Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 14 of 24

but tabarwa kanta sanin cewa ta tsaida lokacin tafiya tabar gidan nan ko ta halin yayane domin taje gurin tushenta wannan karon tashiryawa Mami koda tsiya tsiya setaga mahaifinta sai tafad'i inda ta kai Abba because taga alamun ba gaskiya alamarinta,

ranar wani lahadi da Nisha takasa mancewa dashi cikin rayuwarta tana kwance tana kwance bisa sofa cikin bedroom dinsu Fadeelah da Reeda sun kaiwa Aunty Nabilah ziyara kamar yanda suka saba sunacan sunata zuba mata surutu wanda hakan bakaramin dadi yakewa Nabilah hakan yana mata dadi sosai kasan cewar su kawaye yan uwa uwa uba kuma tana auran yayansu , but rashin jin dadinta daya takasa gane meyasa Nisha ke gudunta bata zuwa tareda su Reeda suna hira kodai ta dauka haryanzu tana fushi ko kishi da itane ita sam duk ta yada wannan mukaman zuciya daya tariketa yanzu ,

koda ace ya Kamal auranta zaiyi yanzu bazata wani damuba because yanzu yarinyar tausayi take tun wancen lokacin but itade tadaina kishi da ita musamman yanda Kamal yake kulawa da ita sosai ko bacin rainta bayason ganin yanzu duk wani abunda yakeso ko zaisashi farin to itama tana son shi saboda tsantsan so da kaunar da take mishi zataso duk abunda yakeso koda ita bai mataba, ta rintsa ido tana ta faman tunanin da tasaba koda yaushe tadaurawa kanta tunani da damuwa bude ido tayi tazauna tareda dafe goshinta cikin tafin hannunta , nan ta sakalo kafarta kasa ta sakko daga sofan tanufi window,

daga labulen window tayi tana ta kallon geat inama ace ana bacewa da tabace yanzun nan because duk tunanin ta ya ta al laka ga barin gidan motsin shigowar da tajine yasa tamaida da hankalinta ga door din ganin Kamal tsaye bakin door din face dinsa yayi jawar idonsa duk yacika da kwallah yasa tajiyo gabaki daya tana kallonshi tareda karisawa inda yake tsaye, kallonshi take sosai cike da mamaki mutumin da kullum yake cikin raha da dariya but yau face dinsa ya canza

"ya Kamal what's happened naganka cikin wannan yanayin? "
Nisha ta tambaye shi ciki kaduwa Amma setaga ya juya baya yadafe hanunshi jikin bangon dakin ya sunkuyar dakai kasa

" Ya Kamal kasani cikin damuwa naganka cikin yanayin da ban saba ganin ka ahakaba, please kasanar dani damuwarka"

"Nisha dama ke ba tawa bace " ras gaban Nisha yafad'i jin abunda Kamal ke fad'in

" but meyasa zakace haka ni takace mana Nisha tabashi amsa cikin damuwa narashin sanin dalilin dayasa yazo mata cikin wannan yanayin yana irin wannan maganan,

"Ke batawa bace Nisha because da aure akanki kika boyemin kuma nazo miki da soyayyata kika amsa ba tareda sanin igiyar aure ne akanki ba , why kika boyemin baki sanar da niba why Nisha? Kamal ya fad'in cikin daga murya gamida damuwa da baccin rai yana tambayan ta,

Nisha turos tayi tana kallon shi da mamakin maganganun da yake fitowa daga bakinsa, 'anya ya Kamal yana cikin hankalinsa kuwa Ammi tagani tazo da sauri kusa dashi ta dafa shoulder dinsa tana fadi'n

"Kamal mekakeyi haka ne? kamata yayi ka tsaya kaji abunda zan fad'i ba kafito ka kyaleniba yayinda nake magana kasaita natsuwarka mana haba Ammi tafad'i cikin sigan fad'a

"Ammi idan kowa zai boyemin ita bai kamata ta boyemin ba because tasan inasonta kuma na baiyana mata soyayya na agareta ta amsa batare da ta fad'amin matsayin taba, am,.

"Ya isa haka Kamal itama ba tasan komai gameda auran nan ba haka zalika shima Ajmal baisan da auranta akanshi ba iya tsakanimu magnar ta tsaya sai kai yanzu da kabijiromin da batun soyayyarku da na nemi na fahimtar da kai kaki saurarata". Ammi tafad'i cikin sigan shiga damuwa sam bataso abun ya kasance ta hakaba taso abi abun asannu ahankali but taurin kai irin na Kamal yakasa fahimtarta balle ya saurareta gashi yanzu yasa tayi subul da baka sirrin ciki yafito fili,

"Innalilahi wa'ina ilaihi rajuun" abunda Nisha take furtawa kenan ahankali yayinda ta dafe goshinta wanda takejin yamata nauyi saitaji mak'ok'oronta ya bushe yawun bakinta ya kafe dib

' Aure! Aure dai ' Nisha keta maimaita wa cikin zuciyarta ba jimawa idonta tasuma ganin walkiya walkiya haske haske hazo hazo kankance mai dakin yafara jiyuwa mata kafin su ankara tafad'i kasa sumammiya, sallallami sukashiga yi harsuna gwaral wajan karisawa wajanta tso da fargaba duk ya dabai bayesu

"Kaga irinta ko Kamal ga irinta nan da ka saurareni munyi maganan cikin nitsuwa da duk haka bata faruba da batajiba bare hankalinta ya tashi yanzu ga abunda taurin kanka ya haifar", Ammi tafad'i cikin rudu da tashin hankali

"Please Ammi kibar wannan maganan yanzu bashine solution ba mudagata mukaita asibiti don aceci lapiyar ta because karwani abin ya sameta"

Kamal yafad'i cikin rikicewa da tunanin mezaije ya dawo

"Kamal kira doctor kira doctor fu'ad please kirashi da sauri"

"Why not bazamu kaita asibiti ba?"

"Zaka sake taurin kainne ko zakayi abunda nace "

Ammi tafad'i a tsawace , cikin hanzari Kamal yamike yazaro phone dinsa cikin pocket dinsa marmaza yashiga dealing number doctor fu'ad yana dagawa Kamal yasanar dashi ana bukatarsa agida yana gama sanar dashi ya katse wayar ya kalli Ammi yana fadi'n

"Ammi taimaka min mudagata izuwa bed kafin doctor fu'ad din yakariso ba musu Ammi tasa hanu suka sunkuci Nisha wacce ke maga shiyar kamar macecciya suka daurata saman bed Ammi tazauna kusa da ita ta janyo hanun Nisha ta daura bisa nata tana murzawa idon ammi duk ya ciko gaba daya tausayin yarinyar ya kamata ita dama kwata kwata bataso al amarin nan ya kasance ba Hajia ce tayanke hukunci ba tareda tayi la akarin abunda zaije ya dawo ba da ace tasan kaunar da Kamal yakewa Nisha tabbas bazata taba bari wannan lamarin yafaruba gashi yazo mata time din da yariga ya makara wanda hakan yajawo tonu abunda aka rufe wanda dama duk daren dadewa zaibud'u,.

duk da sunso abi abun daki daki Amma zuwan Kamal duk ya cakuda abubuwa saboda shegen zuciya irin tashi Ammi hararo Kamal tayi wanda keta safa da marwa cikin dakin cike da damuwa, ba ji mawa Kamal yaji ki ciniyar bude geat aiko cikin sauri yafice ya taroshi cikin hanzari suka kariso shigo cikin bedroom din, ganin Nisha kwance idanuwanta arufe Ammi na gefen ta cikin damuwa yasa doctor fu'ad saurin karisawa kusa da bed din yana tambayan ba'asin meyafaru da ita, saidai ba amsa saima Ammi da ta kai kallon ta ga Kamal wanda shima itan yake kallo ta kuma cilla masa harara wanda ya sa shi sunnar da kai kasa cikin na dama jin shiru ba wanda ya samu daman ba shi amsa yasa yace su ba shi guri ya dubata ba musu Ammi tamike tafice Kamal ma ya rufa mata baya haka suka fito sumu sumu da su.

Gefe Ammi tazauna bisa sofa ta raf ka uban tagumi shi kuwa Kamal bai samu daman zama ba sai kaiwa da kawo yake tsakiyar parlourn, jim kadan doctor fu'ad ya fito wanda suna ganin fitowar shi yasa suka nufoshi suna tambayan shi ya jiki Nisha ya amsa musu da

"Shi is fine but baku bani amsa ba maiyayi causing dinta shiga wannan ya nayin doctor fu'ad ya kuma tambaya yana kallonsu Kamal dai har yanzu bai iya cewa komai Ammi ce ta saukar da ajiyar zuciya jin kyakykyawan labari Nisha na cikin koshin lapia, takalli doctor fu'ad ko ma wa tayi ta zauna kafin tayiwa doctor fu'ad nuni da ya zauna dan yi masa ba ya ni.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.