Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 20 of 52
*Ni kaina tuna nina ya tsaya cak akan wannan al'amarin! Bana fahimtar yaren mom, anya bata nemi tarwatsa mana farin cikin mu ba kuwa? Ko shakka banayi mun qara lulawa ne wata *Doguwar Hanya* mara b'ullewa.........*
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐โค: *๐๐DOGUWAR HANYA....๐๐*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Littafina na kud'ine, idan kana buk'atar ka siya seka biya ka siya, me so ya tuntub'i wannan lambar 07084161619*
13
Kallon Khaleed Oga Shamsu yae
"Kabi mana ghali da yarancen, karsu wuceka fa, koma dai muje taren ja muje" Haka suka ja suka bi bayan ghali dasu Lawuri, ganin ya d'auki hanyar fita gari ya sanya suka sha gabansa damai alamar ya tsaya, sauka yae daga kan titi ya gangara k'asa, suka paka gaba d'aya Oga Shamsu yace dashi bayan sun firfito
"Ina zakaje da yaran nan?" Cikin tashin hankali yace dashi
"Hajiya ce tace na saki cikin gari zuwa barin gari, idan munje a jeji na saukesu na dawo" Girgiza kanshi yae dan dama general yace ya sanya mai ido akan su
"Ka koma dasu gida, kuma ko bana nan aka k'ara sakaka aikata wannan mugun abun ka sanar dani tukunna, kaji dai abinda nace ko?" Girgiza kanshi yae ya shiga motar sa da sauri, shima kuma suka juya suka rakasu har gida, koda suka Dawo Mom hankalinta a kwance tayi sa'a ta rabuda k'aya agidan ta, Oga shamsu ne ya shigo tare dasu da sallamar sa, amsawa tae tana me kallonsa cikeda mamakin ganin su Lawuri a bayansa
"Shamsudeen lafiya dai?" Matar oga ma oga ce sabida haka ya russuna cikeda ladabi yace
"Yarannan dalilin su aka barni agarin nan hajiya, dukda yake tafiyar nan ta aikice ko oga bashida halin hanani yinta amma tunda yake ya isa seya mun umarni da kwana tsaye k'yam akan kulawa dasu, kada ki manta basu san *Doguwar hanyar* da akabi akazo nan ba, basusan Allah ya halicci wata aba wai ita mota ba, zama acikinta ma tsoro yake basu, maza ma dasuka shiga jejin da hanyar garin su take sun girgiza sun tsorata bare kuma mata, hanyar garin nasu bata Abuja ake biba sam cen wata nahiyar ce, na tabbatar bazasu shekara anan ba, General seya saka an mayar dasu gida, ina rok'on alfarma kiyaye hana su fita konan dacen idan bani akeso na musu wani abinba da kaina kokuma wanda suka kawo su nan garin" Cikin Takaici ta kalleshi yaunya hango b'acin rai sosai a idanta game dashi
"Zan kiyaye ubana, sedai kuma kai seka kiyaye gayawa wani wannan maganar, kakuma tabbatar ka baiwa uban gidanka shawara akan kwashemun tarkacen maguzawa agidana dazaran ya dawo dan banason ganin su" murmushi yae irin na matar soja se soja
"Angama hajiya, yana dirowa agarin nan zan bada wannan shawarar sabida ki samu salamar zuciya, amma yanzu dai abasu masauki"
"Ka koma gunku naji" Mik'ewa yae su kuma duk sunsha jinin jikinsu musamman wata uwar harara data bisu da ita kafin ta haura samanta ranta babu dad'i, koda batajin yarensu tana fahimtar dalilin fad'an su akansu ne, takula sam matar tunda ta dawo bata na'am da ita sam! Hankali ya tashi ainun wannan ya sanya a darare ta zauna a
Cikin parlor zuciyarta babu dad'i tana tunanin wannan bak'ar rayuwar data wurgo kanta aciki.
************
Duk juyin sa d'aya da tunaninta yake kwana yake kuma tashi baya k'aunar abinda ze sanya yae nesa da Lawuri kome k'ank'antar sa, ya gagara sukuni yakuma rasa mecece ainahin damuwar sa da ita? Idan abinda yakeji a zuciyar sa game da ita shine so to tabbas kuwa so beyi masa adalci ba, mesa acikin dukkansu seshi kad'ai? Mesa zega jarabawa akan wannan *DOGUWAR HANYAR?*, be samu bacci ba se bayan asuba wannan ne ya sanya shi makara bayan nan, be farka ba se after 11, seda yae wanka da komai ya kimtsa sosai cikin kayan da Abu sufyan ya ciro masa sannan ya fito ya fito waje, ya takure ya taradda su acikin parlor susu kad'ai suna zare zaren ido, kai tsaye kusa da ita yaje ya zauna ya ajiye sandarsa dayake doddogara k'afa sannan da hannu ya tambayeta alamar lafiya? Murmushi ta k'ak'aro cikin yak'e ta girgiza sa masa kanta alamar ba komai, sam be yarda ba wannan ya sanya ya nuna bakinsa alamar cin abinci sunci kuwa? Amaimakon ta bashi amsa seta sadda kanta k'asa kurun, Barbo ya kalla ya tambayeta ta girgiza kanta alamar aa, cikin tsananin mamaki ya mik'e da sandar sa zuwa kitchen
"Sannu Baba Ladi, me ake girka mana ne?" Ya tambayeta yana me sakar mata murmushi
"Yauba wani abinda mukai se kunu da k'osai seko soyayyan dankalin hausa, zaka ci kona sauya maka zuwa wani abun?" Girgiza kanshi yae
"Ina hanifer da cyma? Mesa ne yarancen basuci abinci ba?" Dafe baki Baba ladi tae
"Toh nidai Hajiya ce tace dani tun safe karna girka dasu, shiyasanya kaga ban girka d'inba" B'ata fuska yae mesa mom take haka ne? Ta sauya da yawa d'an adam ai ba'a horonsa da yunwa fisabilillah, gaskia beji dad'i ba
"Baba kozaki girka mana Indomie da k'wai dukanmu plss, kinga zaman da yunwa ba dad'i ko?" Jinjina kanta tae
"Mezai hana kyautar Allah? Mintuna goma sha biyar zakaga na had'o na kawo da yardar Allah, ta furta bayan ta juya zuwa store, shid'inma gunsu ya koma ya zauna dukkaninsu suka k'urawa TV ido kowa da abinda yake sak'awa aranshi ko shakka babu seta nemi hanyar gida wannan shine abinda takeso tayi yanzu, shi kuma tunanin yanda ze rufe mata jikinta yake, sumar kanta ma duk a waje ba d'ankwali ba hijabi, dole ya kaita gun mace me hankali ta rik'a kimtsa masa ita.
***********
Zaman office d'in baze masa inhar beji halin da Lawuri take ciki ba, ina ze iya wannan badak'alar ta tashin hankali, besan mesanya wuya ta zab'e saba hankalinsa kaf da nufsuwar sa baya tare dashi seya ganshi kusa da yarinyar nan, kodai tsafi sukai masa? Banda haka inashi Abu sufyan ina Lawuri? Yaje ina da ita? Zuciyar sa se azalzalar sa take akan ya tashi yaje gida ya ganta, ko shakka bayayi batada abokin hira shishi kad'ai ne ya iya yarenta da kurmanci, danshima bekosan yanda akai suke gane maganganun juna ba, takardunsa ya harhad'a ya fito daga office d'in, yana hurzo iska me zafi daga bakinsa, kai tsaye Airport ya soma nufa inda ze karb'o sak'on agogon hannunsu da aka k'ara yin sababbi kowa da kalar nasa, dama shi Baki yake using Abu Huraira ke amfani da fari, daganan gida ya wuce ya shiga ciki a sukwane, yanxun ma susu kad'ai ne a parlor d'in tarasa yanda zatayi da rayuwarta matar gidan ko k'ara sakata a ido basuyi ba, ga 'yan matan dake kula dasu ma ba kowa acikin su, ita bata gane kan gidanba tun zuwan matar cen da Dawood yace mata mahaifiyar suce. Sallama yae ta amsa masa sabida ta haddace da fara'a d'auke a fuskar sa ya k'arasa ciki, kallo d'aya ta masa ta gane shi cikin sakin fuska tace
"Aboo shufyan sannu" murmushi yae
"Lallai Lawuri an gwanan ce, irin wannan rik'e abubuwa haka ba wuya" kaman taji meyake cewa setayi murmushi, da hannu yamata alamar sunci abinci, gyad'a masa kanta tae alamar e, yana murmushi ya mik'e yake nuna mata yana xuwa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.