ci karo da Heelah ko ta ji motsin ta but sai ta ga sabanin haka wanda hakanne ya bata daman yin aikinta cikin na tsuwa, ta nufi upstairs direct bedroom d'in Ajmal ta nufa ta g'yara masa kamar yanda yayi korafi, tana zuwa bakin door d'in ta shiga yin nocking a hankali bugu daya zuwa biyu ba ayi magana ba hakan yasa ta murda handle door d'in ta ku tsa kai bakinta dauke da sallama ta karisa shiga, .

bedroom din ba kowa ciki duk da anrage light d'in dakin ba komai ta ke iya gani ba d'an haka ta karisa cikin tsakiyar dakin ta nufi switch light d'in ta kunna nan haske mai kyau ya gauraye bedroom d'in nan fa idonta ya hango mata Aheel da ke kwance yana sharan bacci yana rugume da pillow kamar kamar zai shige ciki ya rungume shi tsam ajikinshi Nisha ba ta san sanda ta saki murmushi ba tana mai kallon kyakykyawan face d'in Aheel mai kaman antsaga kara da papanshi, karisawa tayi ta zauna bisa bakin lallausan bed d'in sai da ta lumshe ido tsabar taushi da laushin bed din, cike da murmushi Nisha ta kai hannu ta shafo gefen face d'in Aheel, kamar wanda ya yake jira a taba shi aiko tar ya bude idonsa bisa face d'in Nisha Aheel na ganij Nisha zaune gefen shi tana ta zuba masa murmushi, shima washe mata baki ya shigayi cike da farin ciki ganinta ya fad'a jikinta tare da rungume ta, cikin farin ciki da kyawan yaron Nisha ta dinga shafa bayanshi a hankali kafin ta dan zame jikinta daga nasa ta shiga tambayarshi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.