Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 24

Ina Aunty Nabilah Nisha tasake tambaya karo nabiyu, kamar bazaiyi magana ba sekuma taji yace,"

tana sashin Hajia a can muka sauka duk family anacan kekuma kinanan kina bacci, cikin hanzari nisha tashiga fadi'n, "
Muje can musameso to tafad'i tana kokarin yin gaba , ga mamakinta setaga Kamal yanuke, bakin bed yanema yazauna tareda hade raii, "

Zomuje mana! Nisha tafadi gamida jiyowa tana kallonshi, amma kamal senukewa yakumayi yaki tashi, dariya nisha tasaki ganin yanda kamal yayi tamkar wani baby harda wani nuke shoulder, "
Please meyasa? Nisha tafadi tana d'an shagwab'e fiska "

Naki d'in da murna da d'auki nataho gareki but ko tambayan yanake bakiyiba balle. adanyi hugging dina amatsayina na brother dinki, dariya nisha takumayi tana fad'in, "

I'm sorry bro ya kake let me shaking hands nisha tafadi gamida mika masa hanu , haka kamal yadauki hanu yamika mata amma ga mamakinta setaga kamal gam yarike mata hanu tareda janyo hanunta tafado jikinsa tsam yarungumeta akirjinsa kamar wata baby, cikin hanzari nisha tajanye jikinta akunyace tafice da gudu tana murmushi, shima mikewa yayi cike da farin ciki da nishade yana murmusawa yabi bayanta,

Nisha bata tsaya da gudunba harseda ta iso door din Hajia taja tatsaya ganin Ajmal dake kokarin fitowa wanda harsuna kokarin karo da juna , kallonta Ajmal ya tsayayi da mamakin hanzarin metake gashi harwani haki take kamar wacce tayi tsere , daga kanda zaiyine ya hange Kamal dake biye da ita wanda ganin yayansu yasa yarage saurin yashiga tafiya slowly yana sosa keya irinta marasa gaskiya "

wato shiyasa akane meshi cikin family aka rasa ashe gun wannan yarinyar yaje yatare Ajmal yashiga maganar zuci , baitsaya jiran isowar Kamal ba yasamu daman barin wajan yanufi side dinshi, wanda hakan yabawa Nisha daman shigewa part din Hajia cikin hanzari kamal shima yasamu daman biye mata baya, Ajmal yana isa cikin parlour ya hangi Aheel da mom dinsa wacce tayi amfani da extra key wajan bude kanta tazuba musu abincin da Nisha ta girka sunaci , Aheel naganin papanshi yashiga washe baki yataso da gudu ya rungumeshi , cidak ajmal yadaga Aheel suka karisa dining table suka zauna, "

Your welcome dear Heelah tafad'i kamar ba ita tagama daru dazuba, shiru yayi baice mata kala ba sema kallonta dayake idonta sunyi subul subul dasu saboda kukan datasha dazu , mikewa tsaye tayi tashiga yin serving din Ajmal ba tareda yanemi taimakon taba , shikuwa baiyi kokarin dakatar da itaba hartagama tatura masa plate din abincin gabanshi tareda duk wani abun bukatu , bamusu yasuma cin abincin , yana tsaka da cin abincin kamar wanda aka tsikareshi idanunshi suka shiga hasko masa nisha dake tafe cikin hanzari kamal nabiye da ita,

Nan kuma ya kauda wannan tunanin daga ransa, lokaci d'aya kuma yaji abincin yafita daga ransa ma' ana yakoshi , haka yasoma kokarin mikewa , "

Papa ina zakaje ? Aheel ke tambayan papanshi ganin yamike"

I'm going to the rest kazauna kusa da mom dinka ,gyada kai aheel yayi tareda cigaba dashan cornflakes dake gabanshi , heelah bayan ajmal tabi da kallo tana tab'e baki harya kurewa ganinta ,..
,
Ab'an garansu nisha kuwa tunda suka shiga sashin Hajia , a parlour suka tararda sauran familyn anatashan fira cikin raha Daddy Ammi Hajia da Goggo rabi sesu fadeelah da reeda wanda suka sanya Nabilah a tsakiya sunata zuba mata surutu da tambayoyi, itakuwa Nabilah duk hankalinta nakan Kamal da nisha wanda sukashigo yanzu atare ,

duk yanda Nabilah tayi iya kokarinta wajan mantarda Kamal soyayyan nisha amma abun yaci tura , yanzu gashi daga saukanso zuwa gida ita yafara cigiya , koyanzuma da ake tsaka da hira tafahimci yanda suke jefawa junansu wani kallo suna murmushi, shiyasa koda sukashigo cikin parlour Nisha data dagawa Nabilah gaisuwa ba harzuci ta amsa mataba saboda yanda kishi ke d'awai niya da ita, itakuwa Nisha kallon Nabilah take ganin yanda takara canzawa tayi kyau taciko kuma takara haske ,da alama hutu yakarbeta

Masha allah wasa yayi kyau kamal kundawo cikin SAA sai dai kuma kasam mashemu because bawanda kafadawa , yanzu yakamata mubarku kuje kuhuta kaida matarka dan nasan baza arasa gajiya atareda kuba, Daddy yafadi yana kallon kamal daga bisani kuma yamaida kallonsa ga Ammi yacigaba da fadin,"

yakamata kiyiwa Barka magana ta tanadar musu da abuntabawa , daga bisani kuma munada bukatar ahadamana kayataccen dinner in the night saboda farinciki wannan ranar , "

Insha allah yanzu kuwa Ammi tafadi cikin farinciki tareda mikewa tafice , sundan taba hira sosai yayinda Kamal yaciga ba dabasu labarin yanda wasansu ta kwallon kafa takasance, seguraran azahar tagabato kai suka suma watsewa domin gabatar da bautan ubangiji, koda suka fadeelah suka shigo bedroom dinsu Reeda ne kadai tashiga toilet tagabato alwalanta sukuwa Nisha da Fadeelah suna fashin sallah ya bakon nasu kusan atare yaziyarcesu,

cikin Nisha da yamurda matane nayunwa yasa tatuna tunsafe ba abunda tasawa cikinta , hakan yasa tamike tafice tabar fadeelah dake kwance saman bed tana latsa wayarta , Nisha direct kitchen tanufa ta tadda barka tana tsaka da aikin da ammi tasata , barka naganin nisha tasaki murmushi,

"yar nan yau koma ina kika shiga kolekoni ba kiba inata cikiyarki "murmushi nisha itama tayi tana fadin

"kinsan yanzu papan Aheel yace nadaina kawo masa breakfast daga nan sede naje can part dinsa nayimasa girki dana dawo kuma bacci nakomayi shiyasa yau bakijiniba ai "
.
" Kai amma yayankun nan yana wahalar mana dake amma ko bakomai zaki samu lada ai, amma koya kikeji da wannan masifaffiyan matar tashi mai bala'in kishin tsaya duk ita take kore masu mata aiki saboda rashin hankali irin nata , Barka tafad'i gamida jimami"

"Uhm baba barka taimakeni da a binda zansawa acikina because yunwa nakeji sosai tunsafe namance banci komai ba Nisha tafad'i gamida kaiwar da zancen barka,"

"laa ai ammi tafadamin bake a breakfast din dazu sabida bacci kike baki tashiba shiyasama nakillace miki naki breakfast din amma inda wani abunda kikeso kifadi yanzu sena miki shi,"

"aa basekin wahalar da kankiba iya wannan dinma yayi ,"

"To shikenan kede jekizauna a dining table yanzunan zanfito" Barka tafad'i, bamusu Nisha tayi abunda Barka tace ba dadewa Barka tafito daga kitchen tajerawa Nisha plate agabanta plate din Irish and chicken dawani hadin salad agefe se dan madaidaicin kyakykyawan bowl mai daukeda fruit salad wanda yaji madara Yakuma sha sanyi ,bawani tsayawa jira Nisha tasoma ci seda taci takoshi takauda yunwar dake tareda ita daga nan tadauki plates din tanufi kitchen, tana shiga ta ajiyesu daga bisani tashiga taya Barka da aikace aikacen da take ,sannu ahankali sunayi suna fira hatsuka kammala daga nan suka shiga jera kayan lunch bisa dining table daga nan Barka takoma kitchen tadauko try din abincin data tanadarwa kamal da matarsa masu lunch din tasuma kokarin ficewa,

"Baba Barka ina kuma zaki bayan gani ? nasan lunch din su ya kamal ne da Aunty Nabilah please bani nakaimusu na hutar dake ,"

"Aa yar nan baza ayi hakaba, tunsafe kika gama bautan yayansu yanzu kuma nabarki kikare Dana kaninsa gaskiya baza ayi haka daniba kibarshi kawai yanzu zanje nadawo "

"Please baba Barka kibari nakai mana " nanfa Nisha taita mata magiya tareda dagewa Barka wanda yasa dole Barka tahakura tabata try din abincin nisha ta amsa tareda sa kai tafice , Nisha nakarisowa door din Kamal tashiyin knocking bugu daya zuwa biyu aka bude, koda budewa kuwa Nabilah takagani tsaye cikin shirin kananun kaya t shirt da wando skintight wanda yawuce gwiwar kafarta kadan tasakalo sumarta har baya yakwanta lub tayi kyau da ita, murmushi Nabilah tasakarwa Nisha cikin sanyin murya tace ,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.