Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 16 of 24

"Ki ga far ceni y'ar nan na yanke hukunci ba tareda izini yarda ko amincewarki ba nayi hakanne ba dan na cutar da ke ko saki cikin damuwa ba " tar Nisha ta bude ido jin Hajj mama ke magana ta na kokarin matsar kwalah
Manyan idanuwanta wayanda suka kumbura ta sauke akan Hajia wacce tayi sunkuye cikin kunya da na dama tana ta faman sharce , hawaye da gefen zaninta hankali Nisha tasuma kokarin gyara zama wanda yayi sana diyan dago da kan Hajj mama cikin sauri tashiga taimakawa Nisha wajan gyara mata zaman tana fadi'n

"Sannu 'yar nan ya jikin naki dan allah ki gafarce ni ba na son ki shiga da muwa sabida ni hak'ik'a nayi babban kuskure wajan yanke hukunci ba tare da sani ko yardarki ba amma dan allah,.. cikin hanzari Nisha tariko hanun Hajj mama wacce duk ta da burce ta shiga da muwa cikin sanyin murya Nisha tasuma fadi'n

"Please Hajia kidaina neman afuwa agareni aganina kun isa da ni shiyasa kuka zabamin miji kuma nasan ba dan kucutar da ni bane yasa kukayi hakan, inde nakasance daya daga cikin y'ay'an gidan nan to kunada kowacce irin dama akaina ba zabin da zakuce kunyi nace AA ko nayi musu please Hajia kidaina damun kan ki zabin da kukayi agareni shiya dace dani because ni yar kuce, Nisha ta karishe zancen da rintsa ido saboda hawayen da yacika idanuwanta,

"Aa Nisha kema kina da naki ra'ayin kuma kina da zabi, hakika naji komai daga bakin Ammi soyayyarku da Kamal wanda kuwa da nasan hakane kokusa ko alama da bazan fara wannan katubaran ba nide burina kikasance daya daga cikin sirikar gidan nan alakarmu dake takara kusanci sosai , hakika nice sila aurarraki dayawa daga cikin family nan saboda dauren family na , kama daga auran habu d'ana(Daddy) nina hada auran sa da yar wajan k'anwata hafsa wacce Allah ya azurta ta da yammata biyu Bilkilsu da Maryam, wanda daga baya Allah yamata rasuwa nina cigaba da rikeso lokacin Ina tareda mijina Alh Muhammad bature wanda shi balaraben saudia ne a saudia muke da zama acan na haifi y'ay'ana maza guda biyu Abubakar wanda muke kiransa da habu(Daddy) da Muhammad wanda muke cemasa modi(Abu) sai Rabi'atu itace karama,

Bayan rasuwar k'anwata hafsa can natafi dasu kasan cewar ita a Nigeria tayi aure kuma tana kusa da baffa Sani wanda yakasane wan mahaifinmune shiyarikemu yarenemu saboda mu marayune duk mahaifanmu sun rasu shiya cigaba da rikemu bisa amana kulawa da kuma nuna mana gata because iyayenmu sunada wadata sosai bamusan meye wahala ko taluciba alhamdulillah muna cikin rufin asiri bayan rasuwar baffana da kuma k'anwata ba karamin shiga damuwa nayiba because narasa dangina yanzu banida wasu family da wuce y'ay'ana 5 da mijina dan haka sena rungumesu muka cigaba da rayuwar farin ciki dajin dadi yayinda kowannesu yake karatu gurare daban shi Abubakar a Paris yake ban garan kasu wanci yayinda shikuma modi yazabi Landon ban garan likitanci sukuma y'ay'a matan agabana suke karatu because ni ban yarda da karutun y'ay'a mata awani gurin da ban ba shiyasama kikaga Fadeelah da Reeda suke karatunsu a maryam abacha komai zasuyi ido nakansu,

Bayan kammala karatun kowannesu yacika burinsa yayinda modi ya zama babban doctor nan kasar Landon din yake aiki yayinda yabude hakararren hasibiti nashi nakanshi dake gida Nigeria da sunana HAJIA MADINA hospital inda yarsa Heelah take ai kenan kuma ita take jagorantar asibitin ,shikuwa habu yazama babban dan kasu but shi rayuwarsa harta ban garan siyasa ya taba yayinda yashahara wajan kasu wancin gwala gwale anan kasar England yayinda ta ban garan siyasa yake na hanun daman shugaban kasa, ganin kowannesu yacimma matsayan dayakeso tsayawa yasa nabijiro musu da batun aure cewa kowannesu ya gabatar min da macen da yakeso kuma yakeda burin aure ban garan habu yanuna min shide tukunna bashida wanda yake so yanzu baisaniba ko nan gaba but azahiri yanda naga sunfi shakuwa da Balkisu kullum suna tare suna fira nayi tunanin soyayyace a tsakanin su but saiya tabbatar minda ba abunda nake tunanibane to amma banida zabi wannan alkawarine da nayiwa zuciyata hada auran su dukansu 4 saboda sake dankun zumunci because a ganina nagida bai koshiba ba abawa na wajeba,

Kasancewar modi shine babba senayi tunanin hadashi daHafsa because yarinyar akwai nitsuwa sosai ga hakuri but shi modi akwai taurin kai gaskiya wani lokacin baya jin magana ga fada ba kamar habu ba dan shi yanada saukin kai ga raha but shima wani time inya juye baka gane masa shiyasa nayi tunanin shikuma na hadashi da Balkisu (Ammi) Balkisu yarinyar tana da raha ga suruta kamar aku saide kuma akwai tsiwa wani lokacin shiyasa nake ga zasufi dacewa da habu tasu zaifi zuwa daya saboda ita Hafsa tanada shiru shiru sosai batafiye maganaba kuma itace karama akan Balkisu, koda nakawo shawaran hada junansu aure bawanda yakawomin cikas se modi dama nayi tunanin hakan domin kuwa yaki amsan tayin da namasa na auran Hafsatu yakawomin azurin yanada wacce suka d'aid'ai ta a Nigeria take da zama azirga zirgan dayake tsakanin Nigeria da london suka hadu, har ya gabatar min da hoton ta sunanta Jumanah azahirin gaskiya yarinyar bataminba Hafsatu naso na hadasu amma sam yadage se waccer yarinyar mai ido atsakarka ganin banasu natakura masa yasa nazuba masa ido yayi yanda yakeso yayinda shikuma habu ya amince da zabin da nayi masa, haka itama Rabi ta gabatar min da wanda take so saide shima asalinsa dan Nigeria ne shima babban dan kasuwane yau yanaca gobe yana nan but yafi zama Nigeria, dan haka aka daura aure kowannesu,

Koda aka daura aure modi cewa yayi a Nigerian zasu tareda domin acewarsa amaryarsa tace bazata zauna inda yakeba because bazatabar dangintaba saide shiyabiyota suzauna acan domin bazata zauna inda ba kowa nataba modi duk abunda tace masa kamar yanka wuka haka zaidau lamarin a tak'aice dai yabita can Nigeria acan suka tare , itama Rabi tana can tareda mijinta a Nigerian karatunta da komai ya koma can, nida maihaifinsu wanda yake kwance jinya da habu da amaryasa mukadai muka kasance anan duk da shima habun bai wani cika zama sosai ganin yanda Balkisu take zama cikin kadaici yasa nace yadinga tafiya da ita matsawar bazata takurawa aikinsaba dan haka seyabi maganata yakan tafi da ita sa'i da lokaci kasan cewa itama karatu take bawai ta kammala bane inda take bangaran alkalanci,

Hafsatu ita kadai takasan agabana da batayi aureba tacigaba da karatunta inda take da burin zama shahararriyar barrister saide kafin kammala warta tasamu miji inda wani malaminsu yanuna ra'ayinsa akanta ma'ana yanason ya aureta aikuwa ba bata lokaci akayi auran, saide kafin agama warware gajiyan bikin rai yayi halinsa watansu 3 yayi hatsarin mota Allah ya dauki rayuwarsa tadawo gida muka zamana yayinda ta cigaba da karatunta

alokacinda Balkisu take dauke da tsohon cikin Ajmal a wannan yanayin mijina Alh Muhammad bature Allah yamasa rasuwa bayanda Balkisu tahaihu ta santalo santalelen jarumi d'an wanda yaci suna Muhammad anakirasa da AJEEMAL idan kinji ance Ajmal ananufin abu mafi kyau, mai kya , kyakykyawa, tunda suka haifi Ajmal sama da shekara 8 sannan ta sake samun cikin Kamal wanda kusan tare suka haihu da Rabi tsakanin muhaiseen da Kamal bai wuce sati 2 ba Saida aka hafi muhaiseen bayan sati 2 aka haifi Kamal shiyasa tsakaninsu ba yawa wanda tunda taga haihuwan muhaiseen Rabi bata sake samun wani cikin ba shiyasa ta dauki son dunya ta dau rawa muhaiseen because shi kadai Allah yabata,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.