Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 8 of 24
ahankali yadan zame jikinsa ya mirgina yajuya mata baya because kwata kwata baya son farkawanka ita kuma heelah takasa ganewa itade heelah har kullum mamaki ajmal kebata seyaita zille mata yana gudunta se yanzu take kokarin yarda da kalamun faruk nacewa mijinta bayida maraba da mace da yar uwarta mace take rayuwa gashide aido namiji har namiji but abu yake sekace mace anya kalau yake kuwa? ita tarasa gane wannan lamarin ace kullum ita ke nanike dashi yana zille mata se yaga dama tukun yake iya amincewa da ita gaskiya tagaji da abunda Ajmal yake mata na guje mata da yake
itade tasan ba kazama bace tana tsafta daide gwargwado to meye matsalar ne? wani kuka takawo tasake harda shashsheka cikin hanzari tamike daga bed din tafice daga bedroom din da gudu tana kuka,
Ajmal najin fitan Heelah cikin yanayi kuka yasa ya mike daga kwanciyar da yayi yakoma ya jingina da jikiin bed , shiru yadanyi nawani lokaci yadau tsawan mintuna ahaka kafin yamike yasakko daga bed din yafito daga bedroom din shima , bedroom din aheel yanufa yana zuwa yatura door din yashiga, kwance yasamu Dan nasa yarungume wata big teddy bear yana ta baccinsa cikin kwanciyar hankali karisawa yayi yazauna gefen gadon yashafo gefen fiskan dan nasa yanajin sonsa da kwanarsa yana kara shiganshi, daga nan kuma yamike ya gyara masa rufowan blanket din daga bisani yarage masa hasken light din bedroom din yarufo masa door É—in ,
bedroom din heelah ajmal ya nufa yana shiga yasameta tagama kukanta tahakura har bacci barawo yasaceta gaba daya jiyayi ba dadi tabashi tausayi , duk da bayajin karfi ajikinsa daniyar rarrashinta yazo ya kuma bata abunda tanema to ganin cewa tayi bacci yasa ya gyaleta yakashe musu light din dakin ya haye saman bed dinta ya kwanta tabayanta ya janyu musu blanket yarufe su daga haka yarintsa ido, bajimawa shima bacci yayi awungaba da shi,
tun bayanda Nisha tayi kiran ajmal a phone kusan sau 2 baiyi picking ba yasa ta hakura dasake kira takuma bedroom din su takwanta cikin yanayi na sanyin jiki da rashin jin dadi, dakuma kulla aniyar gobe da safe zataje taga yanayin jikin nasa
__________________________________
washe gari da safe 8:00 Nisha tayi wankanta tashirya cikin shirinta me kyau kananun kaya riga t shirt mai dogon hanu pink color mai laushi tana dauke da adon me alamar heart agaban rigar , se dogon skirt black se hulan dake kanta shima black tayi matukar kyau da ita
fitowa tayi daga bedroom din tabarsu fadeelah da reeda da suketa baccinsu kamar yanda suka saba because dama su basu cika tashin safe dawuriba inba school suke dashiba suna sallahn asuba suke komawa sukwanta bacci, direct side din shi tanufa seda suka gaisa da securityn dake tsaye wajan kamar yanda suka saba gaisuwa yabude mata door din tashiga,
koda tashigo parlourn azaune ta iske heelah bisa sofa da bowl din cornflakes tana sha gefe kuwa saman table plate ne dauke da kayan snacks tana ci tadaura daya kan daya tana kallon tv jin motsin shigowar Nisha yasa tamaida hankalinta gareta , gamida hararota yayinda take karisowa cikin parlourn,"
barka da safiya abunda Nisha tafad'i kenan kanta kasa tana kokarin karisawa da nufin tafiya kitchen,"
Hee uwar iyayi dakata! Heelah tafad'i tana wurgawa Nisha harara, Nisha tsayawa tayi tana kallonta ba tareda tace komai ba, mikewa heelah tayi tana kallon Nisha sama da kasa kafin ta tabe baki tana fadi'n,"
yau uban gidan naki baya bukatan komai already yayi breakfast dinshi yayi fitarsa but zaki iya shiga kitchen akwai wasu wanke wanken da ban iyayiba kihada da wadannan plate da bowl din kitafi dasu daga haka Heelah takuma watsawa Nisha wani hararan kafin tamatsa daga wajan tanufi upstairs tabar Nisha tsaye awajan tana binta da kallo tareda takaici umarni da take bata hala yar aikinta takeson maida ita ,
Nisha hartayi niyar barin parlourn sekuma tafasa takai hanu tadauki kayan tarkacen da Heelah tayi amfani dasu tanufi kitchen, tunda tashiga kitchen din take karewa gurin kallon ganin yanda akayi kaca kace dashi ga tarkacen wanke wanke da heelah ta tarashi agurin bata iya wankesuba har kullum Nisha mamakin Heelah take da irin lalacin da takedashi amatsayin ta na mace kwata kwata ba tsabtace muhalli ba karamin fama papan Aheel yake da Heelah, bawani bata time Nisha tashiga kimtsa kitchen duk wani abunda kitchen din dake bukata Nisha seda ta mishi ta gyara ta tsaftace, tana kammalawa Nisha tafito daga kitchen din tana yarfe zufar face dinta because ba karamin gajiya tayiba , daidai time din da aka turo door din a parlourn,
Ajmal ne yashigo tareda kamal Wanda suka dawo daga raka Daddy airport, suna tafe cike da nishadi kamal ganin Nisha cikin parlourn Ajmal se raba ido take ga zufa duk ya wanke mata face se yashiga mamakin ganinta ita nan suka karisa shigowa cikikn parlourn suka zauna bisa kujera still kamal se kallon Nisha take shikuwa Ajmal kamar baima san da tsayuwarta jikin parlourn ba Nisha matsowa tayi tashiga daga musu gaisuwa kamal yane ya amsa da ganan Nisha tashiga tambayan Ajmal ya jikinsa kansa sunkuye hankalinsa yana kan phone dinsa ya amsa mata da fadi'n,"
Alhamdulillaha! ba tareda ya kalli inda takeba dan tabe baki Nisha da mamakin kamar ba ita yanemi taimako gurin taba har numfashi fashinta yaso tsayawa sobada shi amma yanzu tana tab bayarshi yajiki kamar bazai amsaba balle ya dago ya kalli inda tak yanzu da lapia tasamu za acigaba da halin Nisha sid'i sid'i Nisha tasamu tafice daga parlourn kamal se waiwayanta yake harta fice, "
Bro meyasameka? Kamal ya tambayi y'ay'an nasu cikin nuna kulawa da damuwa, dagowa ajmal yayi ya kalli kanin nasa tareda sakar masa murmushi yana fadi'n,
"Nothing wani dan zazzabi nayi but now I'm okay, cikin sanyin murya tareda sauke ajiyar zuciya Kamal yace ,"
Masha Allah , Allah yakara lpy bro "
Amin!
Ajmal ya amsa fiskarsa dauke da murmushi ,"
yaushe zaka koma office kaci gaba da aiki ko baka gama hutawaba ? Ajmal ya tambaya yana kallon Kamal, dan shafo gefen wuyansa Kamal yayi yana yar murmushi yace ,"
am da yau nakeda niyar komawa but nabari se zuwa gobe because akwai dan Shirin da nake kamal yabashi amsa cikin girmamawa ,"
That's good daga haka Ajmal yamaida hankalinsa ga phone din shi but ya lura da yanda kamal yaketa muzurai kamar bakinsa yana bukatan cewa wani abun se wani nuke nuke yake ,"
Eheem ina jinka kace kanaso muyi wata magana but kayi shiru kuma what happened? Ajmal ya kuma tambayan Kamal yayinda ya ajiye phone din shi saman table din parlourn yana kallon Kamal tareda sauraron shi, Kamal bude baki yayi daniyar magana but jin rurin karan wayan Ajmal yasashi dakatawa daga abunda yakeson fadi'n, Ajmal hanu yakai yadauki wayan nashi ba tareda ya daga Kiran ba ya kalli Kamal yana fadi'n,"
I'm very sorry zan fita office yanzu but zan nemeka any time , "
Okay bro
kamal yafad'i because dama maganar dayazo dashi nauyin fadawa yayan nasa yake dan haka Kamal yayiwa Ajmal sallama yafice daga parlourn, Ajmal yana ganin fitar Kamal shima ya mike yanufi upstairs bedroom din shi yashiga daga nan yashiga cire kayan jikinsa yanemi towel yadaura a waist dinshi yanufi toilet wanka yayi yafito yasuma shiryawa cikin shiga maikyau black suit yayi kyau matuka yasanya black glass da takalmi se wani agogon gold ta hanu daya sanya kyau kan kyau abun ba amagana, fitowa yayi daga bedroom din shi yanufi downstairs daga bisani yafice izuwa haraban gidan parking space yanufa yashiga daya daga cikin motocinsa white color tsadaddiyar hadaddiya abun kallo da ban sha'awa me gadi yana ganin fitowan Ajmal cikin barin jiki ya bude masa geat Ajmal yayiwa motarsa key yasa kai yafiice,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.