Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 23 of 24

"My little yau ba school ne naga Kanata bacci har wannan time d'in, "washe baki ya kuma yi yana fadi'n

"Laaa Aunty jiya fa mukayi hutu, kuma hutu mai yawa aka bamu har 3 weeks Aheel ya fad'i ya na nuna da yan tsun hanunsa uku murmushi Nisha ta tayi gami da fadi'n

"Good tasu muje to baccin ya isa haka" , nan ta juya masa baya alamar ya hau bayanta shikuwa cikin zumudi ya dale bayan Aunty Nishansa tare da sakalo face d'insa gafen wuyarta yana ta dariyan jin dadi daga haka suka fice daga parlourn bedroom din Aheel suka nufa ta sa ya cire wannan tausasun kayan baccin da ke jikinsa ta bashi dan k'aramin towel ya daura yashiga bathroom domin ya wanke jikinshi yayinda ita kuma ta nufi wardrobe ta dauko masa kyawawan kaya t shirt and jeans rigar white color sai black jeans tana jin yanda Aheel ke ta wasa cikin toilet Dd'in yana tsalle tsalle yana wasa da ruwa ganin bayida niyar fitowa yanzu yasa no Nisha mikewa tashiga toilet d'in ta taimaka masa yayi wankan kafin suka fito ta kimtsashi tare da sanya masa kaya kafin ta jawo hanun shi suka nufo downstairs.

Dining table ta nufa dashi ta zaunar da shi ta dauki plate ta sanya masa breakfast duk abunda ya nuna ya naso shi ta sanya masa ta tura masa gabansa ya suma ci, daga haka ta zame jiki ta koma bedroom din.dining zuciyarta daya tunfi toilet domin fara wanke shi murda handle d'in tayi ta shiga , zaune yake cikin bathtub yayi tsam da ranshi idanuwansa a lumshemaganganun Doctor fu'ad sai d'a masa yawo cikin kunnuwa su ke sam ya kasa gas gata maganganun sa because yasan doctor fu'ad dasa zulaya cikin lamauransa in ba daga wajan su Daddy ko wajansu hajia ya ji bataun kai tsaye daga gare suba bazai taba gas gata hakan ba, idan kuma harta tabbata hakan lamarin bazai taba daina bashi mamakiba.

ko Time d'in da aka aura masa Heelah ba waii dan ba yi da ikon hanasu ko da dakatar da su bane kawai ya kyalesune ya zuba musu ido ba wai dan ya rasa yanda zaiyi bane but hakan ba shi zai basu daman jogana masa wannan wata mace ba especially wacce baisan wacece ita ba bai kuma san daga ina ta ke ba ballai asan asalin wacce ita, turo door din toilet d'in da akayine yasashi bude ido da sauri don ganin wake kokarin shigo masa bathroom ba neman izini, Nisha ya gani ta shigo kai tsaye wacce itama da alamar ba ta lura da shi ba because toilet d'in yana da girma sosai tamakar parlourn wani gidan fiskarta dauke da fara'a takarisa gaban katafaran mirror da ke cikin toilet d'in da ya ke fara kallon mutum yayinda ya shigo tsayawa ta yi tana hango kanta ciki rabunta da ta tsaya ta kalli kanta madubi harta mance time d'in kallon kanta ta ke sosai tana karawa tare da shafo face d'inta ta jikin mirror ganin tayi har wani kumatu tayi kuma ta kara haske sosai.

tabbas itama yau tayi mamakin yanda taga yanayinta ya canza gaba daya hutu ya zauna mata haka ta dinta juya lallausan hannayenta tana kallo kamar ataba jini ya fito time daya kuma fara'a ta ta dauke face d'inta ya koma face d'in jimami saka makon tunawa da maganar salma na cewa

'duniya yayi mata dad'in da zata iya mancewa da ita'

duk da ba ta yi tsammanin wannan furcin daga gare ta ba because ita dai a iya saninta bawani jin dad'in da zata tsinci kanta aciki ta kasa tunawa da aminiyar ta kawar yarinta abokiyar cin mushe su kashe su bunne tare wasu zaffan hawayene suka gangaro mata kafin cikin hanzari ta shiga goge hawayen ta suma waige waige don fara aikin da ya kawota kar ogan nata ya zu ya taddata anan tana ta karanta wasikar jaki, wani ihu Nisha ta kawo sake tana sallati gamida rintsa idanunta because ganin Ajmal time d'in da ya mike ya na kokarin daura towel bisa waist d'insa tana kuma yin baya ganin Ajmal tsaye cikin bathtub yana kokarin daura towel bisa waist d'insa, baya Nisha ta kuma yi da sauri idanuwanta a rintsai jikinta sai k'yarma ya ke a aikuwa sai timmm kakeji ta zame santsin tailed ya zamar da ita a zafafe ta ta kuma mikewa tanufi door sai da ta bude ido kafin ta murda handle d'in tafito ta watsa aguje ta fice.

Aheel na zaune bisa dinning table yana breakfast kamar yanda Nisha ta barshi sai ganin Auntynsa yayi tafito fuuu kamar wata mota ta wuce ta fi ce da gudu daga parlourn ko waiwaye ba ta yi Aheel bin ba yanta yayi da kallo tare da kai kallonsa upstairs dan ganin mai ta ke wa gudun dan ba k'aramin tsoro ta ba shi ba sai zare ido ya ke amma ba kowa da ke biye da ita nan ya shi ga zamowa daga kujeran da nufin bin bayanta but sai ya ji muryan mom d'insa ta kira sunansa wanda ya sa ya mai da hankalinsa garaita ya shiga washe mata baki tare da kokarin karisawa gareta yayinda ta ke sakkowa ta na sanyi cikin kananun kaya wata half vest sai d'an wani gajeren wando iya gwiwa ta tufke gashinta a tsakiyar kanta sai lilo ya ke bayanta ta yi kyau da ita, Cike da murmushi ta kariso ga Aheel ta re da sa hanu ta sun kuci d'an nata tana fadi'n

"Good morning in this morning my love"

Morning Mommy Aheel ya fad'i gamida kwantar da kai jikin mommynsa

" What are you doing here" Heelah ta tambaya tana mai kallon Aheel ta na kuma kallon dining table d'in da kawata shi da kyawawan girke-girke kala-kala ta shaida wannan aikin Nisha ne nan ta shiga hararo abubuwan da ke jere bisa dining tana tabe baki nan Aheel ya shiga zamowa daga jikin mom d'insa kafin Heelah ta direshi akasa ta na kallonshi.

"Mom taho ki zauna kiye breakfast Aunty Nisha na ne ta yi mana delicious mai dadi " ta ho ki zauna ke ma " Aheel ya fad'i cike da murna yana washe baki gamida jawo mata kujera alamar ta zauna but Heelah sai Jan wani banzan tsaki tayi tana tabe baki tana kallon Aheel da ke ta rawar Kai wai Aunty Nishansa tabdi.

"Come and seat Mom" Aheel ya kuma fad'i yana kallon mom d'in nasa wacce ke ta faman hararo shi da shi da table d'in gaba daya tana fadi'n

"Kai da Allah rabu da ni mai zan zauna na ci a wannan tsiyar Allah kaidai yasan hade haden da ta ke cikin girke-girken nan da ta ke tana jan hankulanku da tunanin ku ku ke ta wani ribibi a kanta ta ga ma siye zuciyoyinku da yin nasara a kanku to nikam na fi karfinta ta Allah ba ta mutum ba muna fukar banza kawai Heelah ta karisa fad'i hadai da jan wani dugun k'wafa zuciyarta ta sai zafi ta ke ita ta rasa ya zatayi da wannan yarinyar gaba daya ta shige mata hanci da k'udunduni juya baya tayi yayinda ta hade hannayenta a k'irji ta na kada kai ta na tunano irin hanyar da zatabi da Nisha, shikuwa Aheel shiru yayi jikinsa duk yayi sanyi ganin yanda mom d'insa ke ta surfa masifa akan Auntynsa duk da baisan inda zantukan na ta suka do sa ba baikoma fahimce ta ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.