Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 24
wani abun kakesone kafin takomacewa wani abu sejitayi yace ,"
d'agani ! dan tsaro ido Nisha tayi tana kallonshi kafintace ,"
indagaka zuwa ina ? "
Bed kawai taji yakuma fadi yana mai sake rungume pillow jikinsa da alamar sanyi yakeji sosai , kallonshi Nisha tashigayi sama da kasa yanzu inba neman magana irin na papan aheel ba ina ita ina iya dagashi , gaba kidayanta in aka hadata guri guda bata wuce lumansa dayaba ga tsayi gajiki tasan ba karamin nauyi zaiyiba to amma yazatayi tunda ya nemi taimakonta dole ta taimaka mishi yaka karfinta , dab dashi taje takuma tsugunawa ta dan janye pillow dinda yarungume ita kanta pillow seda tayi dumi saboda zafin jikin ajmal, dan koda ta matso dab dashi numfashinda yake fitarwa shima dumine jikinsa yayi zafi sosai,
da ganan Nisha shiga taimaka mishi wajan tashin takamo hand dinshi tadaura saman shoulder dinta dakyar da sidin goshi tareda taimakonsa cikin karfin hali suka samu daman mikewa , sede koda suka tashi taku daya zuwa biyu suka shigayin tangal tangal da juna ajmal karfenshi ya gaza because jikinsa ba kwari sosai bayajin karfi ajikinsa jikinsa duk amace yake haka Nisha taji yasake mata ragaman jikinsa gaba daya duk yanda Nisha tayi kokarin tallafoshi amma se jikake luuu ajmal na kokarin faduwa aiko cikin sauri da fargaban faduwar tasa Nisha taja hanusa da karfi suka fada saman bed tare kamar kifan mazar k'waila haka suka kife ruf ajmal yarufe Nisha da faffadan k'irjinsa ko burbud'inta ba agani, wani dugun numfashi ajmal yashiga saukewa jinshi saman lallausan bed din shi zamu iyacewa gaba daya ajmal baya cikin sense dinshi Sam yamance yana kwance kan halittan da adam ,
itakuwa Nisha tunda suka kife takasa motsi se zazzare ido tashigayi face dintama ba agani balle hancinta yashaki numfashi taririn zafin jikin ajmal sebugunta yake gashi bayida niyar dagata hala ko suma yayi taji shiru bai dagataba bugun heart dinshi da yanayin yanda yake sauke ajiyar zuciya duk tana iyaji , shikuwa mutumin jin dumin jikin Nisha yabashi wani yanayi mai dadi da kozari ajikinsa yasa yashiga sake tattarota jikinsa yarungume kamar yanda yasaba rungume pillownsa jinwani wawan runguma da ajmal yamatane yasa idanunta suka fito waje tsabar tsoro dakidima Nisha tasaki wani kara tana fadi'n,"
Wayyo Allah wayyo ummana zaikashenii.., tar ajmal yabude ido jin muryan Nisha datake sumbatu, cikin zafin nama dakarfin hali ajmal ya kauce gefe cikin sauri yasa hand yadafe goshinsa face dinsa yana kallon sama yarintsa idonshi, Nisha najin kaucewan ajmal tayi hanzarin zamowa daga bed din tana sauke ajiyar zuciya tareda tattaro numfashin ta dake kokarin tsayawa hanu takai tadauki mayafinta dake saman bed din Wanda yafice daga kanta tamaidashi mazauninsa , sidi sidi tasuma kokarin barin bedroom din kanta asunkuye hartazo bakin door tajiyu takai kallonta gareshi, lokacin harya yasan gyara kwanciyarshi yakai hannu yaja blanket yarufo jikinshi , Nisha juyawa tayi tafice daga bedroom din ajmal yabi bayanta da kallo akunyace yarasa wani irin zazzabine yarufeshi haka da har yakasa control kanshi har seda yanemi taimako,
rintse ido yakumayi gashide yarufe jikinsa da blanket but baisamu irin relief dinda yasamu dazu da yarungume Nisha ba amatsayin pillow shine mai wannan dumi me dadinba dan mintunan daya samu yayi ajikinta har yafara jin saukin abunda ke damunshi, gaba daya ji yayi ransa yadagule masa yarasa meke masa dadi , Nisha kuwa tana fitowa daga bedroom din tanufo downstairs gudu gudu sauri sauri haka take sakkowa idonta duk sun fito waje tsabar o, tana gama sakkowa taja ta tsaya ganin doctor fu'ad zaune bisa kujeran parlourn yanata faman Kiran line din ajmal,
ganin sakkowan Nisha arikece yasa hankalin doctor fu'ad dawowaa gareta wanda yasashi mikewa yashiga yimata murmushi, itama murmushin tashiga kirkirowa tana shafa gefen wuyanta daga nan tashiga dagawa doctor fu'ad gaisuwa, cikin fara'a ya amsa da mamakin yanda yariyar ta canza kyanta yagara baiyana dan da ace baisan tabama ba lallai yace yataba ganin taba ,"
mutuminfa nakirashi bai daukaba doctor fu'ad ya tambaya,"
yana bedroom din shi Nisha ta bashi amsa asanyaye,"
Alright barinaje naduashi doctor fu'ad na gama fadi'n haka yanufi upstairs tareda akwatin agajinsa yana kuma waiwayen kallon Nisha yarinyar akwai kyau da kwarjini ba amagana gurin yarinyar ga hankalin da nitsuwa ga kuma shiga zuci, yana isa bakin door din yatura door din yakarisa shiga bakinsa dauke da sallama yanda Nisha tafita tabarshi haka doctor fu'ad yazo ya taddashi idonsa arintse kamar mai bacci, ajmal jin bude door anshigo yasashi bude ido ahankali ganin doctor fu'ad tsaye kansa yasashi kara bude idon dakyau yana kokarin gyara zama doctor fu'ad dakanshi ya taimaka masa wajan gyara masa zamar ganin cewa yau abokin nashi jikin ba kwari sosai, "
sannu boss yajikin ?doctor fu'ad yafad'i tareda duba yanayin zafin jikinshi , "
tunyaushe kake fama da zazzabin maizafi haka? doctor fu'ad yakuma tambaya, Dan numfasawa ajmal yayi cikin cool voice yake fadi'n "
Problem din da kasanine ya tasomin after that bayan sallahn asuba zazzabi yabiyo baya , "
meye amfanin pills in problem din yatasu meyasa kakeson wasa da lapian kane ? "
I'm tired ajmal yafad'i yana Dan ya mutsa face, Dan murmushi doctor fu'ad yasaki yana kallon abokin nasa wanda ya hade gira yabata fiska "
Hmm naji tunda ka gaji dashan pills se ka sauke miskilanci dake kanka kafahimci rayuwar aure kadinga sauke hakkin dake kanka kabar cutar da kanka da bokiyar zamarka duk da nasan matsalar ka da ita amma hakan bazai hana katauyewa kanka hakkiba, so gaskiya inde zaka cigaba da cutar dakanka haka zanyiwa Daddy da ammi bayani Dan bazan tsaya insa maka ido kana kokarin cutar da lapiyar kaba , kana daya daga cikin maza masu bukata over so kama tayi katafiyar da lapiyar ka yanda yakama karka tsaya cutar da kanka because wannan problem din bakaramin effect garetaba lokaci daya zaiyi affecting naka ba tareda ka ankara ko kashirya masaba so you have to be very careful with that issue
ajmal shiru yayi yana sauraron zantukan doctor fu'ad duk da ba yau yasaba jinsuba yasaba tunatar dashi duk lokacin da suka kasance tare shima duk yarasa meke damunshi , idan yace baya bukatan mace yayi karya to amma feelings akan matarshine Sam bayida ita kwata kwata bayajinta aransa balle yaji shaawar neman wani abu daga gareta , some times itake bibiyanshi tana shishshige masa wani lokacin yabiye mata wani time dinkuma inta dameshi haka zaizame yafice yabata guri ,
duk da wani lokacin yakanso yiwa kansa fada Dan yasan ba karamin cutar da ita yakeba baya bata kulawar da tadace , to amma ya zaiyi rayuwarsace tazu da haka amma yana fatan canzawa , sauke ajiyar zuciya yayi yana kallon doctor fu'ad wanda ya mike tsaye yabude akwatin agajinsa ya zaro allura seda yayi arranging din alluran kafin ya kalli abokin nasa yana fadi'n,"
Allura zan maka wanda zazzabin zai sauka daga haka yanufoshi ba musu ya gara yamasa alluran daga bisani yakuma dauko daya alluran yakalli ajmal yace wannan kuma alluran baccine zan maka because kanada bukatan kahuta sosai nasan jiya baka iya bacciba , shide ajmal binsa yake da ido bayacewa komai harya gama alluransa ya kuma ya tsaya yana fadi'n,"
Zuwa anjima bacci zai iya daukanka kafin doctor fu'ad yagama ida zancensa seji sukayi anturo door anshigo Nisha ne tafe bakinta dauke da sallama tashigo hanunta dauke da try din abinci tanufi table din tsakiyar dakin ta ajiye daga bisani takai hanu tadauki cup din dake bisa saman try din Wanda ta hadowa ajmal hot coffee din daya saba sha yakeso especially yau datake tunanin baisa komai acikinsaba saboda rashin lapiyan da yatashi, dashi , gabaki daya zuba mata ido sukayi barinma ace doctor fu'ad yakalleta yakalli ajmal wanda ya zuba mata namujiya yana kallonta gaba daya itama Nisha setaji wani irin nauyin ganin irin kallon da suke mata , "
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.