Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 28 of 52

"Nifa Abu Hurairah inaga adu'ar neman tsari ya kamata mu nema da wad'an nan mutane, bawai kai kad'ai ba nida kaina seda na fad'a tarkon ta, da momy ta kula ta dinga mun adu'a aka saka malamai ma sunayi sannan na samu lafiya akanta, abu na gaba kuma idan ka kula da kyau zakaga cewar bamune muka koresu ba da kansu suka bar gidan kuma Allah ya gani munyiniyakar yinmu, yanzu me kakeso muyi" Nisawa yae cikeda damuwa

"Amma dukda haka baka ganin ya dace mu koma garinsu mu bincika kosun dawo, ka tabbatar fa cewar bawai sunsan hanya bane ba, bakuma wai sunajin yarukan garin bane, yarbawa kuma bawai lallai su taimaka musu ba" kallon tuhuma dawood yake masa cikeda mamaki da tunanin anya hankalinka d'aya kuwa

"Kana haukane Abu Hurairah, yanzu kai Allah ya tsamoka daga hallaka sannan kace zaka koma, kasani irin azabar damukasha da *Doguwar hanyar* damuka bi Allah ne kad'ai yasa munada sauran shan ruwa agaba, kuma banda Allah babu me iya mana wannan, bari kaji idan harkai so ya rufe maka ido ni badaniba bazan tab'a komawa wannan hanyar ba, dan inada hankali na, ko dama nifa kurun ina sha'awar mukai musulunci agarin dababushi ne amma ban shirya hallakar da kaina akan mace ba"

"Haba mana Dawood mesa bakwa tausayi nane wai? Mesa kakemun haka? Wlhy rashin ganin wannan yarinyar tamkar rasa wani b'angare ne ajikina, ka taimakeni"

"Tausayinka nakeji wlhy d'an uwana, dole zanwa mommy magana ma anema maka magani kaima dan wannan abun tashin hankali ne, ace dai duk uquba da azabar damuk sha a wannan *DOGUWAR HANYAR* har kake iqirarin zaka koma?" Ai wannan kasan bawai aikine na hankali ba" Shiru kurun ya masa harya mik'e yabar masa d'akin gaba d'aya.

************
Tunda yake maganar general kallonsa kurin yakeyi, mamaki yake yanda yaron ya k'wallafa ransa akan yarinyar ya sani uwarsa koze mutu bazata yardaba, kuma yasani tabbas idan be masa abinda yake soba akwai matsala

"Amma kai Huraira dolene sekaje da kanka? Idan neman yaran kakeso ayi kabari da kaina zan tura manyan soji suje garin amma bazan bari kai kaje ba" langwab'ar da kanshi yae ya marairaice fuska

"Dad ka taimakeni aje dani, dan Allah na roqeka, kuma ni base ka gayawa mom ba kurun dai nika barni i promise u zan tsaya bayan sir shamsu akoma meye" Shiru yae yana nazarin maganar sa secen yace

"Idan kun tashi kubi ta wannan ruwan, ta garin wannan fulanin wannan jejin yanada matuk'ar hatsri, zan maka adu'a kakuma tabbatar hadda yad'uwar musulunci ya sanya kakeso kaje da wannan Allah ze dafa maka" haka yae godiya ya tashi murna fal aranshi.

**********
Tunda yaje gunta suke magana da 'yan kalmomin daya iya na yarbanci, komai shine yake shige mata gaba tanayi, sunyi shak'uwa me yawa, a hakan kuma yake mata hausa, lokuta da dama tare suke kulawa da ita shida Ayusher ko yanzu atare suke suna hausa suna yarbancin dasuma tsinta gwanin dariya, danma tanada kan kamawa sabida acikin 3 weeks harta soma iya mayarwa da hausar, ita kuwa Ayusher baiwar Allah har ita ake koyon yarbancin sabida tanaso taga Abu sufyan acikin farin ciki, kuma zaman yarinyar agidansu ya k'ara janyo kusanci a tsakanin su sabida kusan kullum yana gidan..

Mik'ewa yae ze tafi ya soma sallama dasu, kurun se Lawuri ta soma kuka akan zata bishi, hannunta ya rik'o duka biyu

"Má binó Lawuri (kiyi hak'uri Lawuri)" Langwab'ar da kanta tayi cikin shagwab'a tace

Igbawo lóma dé ? (Yaushe zaka dawo)

Murmushi yae yaji me tace amma besan meze ce mataba da
yarbancin se cewa

"Da sassafe gobe" sarai ta fahimce shi setayi murmushi tace tana zare hannayenta

"Odaró (seda safe)

Ta furta tana me juyar da kanta alamun btaso ya tafi, takaici duk se ya kama Ayusher amma seta had'iye kurin itama ta soma rarrsahinta da hausa.

Abu sufyan yabar wurin cikeda begen Lawuri yanaji aduniya baze tab'a iya yafewa waninsa itaba har abada.

**********
Shirin tafiya sukayi akan shi Huraira zashi tafiyar aikine sokoto, adu'a sosai mahaifiyar sa ta masa sannan yabar gidan, inda akayi zasu had'u da sojojin anan suka had'u general ma yayi adu'a sannan suka kama *Doguwar hanyar* dasuke fatan binta a wannan karon ya zamar musu alkhairi.

Niko nace Allah ya fitar ga A'i ga cinikin rogon ta kodai ta fad'i ko taci riba.

*********

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

 

*Littafina  na kud'i ne, dan Allah idan baki siyaba karki karantamun, kokimun ki tura wani gurin, bana Allah ya isa bane amma dai haqqina yana wuyan wanda ya aikata d'aya daga ciki, kuma koda ban fad'a ba duniya shaidace akan Allah isashene. Idan har kina buqatar karantawa ki nemeni ta wannan lambar 07084161619*

       19
Zaro wayrsa yae daga aljihunsa cikin takaici dan sosai ta dameshi da ringing, ganin Al hussain da yae yana kiranshi yasa ya d'aga cikin mamaki

"Mekenan haka kayi bro? Mesa zakamun haka?" Kishingida yae ajikin kujerar  motar yana lumshe ido

"Me kuma nayi maka?" Ya furta cikin mamakin kalaman d'an uwan sa

"Dad ya gayamun komai, Amma na sanar dakai yaran nan basa garinsu fa mesa zaka nace akan sekaje?" Sumar kansa ya shafo zuwa sajensa har zuwa gemunsa yad'anja a hankali

"Wane yaqini ne dakai nacewar basa garin su? Hakan yana nuni ne da cewar kasan inda suke kenan?" Se a sannan ya gano wowtar da yae na furta hakan

"Da nasan inda suke yaya zan barka ka tafi a banza? Kurin dai ni nasan basu san hanyar bane ba ko alama, kuma naga k'afarka har yanzu kana d'ingisawa ai"

"Wannan ba damuwa bane kaidai bakaso ka joining hand dani mu taimaki musulunci, baka kuma so in smu abinda nakeso so kayi abinda ya shafela plss ni zanyi nawa"  mamaki sosai kalaman sa suka baiwa sufyan

"Bro abin yakaimu haka mesa zakamun wannan maganar" tsaki Huraira yae

"Sufyan plss pray for me if u can, babu abinda zaka gayamun yanzu, banaso mui wata doguwar magana yanzu plss" yasan halin huraira tunda yace fushin yake da gasken kuwa shiyake mutunci d'aya zewa kanshi ya barshi for now, da wannan yamai adu'a kurin yana mejin zafin zuciyarsa duk yanda yaso ya sanarwa d'an uwansa gaskia zuciyar sa ta hana.

***********
    Yau duk sukuku Sufyan yake har Lawuri ma ta fahimci haka seya kasance basu wani hira, tunanin d'an uwansa duk ya dameshi, shibesan meke damun saba, zama kusa dashi tae ta shagwab'e fuskar ta amma ta rasa ma me zatace masa, da k'yar ta tattaro kalmar

"Kiló shiyé lèni "Meke damunka yau" be fahimta duka ba amma tabbas ya gane abnda take nufi, murmushi ya qaqaro

"Ba komai fa Laure" Langwab'ar da kanta tae adaidai sanda Ayusher ta shigo d'akin da sallamar ta hankalin ta yana kan yanayin sa dakuma yanayin zamansu, zama tae ad'an nesa dasu idanta yana cikin nasa

"Sannu" shine abinda tace dashi kurun ta kawar da kanta gefe d'aya cikin takaici

"Menene damuwar kuma? Naga duk kin canja" ya tambayeta cikin nuna kulawa

"Ba komai idan ka gama abinda kake zan jiraka a babban parlor akwai maganar danakeso muyi" jinjina kansa kurun yae

"Muje a shirye nake, kallon Lawuri yae ya shafi sumar kanta

"Zan dawo yanzu kinji?" Ya furta cikin harshen hausa, gyad'a masa kanta tae danta fahimci me yake nufi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.