Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 46 of 52

"Yaa hurairah marata ne ta murd'emun sosai bansan mesa nakejin hakan na" be juyo ba yace

"Zamuje kiga Dr. Da safe inaga wannan abinne da nakeji ana cewa juyi ne na yaro sannu" shiru tae sabida tsakani da Allah buk'atar sa take sosai bazata iya sanar masa bane kurun, shiru dukkansu na wani lokaci cen dataga kaman yayi bacci ta saki kuka me sauti kad'an harga Allah tana cikin buqata...

********
General ya gama yanke hukuncin sa akan yanda zeyi da Lawuri amma dole se matakin farko ya shiga gaban mataki na biyu tukunna, da wannan ya nemi malamin addini bayarbe ya d'auketa ya kaita gunsa domin ya mata bayani akan addini kuma ya gamsar da ita akam zata iya musunta domin d'aukar mataki na gaba.

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:02 PM] Maamah twins💕❤: 33***Banaso bana kuma k'aunar ganin kowa se Mazajen nan guda biyu, ko wanne inada dalilin son ganin shi, naji zanyi musulunci badan kowa ba sedan Allah, amma bazanyi a banza ba, banaso in koma garin mu, anan nakeso in rayu tare da Abu Hurairah kaman yanda kace kuna had'a aure kuma anan" kallon ta malamin yae

"Duk wad'an nan abubuwan bazasu yuyuba harsekin karb'i musulunci da zuciya d'aya, zan taimakeki har iyayen kima su karb'i musulunci da duka 'yan garin naku baki d'aya" shiru tayi

"Amma yanzu idan na shi kuma hurairan yace baya sona fa?" murmushi malamin yae sabida shi haukanta yake kallo, babu yanda za'ayi ya bari wannan yarinyar ta sub'uce masa

"Ai Lawuri musulunci da kike gami abune me matukar sauk'i, Allah ya had'a zukatan mu da samun sauk'i idan suka mik'a masa lamuran su, aure muk'addarine kedai idan musulunci zakiyi toki yarda dacewar akwai k'addara me kyau akwai kuma mara kyau, ki yadda da cewar kowace k'addara tazo maka daga mahaliccine, a labarin dakika bani naji cewar kinada wanda da zaki aura a garin ku to bakiga iyawar Allah ba tun a kansa? Tunda kikaga Allah ya rabaku ki d'auka cewar shid'in ba Alhkairi bane a tattare dake kingane ko?" Jinjina kanta tae cikeda gamsuwa da bayaninsa sannan suka tusa daga inda suka tsaya.

*********
"Zuwa zakiyi ki koma gidan da zama, ni babu yadda za'a nemi mayar dani uwar banza, ga zab'ina azo a wani ce wai dole se wacce lalatacciyar ta tare, shi General besan halina bane " kallon mom hanifer tayi

"Mom to akan me zance gidan amarya na tare? Kinga hakan ai shiga hakk'ine ko?" Kallon mamaki mom tanita dashi hadda su tsarabar rank'washi

"Ke wawiya ce why, Ita Cya zan turata ne gidan Abu sufyan, ke kuma zance ne kije gidan Abu hurairah kike rik'ewa matarsa ayyuka tunda yake tanada juna biyu, ai bawai zamu fito zahiran bane, a baibai zamu b'ullo musu" jinjina kai Hanifer tae

"Nagode mom" rungumeta mom tayi

"Farin cikina shine inga auren Abu Hurairah akan ki" murmushi kurinntae cikeda kunya ita adole ga surukarta.

Tunda ya dawo ya taradda Hanny agidan beji ajikinsa alkhairi bane ya kawota amma idan ma da wani k'udirin tazo shime maganin tane cikin ruwan sanyi

"Sannu yaa Hurairah ka dawo?" Ta tambayeshi cikin sakin fuska bayan fuskar nan tasha ado" kallonta yake yana mamakin Hanny sam ita bata fushi koma me aka mata

"Lapia lau, yau wuni aka kawo mana kenan" murmushi tae
."ai zama ma zanyi mom tace inzo in zauna anan, ba'a samo house help ba"

Jinjina kansa yae "To sannu da k'ok'ari ina Zuhrah?"

"Tana ciki, ni tunda nazo ma muka gaisa se kurun tabarni anan ban kara ganinta ba" Tab'e baki yae

"Batajin dad'i ne aikin sani" murmushi ta k'ak'alo

"Ea shiyasa ma na shiga kitchen ai, yayana da kaina nayi favorite d'inka semo da miyan egusi yaji kifi kuma" kallon ta yake tana bashi mamaki, yasan halin Hanny amma besanta da wannan sabon halin ba irin wannan kwarkwasan haka, k'ara tab'e bakinsa yae ya juya zuwa d'akin Zuhra yana cewa

"Thanks" a tak'aice.... D'akin da zuhra tae mata masauki ta koma ta shiga shirya wa cikin wasu kaya na d'aukar hankali....

A kwance ya taddata, kai tsaye kuwa wurinta yaje

"Zuhrah menene?" Kallon sa tae idanta ya d'anyi ja

"Jiri nake yawan ji, ga ciwon kai kuma inajin yunwa amma bana iya cin komai"

"Subhanallah sannu, tashi muje asibiti" kallon sa tae

"Ai inaga damun hak'ura ze sauka ne da kanshi" b'ata fuska yae

"Zaki fara mun wasa da lafiyan yara nane ko?" Batace komai ba adaidai lokacin wayanta ya soma bulayin neman d'oki, tanaso ta d'akko amma tana tsoron abinda zeje yazo, ringtone d'in kawai ya isa sanar mata da cewar yaa Faruk ne me kiran nata, kallon allon wayar yae wani zafi yaji ya taso masa amma seya kawar da kanshi ta hanyar barin d'akin

"Ki tashi ki sanyo hijab ki sameni waje" bata d'auki wayar ba harya tsinke a karo na biyu, da k'yar ta iya tashi ta wanke fuskarta ta sanyo hijab, a mota ma se kiranta faruk keyi tunda tace masa batada lafiya yake danna mata call har seda ta tsargu shi kuwa gogan se wayancewa yae tamkar be gani ba.........

*********
"Dama na barta ta tafi ne sabida in kashe su,tace sunan yaran Abu Sufyan da Abu hurairah , ka aika musu dodon tsafi su mutu ita kuwa a karkato da hankalinta ta dawo gida aure zan mata" kallon sa bokan yae

"Haba K'uru kafin ta tafi kyau in sani, kafin komai insan me zanyi, seda kanaso ta dawo zaka ce wani inmata aiki" Kawar da kanshi yae

"Kayi Hakuri Lantai, bani k'arawa amma dai yanzu kamata maganin suma a kashe su" wasu surutai ya somayi na hauka kusan mintuna ashirin kafin daga bisani ya kalli sarki k'uru

"Kafin wayewar garin gobe 'yan biyu sun zama tarihi, ita kuwa koda k'afane seta dawo gida na aika musu mutuwarsu yanzu" Tashi yae tsaye ya soma dirzar rawa sekace wani hauka sabon kamu......

*wannan littafin na kud'ine, idan kinsan baki biyaba karki karantamun dan Allah, mesonta siya seta tuntub'i wannan lambar 07084161619*

Tunda Abu Sufyan ya farka yau be k'ara samun nutsuwar zuciyar saba, wani irin fad'uwar gaba yake fama dashi mara misaltuwa, tun yana iya daurewa har ya soma jin ciwon kai da jiri, dolensa ya tattare komatsan sa yabar office cikin tsananin tashin hankali....

Kallon zuhra yae yau shima zuciyarsa a wani cunkushe yake jinta

"Ki yawaita adu'a zuhrah, shed'an yana tattali sosai wurin ganin yayi rinjaye a kaso 75 na al'amuran rayuwar ki, bakya sonyin azkhar, bakya sonyin nafila bakuma kyason tsawaita adu'a, bana miki fatan koma se Alheri zuhrah banida niyyan cutar dake, gaki da ciki irin wannan lokacin kyau ace kin fauwalawa Allah lamuranki, ki kuma sani martaba da darajar aurenki yana hannunki idan kin rik'e knki idan baki rik'e bama kanki, ki sani babu namijin daze aminta dake bayan kinci amanar auren wani tare dashi koda nan gaba k'addarar aure ta had'aki dashi kowaye shi anwurin ki kuwa, anan zan iya cewa dake Fatima kukan kurciya ma jawabine me hankali kad'ai kan iya ganewa, doguwar hanyar damuka d'akko nidake ya dace ki sani had'in bana mutum bane na Allah ne" jikinta ne yae mugun sanyi tama rasa me zatace, kaddai ya gano kiran da yaa faruk ke mata? Batace dashi komai ba kurin dai tayi murmushin yak'ene wanda akace yafi kuka ciwo.......... Ganin yanda Abu sufyan yazo ya shallake ta gabansa da wani mahaukacin gudu ya firgitar dashi, yasan yanda tuk'i wannan yayi yawa kam, wayarshi ya zaro yakira sufyan d'in, adaidai lokacin kuma shi ya kaiwa allon wayarsa kallo, beyi auneba yaji ammasa eban karan mahaukaciya, wata motar tazo ta ebeshi sunyi gaba, Abu Hurairah dake kallon komai hankalin sa ya tashi, ya k'arisa wurin yae parking yanata faman sharce uban gumi, yana kallon yanda ake kokarin ciro d'an uwanshi, jini ta hanci data baki ga wani uban yanka a saman cinyar sa daya ratso har kana hango naman jikin sa, gaba ki d'aya Abu Hurairah rikicewa yama rasa abinyi.....
Zuhrace ta kira mahaifinta atake yazo wurin aka kwashi sufyan da Hurairah da shima ga alama kanshi ya tab'u, se surutai yake suka nufi asibiti..

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.