Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 1 of 52

*🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.

We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors

We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.

AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.

Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

   *Littafina na siyarwa ne, idan kinsan baki biyaba dan Allah karki karanta, bazan miki Allah ya isaba koban fad'a ba dama Allah ishashene kowa sani, dan haka idan kinga daidaine seki karanta*

                0
Dukda nasarar shigewar da Abu huraira yae hakan be hanawa murfin motar dakar k'afarshi ba, da sauri ya rufe motar suka soma zarar ido suna bin halittar datayi burki tana kallonsu harshe a waje, bazasu iya gano ko wace halitta bace ba amma tabbas bazaki bane ba, hasken dake nan na farin wata baze basu damar ganin abun da kyau ba, sedai koma miye muguwar halittace kuma taso cutar dasu, haka tafi 1 hour tana zagayen su su kuwa se had'a gumi sukeyi dukkansu acikin mugun tashin hankali suke mara misaltuwa, daga bisani dabbar ta wuce abunta kuma, dukda haka sun kasa sakin jikinsu gashi k'afar ta Abu Huraira tana masa zogi, Allah ne ya taimakeshi amma ya bugu da kyau, Tawayen sane yaja masa qafar gaba man zafi haka sukai masa luddan gaske suka rage glass na motar sabida ventilation ya shigo sosai.

*************
   Yau daikam baccin ma babu wanda yayi shi acikinsu, da asuba haka suka daure suka cire tsoro suka sakko sukai alwala sukai salla, sun jima suna adu'o'i har gari ya waye sannan suka k'urawa inda suke ido, kowa hankalinsa atashe yake

"Abu Huraira ni wlhy tsoro nakeji, nagaji kuma inaso inje gun Mom ma" dama yasan halin rikicin d'an uwansa shi arayuwa bayason takura ko rayuwan wahala sam

"Haba Twin? Kayi hakuri mana, ya zaka sako zancen gajiya agun dababu alamun mutane ma bare musamu maceci? Wannan wurin abu d'aya zan sanar daku ku saka aranku cewan Allah ne kawai ze fitar damu a wannan jejin, so acire zancen zuwa gida yanzu, Allah dai ya rufa mana asirin mu ya nuna mana hanyar barin wannan gun acikin sauqi" Kallonsa kurin yae amma bece qala ba, hankalinsa atashe yake dan shima ya hango abin, ga basuda mai isashe danko rabin tanki basu dashi....

***********
   "Haj na sanar dake yaran nan suna lafiya, mesa kike hakane wai?, ni kinga yau zanje ghana tafiyar nan ta aikice ba fashi, bazanji dad'i ba ace wai na barki a wannan halin, ki kwantar da hankali, na tura su barde mota biyu da sojoji tare dashi mukaje kaita wancen lokacin yasan k'auyen inyaso su duba idan sun baro ne se aduba ko ina, bana tunanin komai amma an sanar dani wai wataqil sun saki hanyane, dan inka shiga jejin rud'u ne dashi amma babu namun jeji sosai a wurin dan haka kiyita adu'a, kinji" Nisawa tae yanzu kam

"To hakan ma yayi Allah ya tsare munkai su kuma ya bayyanar dasu cikin qoshin lafiya" murmushi yae ya shafi gefen fuskarta

"Ayita adu'a hajiyan general, Allah ya bayyanar mana dasu" Murmushi ta rakashi dashi kurun harya bar gidan.

******'''''''******'''''''*******
 
      Tafiyar nan dai anyita babu ji ba gani, amma ba alamun gari agaba ko kuma abayansu abu huraira, basuda wata torchlight seta waya, gabaki d'ayan hankulansu sun tashi, tuni man motarsu ya k'are qaf, gasu a tsakiyar jeji ba hanyan gaba babu na baya, suna gudun su taka konan dacen ne azo kuma idan anga abun tsoro ba wurin b'uta, acikin k'ank'anin lokaci duksun rame sun zagbe

"Bana tunanin shawarace me kya barin gun motar nan da yamman nan, kurun mu kwana kaman yanda muka saba, inyaso da safe semu soma cin kasar" jinjina kai Dawud yae cikin gamsuwa da bayanin Abu sufyan

"Hakan yayi, mu kwana amma fa idan muka cinye cake da wancen bushashen donut ko shakka banayi se yunwa ta hallakar damu idan bamu b'ulle tafiyar jejin nanba gobe, sabida bamuda sauran wata madafa" Girgiza kai Abu hurairah yae

"Allah yasoma acikin k'aramar jakar cen ta baya akwai cookies me yawa da cyama ta mana, bamuko tab'a shiba, idan zaku tafi mu kwashe bread da Baba ladi ta bari dukda ya soma sandarewa" Babu wanda yae magana yammakam acikin bayan motar suka kwana dukansu a takure rayuka ba dad'i.

***********
   Sallan Asuba kurun suka idar suka kama hanyar dasuke tunanin itace me b'ullewa, badan zukatan su sunyi na'am da bin hanyar ba sedan basuda wani zab'in daya wuce wannan.

***********

    Zaman shiru ne ya ratsa wurin na kusan dak'ik'u sama da hamsin kasamcewar hanyar dasuke tunanin itace har sukai tattakin binta ta b'acewa ganin su, mamakin ganin agaban wannan babban Tekun sukeyi tunda yake sun sandai mota bata tsallaka ruwa, kuma su sam basu bi wannan hanyar ba, agogo Abu sufyan ya kalla dake d'aure a wutsiyar hannunsa k'arfe biyar da rabi na yammaci, tun asuba suka kamo hanya da k'afa kasamcewar motarsu ba mai, gasu d'auke da kayan abinci na flour da ruwan sha, ga daddumar sallah, sun gaji iya gajiya idan ba wannan hanyar bace ba ana nufi juyawa zasuyi su koma baya kenan? Subar jejin yaushe? Koda yake har suka iso nan babu wara dabba dasuka had'u da ita idan ba tsuntsaye da k'adan garu ba,se kulb'a dasuka gani so d'aya jal! Shiru kowa da abinda yake sak'awa aranshi secen Abu Huraira yace

"Ku tashi mu mik'i hanya muga ko zamu kai k'arshen kogin nan, bana tunanin ma a Nigeria muke yanzu kam watak'il tunda kukaga ruwa idan muka tsallaka zamu samu hanyan b'ullewa mu fita daga cikin wannan doguwar hanyar mara hanyoyin b'ullewa danni fa a gaskia na sare ma da rayuwar gabaki d'ayanta"  Nannauyar ajiyar zuciya Dawud ya sauke

"Hakane mu zagaye mugani, tunda akwai ruwa da ikon Allah zamu akwai gari a kusa" Haka suka mik'i hanyar zagayen babban ruwan dabashida iyaka dan basako hango k'arshen sa takowane kwana.

Sunyi kusan awa d'aya babu labarin k'arshen ruwa ga magrib tayi duhu ya sauka sallah suka tsaya sukayi, da ruwan sukai alwala bayan sun idar suka karanci alkur'ani me girma sannan suka suka zauna suka jira zuwan isha suna idarwa suka kunna torchlight ta wayan Dawud dama irin me hasken nan ce ga wayar tana baiwa wata wayar charge ma suka qarayi gaba, basa so su kwana abakin teku, so suke suga wuri me yalwar fili sabida tsaro.

**************
  Hankalin sarkin atashe yake sabida yau saura kwana bakwai ayi sacrifice da rayuwar wani me tsautsayin tsallakar tekun ya shigo garin su, gashi har yanzu shiru, wani daga garin be tsallaka ba gashi wani daga wani garin be fito ba, idan har sati ya zago batare da ansamu wanda za'a sadaukar ba shi za'a yanka, kuma a k'ona iyalanshi da ransu, shekararsa ashirin da uku kan mulki wannan ne karon farko dayazo saura kwanaki bakwai batare da ansamo me tsautsayin daya tsallako ba koya fita ba, sun tura jirgi yakai bakwai amma shiru kakeji kanshibya matuk'ar d'aure....se zagaye yake a d'akin shishi kad'ai yana zare idanshi, batun yauba yaso ya kashe wannan bak'ar al'adar amma be samu dama ba har yanzu, duk yanda yaso bokan garin baya barin sa, shikad'aine sarkin dayae shekaru masu yawa ma, sauran duk basa wuce uku biyar zuwa bakwai, cikin damuwa matarsa ta kallesa da yaren dabaka gane wane iri ne tace dashi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.