Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 24

Daga ban fitowa tayi ta dauki vaccum cleaner ta shiga tsaftace parlourn k'wata k'wata parlourn bai cika dutti ba kamar ba a zama cikin sa, tana ga mawa da parlourn sai kuma ta shiga haurawa upstairs,

Bedroom din Aheel ta nufa tabude ta shiga wani murmushi ta sake har kullum dakin Aheel ya masifar burgeta especially kyawawan Teddy's d'insa masu kya da ban sha'awa duk ya watsasu ko ina har saman bed, karisawa tayi ta zauna bisa gefen bed din lokaci diya tasaki wani murmushi mai sauti big teddy bear d'in da Aheel ya yake kwanciya da shi lokacin shitaga ya sanyawa Teddy bear d'in shi dariya ne ya kufcewa Nisha tare da daukan teddyn tana kallo, daga bisani ta rungume Teddyn kafin ta maida shi ta ajiye nan tashiga g'yarawa Aheel shin fidarsa tareda tattare masa kayan wasa da Teddy's d'insa guri guda kafin ta fito ko door d'in Ajmal ba ta kalla ba balle tayi tunanin ta shiga ta g'yara du ba da gargad'in da Heelah tayi mata akan shiga bedroom d'in mijin ta so duk randa tayi katari ta shiga tofa sai d'an buzun ta shiyasa ma ta dawo downstairs ta koma kitchen domin ci gaba da aikinta ,

Guraren 9:35, motar Ajmal ya sako kai cikin gidan time din da mai gadi yabude masa geat sai yayi parking kafin ya fito ya nausa kai cikin side din shi har security ya taho da niyar bude masa door Ajmal ya dakatar dashi sau da dama yakan hanasu yi masa duk abunda yasan zai iya wa kansa tofa yafi gane yayi da kanshi shiyasa bude masa door mota ko door din parlourn ko wani rakiya private bai cika son amasa hatta door din office d'insa da hannunsa yake budewa baya bukatar taimakon kowa sai dai irin wani taron biki ko taron siyasa ko wani taro na musamman da zai kasan ce awajan to nanne yake bukatan girmamawa kasan cewar shi shugaba koma shararren dan kwangila,.

Yana shiga parlourn saman table d'in parlourn ya ajiye key d'in motarsa tare da phone d'insa daga bisani shi kuma ya zauna bisa duguwar sofa ya mike yana sauke ajiyar zuciya remote ya dauka ya kunna television, dai dai time d'in da Nisha ta fito daga kitchen hanunta dauke da tray d'in abincin ganin Ajmal da tayi zaune bisa kujera ya kurawa TV ido yana kallon News channel, shi kuwa jin motsin mutum ta ba yanshi ya sa shi ju ya wa suka hada ido .

Kallon kallo suka shiga yiwa juna daga bisani Ajmal ya dauke kai ya maida shi kan TV yayin da ita kuma Nisha tashiga ta kowa ahankali ta kariso tsakiyar parlourn tare da ajiye tray d'in abincin bisa table kafin ta dago kai ta kallai shi.

"Ina kwana antashi lapia?"

Kamar bazai amsa ba amma kamar wanda akasa dole daker ya motsa baki ya amsa mata da

"Fine"

Mikewa tayi da nufin tashi ta fita but sai ta ji ya ce

"Zo nan"

Jiki asanyaye Nisha ta dawo ta t'suguna ta sauraron mai zaice,

"Mai yasa kika daina g'yara bedroom d'ina" Ajmal ya tambaya yana tsareta da ido daker ta iya motsa labenta wajan fad'in

"Am., damman Aunty Heelah ce ta ce karna sake shiga inba haka ba zata karya kafata" Nisha tafad'i kanta sun kuye, saura

"Nina saki aikin ko ita ?" Ajmal ya tambaya yana b'ata fiska tare da hade gira, cikin rawar murya Nisha ta amsa da

"Kai.,kkaine"

"So kar nasake miki tambaya akan hakan "

"To" Nisha ta amsa tana g'yada kai nan yayi shiru na dan wani lokaci bai sake magana ba ita kuma Nisha kanta na sun kuye jin shiru ya sa tayi tunanin ya gama korafin nashi hakan yasa cikin hanzari Nisha ta sake mikewa da shirin barin parlourn still sai ji tayi ya sa ke fad'in

"Come back ban ce kitafi ba" Ajmal ya fad'i yana hararota , cike da k'osawa Nisha ta dawo ta kuma duk'awa ba karamin ga jiya tayi ba tana bukatan ta huta but ya tsaida ita yana mata surutai gaba dayaa sai taji haushinsa ya kamata duk abubuwan da take masa ba gani yake ba, jin knocking anturo door yasa Ajmal da katawa daga maganar da yake kokarin yi ya kurawa door din ido don ganin wa ke shigowa haka babu excuse.

Doctor fu'ad ne ya turo door ya shigo bakinsa d'auke da sallama ganin haka yasa Ajmal g'yara zama time d'in da doctor fu'ad ya karisa shigowa ya nemi guri ya zauna face d'insa cike da fara'a yana kallon Ajmal da Nisha wacce tayi sunkuye da kai tana d'urk'ushe saman carpet tayi ladab

" Yallabo'i amin afuwa nashigo babu karban izini Doctor fu'ad yafad'i yana kallon Ajmal wanda shi d'in ma shi yake kallo, Ajmal bai ce masa k'ala ba dan yasan halin doctor fu'ad ko yaushe cikin tsokana da wasa yake

" Ina kwana?" Doctor fu'ad ya tsinci y'ar siriruwa muryan Nisha tana mai d'aga masa gaisuwa cikin kankan da kai .

" Lapiya qalau ya jiki naki " Doctor fu'ad ya amsa yana mai tambayar ta dagowa tayi ahankali kafi ta amsa masa da cewa

"Da sauki"

" but now naje duba ki aka shaida min kina nan shine nabiyo naga yanayin jikin naki but alhamdulillah naganki garau dake masha Allah" murmushi kawai Nisha tayi masa tana g'yada kai becauseause ta kosa ta tafi shikuwa Ajmal mamaki maganganun doctor fu'ad yayi because dama tambayar da zai mata last kenan, Ajmal komawa yayi ya kuma manne wa bayan shi da jikin sofa yana kallon Nisha karfin yayi gyaran murya hade da fad'in

" Sai nace ki zuba abincin" mamaki Doctor fu'ad ya shigayi ganin mulkin mallaka da Ajmal ke yiwa marainiyar Allah sid'i sid'i Doctor fu'ad ya ga Nisha tamike a sanyaye ta nufi kitchen wasu plates da spoons Nisha ta kuma dau kowa ta dawo ta bude foodflast tashiga serving dinsu wani daddadan kamshin na musamman ya shiga gauraye parlourn fried chips with plantain and vegetables soup with roasted chicken ga sandwich with pancake gefe kuma ga lemon iced tea Nisha sai da ta gama serving din ogan nata kafin ta janyo wani plate din tasoma kokarin serving din doctor fu'ad

"No karki wahalar da kanki kibarshi kawai zanyi serving da kaina tunda kin sallami mai gidan naki ya wadatar" wani kallo Ajmal ya dago yabi doctor fu'ad dashi kafin ya maida hankali kan abincin sa ya suma ci ,

"Za,.zan iya tafiyaiki "

Nisha ta tambaya tana kallon Ajmal yayinda ya kai yayinda ya kai lallausan pancake bakinsa g'yada mata kai kawai yayi ba tare da yayi magana ba cikin hanzari Nisha tamike ta fice daga parlourn sai turo baki ta ke shi kuwa Doctor fu'ad an barshi da mamakin abokinsa ganin yanda ya tusa yar mutane gaba yana bata umarni cikin isa da gadara wai dan ma bai san matsayinta gareshi ba ,yarinyar akwai hankali da nitsuwa kuma ba maisun ha ya niya bace balle yawan magana ,.

sam baya so Ajmal ya dauki halhakinta da yawa because yasan halin Ajmal na ko in kula especially yanda yaga yamai da yarinyar tamkar mai masa hidamane y'ar aiki kawai yana fatan akan yarinyar nan Ajmal ya fahimci maiye soyayya kauna da kuma yadda akejin shaukin wadda akeso ya fahimci rayuwar aure da kuma ma'anarta, a iya sanshi da Ajmal duk bai fahimci wadannan a baben ba kuma ya kasa tsayawa ya fahimta , haka ma ta ban garan aurataiyya bai daukeshi da wani mahimmanci balle ya tsaya ya fahimci yanda alamuran suke tafiya but ya tsaya ya na ta wahalar da kanshi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.