Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 9 of 24
Karfe 11:30 Hajia da Goggo rabi dasu Reeda suna zaune parlour wanda tun bayan kammala breakfast dinsu suka yada zango gurin suna dan taba hirarsu da suka saba ,"
yaude yakamata naje saloon din nan da shopping kafin tafiyata gobe Hajia karama (Fadeelah) fatan zakimin rakiya , Goggo rabi ta tambaya tana kallon Fadeelah dake washe baki gami da faÉ—i'n,"
Eh Goggo rabi zan miki rakiya Fadeelah tafad'i tana kallon Reeda gamida yimata g'walo Banda Nisha datayi sunkui da kai tana murmushi , Fadeelah da Reeda suna kaunar fita yawo because basu cika fitaba daga gida se makarnta barin ma yanzu dasuke hutu ba zuwa school duk se zaman gidan ya ishe "
Goggo rabi dukansu uku taso suyi fitan tare zaifi armashi but ganin cewa Nisha da igiya uku akanta baikamata sufitaba ba tareda sanin mijin taba , to gwara sutafi da Fadeelah Reeda ta Taya Nisha debe kewa kar abarta shiru ita kadai, itama taban garan Nisha da Goggo rabi cewa tayi tare zasuje amma ganin cewa tacanza zabi se bata damuba , Hajia itama tasan dalilin dayasa Goggo rabi tayi hakan amma da tare duk yakamata sufita tunda dukansu suna shaawar fitan, "
Allah sarki yarinyar batasan nauyin da ya rataya wuyan taba wannan duk ninayi sanadin hakan amma nan ba da jimawaba zata San nauyin dake kanta duk da batasan ya Nisha zata kalli lamarin takuma karbeshi batareda wani damuwaba duk da tasan hankali da nitsuwa irin na yarinyar, Hajia ke maganan zuci yayinda take kallon Nisha cikin tausayawa da hukuncin da tayanke ba tareda tayi la akari da wani abunda zaije ya dawoba , tana matukar kaunar yarinyar tana kuma jinta sosai cikin zuciyar ta bazataso tayi wani abunda zaicutar da itaba,
sunyi firansu sosai gabatuwan sallahn azahar ne yasa duk suka Mike suka nufi muhalinsu domin gabatar da sallah , Goggo rabi da Hajia suka nufi sashinsu sukuma yan matan suka nufi bedroom dinsu'
bayan sun idar da sallansu suka daura aniyar zuwa side din Kamal gurin Auntyn su Nabilah yar uwa kuma kawarsu suna jin dadin kasan cewa da ita ba kaman Heelah ba da ko kallon side din ta basayi balle suji sha' awan zuwa duk da ita din yar uwarsuce tajini but halinta yasha ban ban da nasu because Heelah akwai bakin hali da rashin kunya shiyasa basa shiri balle suje inda take "
Ke bazaki biyomu muje firan bane gurin Aunty Nabilah, su Reeda ke tambayan Nisha wacce take zaune bisa bakin bed tana kallonsu,"
A'a ni bacci nakeji kuje kawai, Nisha ta basu amsa , basu takura mataba because sunsan kwanan zancen dan haka suka fice daga bedroom din cikin rawar jiki sukabar Nisha wacce ta gyara kwanciyar ta bisa saman bed din , nanfa tafara g'yan'gya dawa bacci yanason cinye idonta Karan shigowar message ne yasa tabude ido da kamar bazata duba wayarba sekuma ta janyota tashiga dubawa , tsulum tamike tazauna ganin message din Ajmal ne Wanda yake bata umarni tashirya masa lunch hulan kanta tazara da sauri Wanda yafice daga saman kanta tamai dashi mazauninsa, dan turo baki tayi ita batasun komawa side din shi ta tarar da wacce masi faffiyar matar tashi tunda matarshi tana nan mai zai hana ta mishi lunch din kamar yanda tamasa breakfast ,
mikewa tasomayi daniyar tafita daga bedroom din ganin shigowar Kamal yasa taja ta tsaya tana kallonshi da mamakin me yakawoshi ,"
yade wannan kallonfa? Kamal ya tambaya yayinda yake karisowa yanemi sofa ya zauna , still de Nisha kallonshi take ba tareda ta motsaba kotace wani abinba ,"
sisy kizauna mana wata magana nazo muyi Kamal yafad'i yana kallon Nisha wacce tadaga kafa ahankali takoma tazauna bakin bed tana kallonshi, murmushi Kamal ya sake yana kuma fadi'n,"
Ko kina wani uzurinne nazo nakatseki , murmushin itama ta kwakwalo tana faÉ—i'n,"
A'a bakomai, "
Alright barinaje kan batun da yakawone ba tareda bata lokaciba, "
yarda da amincewarki nakeda bukata, dan zaro ido waje Nisha tayi tana faÉ—i'n,"
Amincewata akan me ya Kamal,? dan gyara zama Kamal yayi hankali kwance yana mata murmushin kashe zuci yace,"
tunbayan da nabada labari abaya gaban Nabilah friends da sisters dina yanda sonki da kaunar ki yadinga d'a wainiya dani har kawo yanzu damuke gida daya dake but ta ban garanki bansan ya kika dauki soyayya taba inaso naji daga gareki ya matsayin kaunata agareki ? yakike feeling soyayya ta cikin heart dinki? shin kina sona kamar yada nabai yana miki ko aa? inason sani wannan shine tambayoyin da Kamal yajerowa Nisha Wanda yasatayin shiru tana kallon kasa kamar mai nazarin wani abu, "
sisy what are you silent kamata yayi ki amsamin tambayoyina ,"
Ya Kamal tambayarka bata da amsa Nisha tafad'i ba tareda tadago sun hada idoba,
"means bak'ya sona? nikaÉ—ai nake ta dakon soyayya? shiru Nisha tayi batace kalaba bata kuma É—ago kai takalleshi ba , shima Kamal shirun yayi tareda sunnar da Kai kasa tsawon wasu mintuna kafin ya É—ago kai yakuma kallonta idonsa duk yayi jawar kamar mai Shirin yin kuka , mikewa yayi jiki ba kwari yasuma tafiya asukwane kamar wanda aka zarewa lakan jiki, wani dariya da Nisha tafashe dashine yasa Kamal dakatawa daga tafiyar dayake yajuyo ahankali yana kallonta,
ganin yanda Kamal yajiyo yana kallontane yasa ta kai hanu takulle bakinta tana me cigaba da dariyan kasa kasa tareda mikewa daga zaunen da take tashiga karisowa inda yake tsaye seda tawurga masa wani murmushi kafin tace,
"tafiya zakayi ba tareda kaji mai zan faÉ—i' ba"
"mekikeson na tsaya naji bayan kince ba k'yasona , still kin ɓige dayimin dariya like kinga wani mahaukacin" Kamal yabata amsa tareda hararota yana mai kauda kai gefe, murmushi Nisha takuma yi tana fadi'n
"ya Kamal yaushe kaji nace bana sonka?" Nisha takuma tambaya still ta tsareshi da ido , rintsa ido Kamal yayi ya bude tareda sauke ajiyar zuciya ahankali kafin ya jiyo da face dinsa suna facing juna yace
"I'm hearing you talk me kinasona kamar yanda nakesonki ko a'a ?" Kamal yakuma tambayan Nisha yaname tsareta da ido , dan juya mishi baya Nisha tayi kafin tashiga fadi'n,
" Ya Kamal wata macece zaka mata tayin soyayya taki amsa , tun ranar da muka soma haduwa nayabawa hankalinka duba da yanda ka durkusa kana bamu hakuri bisa rashin hankali da dan uwanka yamana duk da ba laifin ka bane haka kuma baka sareba kabimu har lnda muke kaci gaba da bamu hakuri, juyowa tayi takalli Kamal wanda ya tsura mata ido yana kallonta yayinda take maganar kafin taci gaba da faÉ—in
" Ya Kamal baka da girman Kai zuciyar ka kyakykyawa ce kuma kana da tausayi duk da ilartar da kai danayi cikin rashin sani sana diyar zalunci irin na dan uwanka hakan bai hana nazo da damuwata gareka ka kasa kashare min hawayeba a lokacin da narasa me taimakona ,amm tunani na.......
"shiiiii Kamal ya katsare ta daga surutan da take tafaman kwararo masa
" har yanzu banji amsar da nakeson jiba daga gareki do you love me or not" Kamal yasake jefo mata tambaya, dukar dakai kasa Nisha tayi kafin tace
"Ina sonka ya Kamal but Aunty Nabilah.., cikin hanzari Kamal ya dakatar da ita daga maganar da takeson yi yashiga fadi'n,
"karkisa wani tunani game da ita kibar komai hanuna , kwai abunda zan gaya miki shine bana tsayawa buye abunda nakeso dan haka zan sanar dasu Ammi cewa muna soyayya kuma aure zamuyi banason bata time, dan zaro ido Nisha tayi tana faÉ—in,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.