Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 9 of 52

Kallon juna suke ko k'iftawa basayi daga shi har ita, seda ta gaji ta janye idanta, hannunta takai inda gefen k'irjinta na hagu naji yanda wurin ke harbawa sauri sauri kaman ze faso k'irjinta ya fito da sauri tace a mayar dashi...lallai tsafine, so yakeyi ya kasheta, me kenan haka takeji a k'irjin ta?

********
"Bana tunanin baza'a gane wannan shirin namu ba, ina tsoron azo asamu matsala gaskia, kar su cutar dakai Abu sufyan, tun jiyan nan seda na sanar dakai banso wannan shirin ba, dan Allah ku taimaka na mayar da komai nawa, idanfa mutuwar ce k'addarata anan tabbas sena mutu kome sabarar ku, dan Allah ku sauya tunani" Dawud ne ya karb'e zancen da cewa

"Nasan tsafine shisa nace kuyi hakan, idan tsafinsu akan wanda ya kashe zakin ne kaga baze kama Sufyan ba, tunda muka fito gida muke had'uwa da hatsarin rayuwa iri iri, kuma adu'a ce take bamu kyakyawar kariya ko yanzu adu'ar zamuyi" haka suka zauna suka dinga zuba adu'a kaman ba gobe kafin a kawo Jiqaqqen ruwan zaki.

*kark karantamun littafi idan baka biya ba, idan ka karanta kuma toh.....idan kanason ka siya ka kira wannan number 07084161619*
Mom Nu'aiym.
  
  
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

  *Lillatfina na kud'ine idan baki biyaba karki karanta dan Allah idan kin karanta kuma toh, masu son su siya ga number dazaku tuntub'a 07084161619*

   06

Kwana d'aya sukayi kafin su tarar da inda motarsu Abu Huraira take ajiye, ganin motar ya tabbatar musu da cewar lallai nan suka bi, amma suna ina? Shine tambayar da suka gagara baiwa kansu ansa, barde ne ya jagoranci ci gaban tafiyar sabida ya tabbatar akwai dalilin su na ajiye motar, kuma amaimakon baya gaba sukayi, dankuwa ko yanzu bayan aka tsinci motar.

***********
Shirye shirye kurun akeyi na yanda za'a gabatar da bikin sadaukar war da za'ayi nanda kwanaki hud'u masu zuwa, yayinda aka jiqa gawar Lamme (zaki) ana so yacika lokacin da akeso a baiwa Abu Hurairah, Lawuri dukda jikinta a mace yake hkan be hanata murna ba, za'ayi maganin wanda ya Rainata, yacika son stoma idanshi acikin nata,tunda take kuwa babu namijin daya tab'a kallon k'wayar idanta seshi, agarin tagwaye so d'aya aka haifa 'ya'yan albarka ake musu suma maza ne kowa yanaji dasu amma suma basu tab'a kallonta haka ba, yanzu ta fahimci irinsu d'aya da wad'ancen bak'in, shirinta tsaf tayi tayi kwalliyar daidai yanda ta saba, taja layi itada masu take mata baya zuwa filin daza'a shayar da Abu huraira ruwan, burinta kawai taga da kanta tana tsaye yasha ruwan harya mutu agabanta taga yanda idan na raini ze kalleta.......

Duk yawan yalwar iskar safiyar dake kad'awa hakan be hanawa Abu sufyan had'a gumi ba, baze iya kallo akashe masa d'an uwansa ba amma tabbas a tsorace yake, shi kanshu Huraira baya cikin nutsuwar sa ko kad'an, banda adu'a babu abinda suke aransu dawud ma haka ba wanda zuciyar sa bata tsere wurin dukawa amma hakan be dakatar dasu daga ambaton Allah daneman kariyar shiba.

**********
Mom yaukan tafi ko yaushe rikicewa, kwanaki nawa suka shud'e? Lokaci yanata kwaranya ba daddy babu kuma labarin shi dama 2 weeks zeyi ga wannan mutanen kusan sati da tafiya amma shiru, bata samun wayan kowa acikin su, ta kasa gane meke faruwa, Cyama dake zaune kusa da ita itama cikin damuwa ta kalleta tace

"Mom please yaran nan inaga da adu'a kika dage kina musu daze fi musu amfani akan wannan damuwar, mom wai kinga yanda kika rame kuwa mom? Dan Allah niki rufamun asiri ki tashi muje k'asa kici abinci semu zauna mu musu adu'a"
A raunane ta kalli yarinyar

"Cyama wazan gaywa kukana dacen banda Allah?, kowane lokaci kika ganni a damuwa shi nake gayawa, ko yanzu shina duk'ufa nake gayawa ina yin adu'a na tabbatar Allah ze amsa mini sabida shi maji roqon bayin sane" Rik'o hannun mom d'in tae

"Tunda kinsan hakan mom seki rage damuwa, kinyi imani da Allah tokuwa tabbas zakiga ribar imanin, dan Allah kici abinci, ban isa ince karki shiga damuwa ba dankoni ma ina cikin damuwar amma baxanji dad'i ba ace bakyacin binci" Jinjina kanta tae

"Shikenan Cyama muje, inshaa Allah zanna rik'aci Allah ya miki albarka" .

**********
A filin aka ajiye Abu sufyan shishi kad'ai su Abu huraira kamma suna cen gefe an ajiye su, ruwan aka kawo inda sarki k'uru yae bayani akan yanason ya cikawa 'yarshi Lawuri burinta, ta shayar da ruwan ga mugun da kanta, take agun aka yarda da hakan manyan garin sukace shine daidai hakan.

Kallonsa takeyi sosai amma shi sam yaqi ya had'a idanshi da nata, a yanayin data kula dashi ma kaman tsorace yake, batajin fad'uwar gaba, kazalika batajin wannan idan daya gagara had'a ido da ita mamallakin gangar jikin ne ya gagara had'a idanshi da nata, mesa takejin daban? Ya akayi takeji cewan ba wannan bame makashin zakin? Idan hakane kenan sanjiya sukai? Kenan so suke su juyar musu dakai, tajima tana tsaye amma kanshi a k'asa duk yanda taso ya d'ago ya kalleta amma abun yaci tura, waigawa tae ta kalli Babbar yarinyarta hadimarta me suna Linta tace

"Kicewa aakam ya kawo d'ayan yaron me kamada wannan" sunkuyawa tae ta amsa sannan ta juya cikin sassarfa, bata dawo ba se tare da Abu Hurairah jerasu akai gu d'aya tabisu da ido bata ko k'iftawa, kafeta da ido shina Abu Hurairah yae cikeda tsana, kallo d'aya ta masa tagano Abu sufyan bashi bane ainahin me kisan Lamme, bashi bane me sanya zuciyarta na harbawa so dubu saba'in acikin daqiqa d'aya ba, idan hakane mezai faru idan da an baiwa wannan ruwan? Amma ita sam bazata iya tonawa wannan me kallon nacin asiri ba, bazata iya furtawa da bakinta tace shi bane ba wannan me kamadashi ba

"Ku mayar dashi" shine abinda ta furta jikinta ba k'wari cikin murya me tsananin rauni, batasan wane kalan tsafi yae akanta ba, wannan waiko aljanai ne? Ta tambayi kanta, da kanta tayi tsaye seda taga yasha ruwan adadin yawan da ake buk'ata tana mamakin wace kalma ce yake furtawa kafin yasha ruwan menene yake furtawa haka?.....

Ihu suka hau yi ganin yagama shanye adadin copunan da akeso yasha, jira kurun suke suga macewar shi, amma shiru shiru har akafi tsawon mintuna talatin!! Ganin hakanya sanya barade soma dukanshi kaman ba gobe da manya manyan itatuwa, tun yana iya kaiwa kanshi kariya da hannunshi harya galabaita ya durqushe, Dawud da Abu Huraira se ihu suke suna k'ok'arin k'wacewa amma an rirriqesu, duka aka masa bana wasa ba, harseda ya dena numfashi, haka suka d'aukesi akan wani abu me kaman dogon baro amma wannan shanaye suke turawa sukai ta zaga garin dashi daga k'arshe sukai bayan gari dashi.

************
Duk yanda Dawud yaso ya basu hak'uri akan su basu koda gawar Sufyan ce abin yaci tura, acewar su sun jefar dashi ma acikin jejin da naman jeji ze cinyeshi, kuma ma tunda yasha wannan ruwan narkewa zeyi.

Abu huraira kuka wannan ma ya gagareshi, idanshi ya weqashe duk shi ya janyowa d'an uwanshi mutuwa,daya sani dashi yaje yasha, duk sa'in daya tuna da yanayin dukan da akamai akanshi seyaji hankalin shi ya tashi, yana jiyo amon sautin muryarshi yana furta
"Huraira ka taimakeni, huraira zasu kasheni" runtse idanshi yae sosai ya k'udurta aranshi seya nemo d'an uwanshi, jikinshi be bashi cewan ya mutu ba kuma a wannan daren ze fita.
********
Littafina na kud'ine kada ka karantamun idan har baka biya ba, idan ka karanta kuma tam. Me buqatar siya ya tuntub'i wannan lambar 07084161619

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.