Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 24
Aheel raunin mahaifinshine baiso alakar Aheel da Nisha tayi nisa haka bas because Ajmal hankalisa Sam yakasa kwanciya da yarinyar yakasa karbarta kamar yanda agdn suka karbeta hanu biyu wani tunani yake da ban akanta da kuma shakku , wani lokacin kuma tausayi take bashi yanda take wasu abubuwan cikin tsoro da rawar jiki kamar mara gaskiya wannan yana daya daga cikin abunda yasa yakeda alamar tambaya akanta,
"you can go"
abunda Ajmal yace kenan , kamar jira take because tagaji daga dukawan da tayi dan haka cikin sauri tamike tafice taname goge hawayen face dinta , lumshe ido yayi tareda tunanin cikin zuyarshi yarasa meyasa yarinyar sometimes cikin fiskar damu take yanzuma harda hawaye yagani saman kuncinta Wanda yasa yakasa tambayar takamar yanda yayi niya lallai akwai bukatan sanin wacce ita da kuma labarin ta, mikewa yayi danufin haurawa upstairs kamar ance ya daga kai sukayi ido biyu da Heelah wacce take tsaye tundazu daga saman bene tana kallonsu kauda kai yayi irin na ko inkula tareda haurawa upstairs yana kokarin nufan bedroom din Aheel Heelah kamar jira take yagama karisowa tayi sauri shan gabanshi tana fad'in
"ahala wannan stupid girl din harcikin dare kanada bukatar ta , wai nikam me kuke nufine because nakasa ganewa lamarinku , Heelah ta tsareshi da tambaya cikin yanayin tuhuma but bai kulataba yaka kauce mata danufin ci gaba da tafiya amma se ta sake shan gabanshi tana cigaba da fad'in
"ina magana kashareni to mezai hana ka aureta da irin wannan maden da kukewa juna... damko gashinta dayayi da karfine yasa tahadiye sauran maganar da take kokarin yi tashiga kiciniyar kwace kanta
" a kullum ina fada miki kidinga nan na de harshenki daga warwareshi da kike kina furta abunda kikaga dama ni ba d'anki bane kuma niba sa'anki bane so be careful with me yana fadi'n haka ya kuma jijjiga gashin kanta da karfi kafin yayi wurgi da ita gefe yawuce yanufi bedroom din Aheel domin tabbatar da lapian shi, koda yashiga yasameshi cikin aminci yana tashan baccinsa harda minshari dan matsawa yayi kusa da bed din nan yaci karo da hulan Nisha da ta mance saman bed din Aheel wanda bata lura da shiba a takaicema batasan baya kantaba tsoro da far gaban mafarkin da tayi da kuma baccin da yasaceta a bedroom din Aheel side din Ajmal besa ta lura da shiba ,
hanu yasa yadauki hular yana jujjuyata daga bisani ya ajiye ya gyarawa Aheel blanket yarufishi dakyau kafin yanufi hana hanyar fita, koda yadawo parlourn ba takoma bedroom din ta cikin kuka , bedroom din shi yashiga daga bisani ya ajiye phone dinsa kafin ya nufi toilet danyin alwala domin time din sallah ya kawo kai yana idar da alwalan yafito da nufin shiga masallaci koda yafito suka hadu da Kamal wanda yafito shima danufin tafiya dan haka suka hade hanya suka tafi a tare duk da kasancewa masallacin a gidan yake but se kafita geat kafin ka iya shiga masallacin because kofar tawaje take ba ta cikiba,
Nisha kowa cikin hanzari tashige bedroom dinsu tasamu duk suna bacci Fadeelah nabisa gado Reeda yayinda Reeda kuma tamike saman sofa tana bacci slowly kamar mara gaskiya tadauki towel direct toilet suma kokarin shiga sekuma ta tsinkayi muryan Reeda wacce tayi likimo ta kira sunanta , Nisha tsayawa tayi jikinta duk asanyaye , karisowa Reeda tayi tana mai karewa Nisha kallo wacce ta jingina kanta da jikin bangon dakin cikin damuwa
"yadai Nisha Ina kuma kikaje bade a side din ya Ajmal kika kwanaba because bamu iya ishashshen bacci ba tareda keba, Nisha fada mata yanda sukayi da Aheel tayi irin rigimar da ya shiga mata sede sukwana tare bacci ya dauketa garin rarrashinsa but bata san time yaja hakaba,
" Alright no problem sede kuma kamar yanayin ki nagani cikin damuwa what's wrong? girgiza Kai Nisha tayi tana fadi'n
" Bakomai"
"okay"
Reeda tafad'i tareda ja baya domin bata damar shiga toilet da takeda niyar yi , Reeda komawa tayi tazauna bakin bed da tunanin keyasamu yar uwan tasu taganta haka bade yayan nasu bane yamata wani abin haka Reeda tazauna tana ta sake sake har Nisha tafito daga wanka hade da alwalan because ta kammala period dinta dan dama tarega Fadeelah farawa wardrobe tanufa ta zaro riga da hijab ta sanya daga nan tashin fida sallayan ta tada sallah ganin haka yasa Reeda Jan wani goron numfashi sannan itama tamike daga zamar da tayi tanufi toilet tayiyu alwala tanemi hijab ta sanya ta jera da Nisha itama ta tada sallahr daidai shigowar Amma domin tayar dasu sallah kamar yanda ta saba but setaga yau yaran nata sunyi hankali yau suntashi da kansu sun hutar da ita Fadeelah kawai ta hango saman bed ta baje se bacci take wacce tasan matsalar ta murmushi kawai Ammi tayi tafice da ga bedroom din tanufi nata dakin,
kamar yanda kowa yasani yau jirgin Goggo rabi zai daga zata koma karfe 10 na safe bayan kammala breakfast gaba daya family suka kasance compound din gidan domin sallama da Goggo rabi because yau zatatafi Hajia Ammi Nabilah gefe su Reeda banda agogo sarkin aiki Heelah tun farar safiya tafice daga gdn, su Fadeelah sunyi jigun jigun dasu lamari babu dadi zasuyi miss din Goggo rabi comedy bazasu sake ganintaba kuma se biki dama bawani zuwa takeba sosai se sa'i da lokaci, sekuma wani taro mai mahimmanci biki ko suna, Nisha da bata santaba abaya yanzu setaji yanzu tafi kowa shakuwa da ita , an kammala sanya kaya a mota komai ya zama ready,
" To saduwan alkhari se biki kuma in Allah yanuna mana muna cikin rayayyu " Ammi da Hajia suka shiga fad'in
"Amin " daga nan Goggo rabi tashiga daga musu hanu suma suka shiga daga mata hanun daga bisani tashiga rantsatstsiya motar Ajmal wanda dashi acikin rakiyar kuma a motarshi shiyake but Kamal ke driving dinsu se Ajmal ke gefensa muhaiseen da Goggo rabi suna daga gidan baya nan Kamal yayiwa motar key mai gadi yabude musu geat Kamal yaja motar suka fice, harsuka fice Fadeelah da Reeda basu daina bye bye ba sun sake baki se daga hannu suke
"To malamai sun bacewa ganinku daga hanun ya isa haka" Ammi tafad'i tana hararosu yayinda tajuya tanufi cikin gida,su Reeda sauke hannun sukayi jiki asanyaye ko wannensu ya nufi muhallin shi ,
,...... rayuwa yanzu yayiwa Nisha kullin huhun goro kullum cikin tunani da far gaba take tunanin mahaifinta da sanin wani hali yake ciki kullum shine aikinta hatta kyakykyawan cin abinci ta dainayi alwalantama ba kamar da ba wanda yasa hankalin su Hajia ya dawo kanta ganin canjij da sukayi atareda ita, but sun tambayi mai yakawo sauyi a tareda ita mai yake damunta setace "babu"
dan haka sesuka daina tambayan suka cigaba da janta ajiki cikin kulawa tareda wasa da dariya domin a tunanin su kewar mahaifiyar tane ya dawo mata sabo, wanda kuwa ba haka bane yanzu ba abunda take ga umma da yawoce addu'a gareta da fatan dacewa ga mahaliccinta tunanin ta daya shine tasamu hanyar fita daga gidan nan because taji gidan ya ishe tunaninta ya koma kan abbanta tun mafarkin da tayi da ashi da kuma halinda ta ganshi yana bukatan tai mako sede duk hanyar da tabi na kokarin barin gidan abu yaci tira because ko barawone yasamu nasaran shigowa gidan nan tofa fita zaiwuya agareshi matukar da kafarshi zaifita , sede in ba cewa zaiyi domin security ne abaje ko ta ina gashi ko kyakykyawan bacci basayi balle kasamu daman silalewa , gashi su gdn bawani fita akeba kullum ana jikin gida duk wani shopping din gidan barkace kezuwa tareda wasu securities din,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.