Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 38 of 52
"An gayamun komai Rose karki damu, sannu, nayi alqawarin dama zan jiraki bazan tab'a aureba se sanda Allah ya bayyanar mana dake nayi kewarki, nayi rashinki Rose nagidewa Allah daya amsamun adu'a na akan ki dawo mana" Murmushi tayi cikin fad'uwar gaba
"Nagode sosai da karamci yaa Faruk Allah yabar k'auna" Murmushi yae
"Rayuwar jejin ce ta sanya kika manta da sunan dakike kirana dashi" Cikin hikima ta zare hannunta daga nasa koba komai ita matar aure ce
"Na isa in mata dan Mon cherie na?" Ta fad'a tana murmushi" yanzu nashigo grin kuma gobe zan koma aiki nake dashi sosai a office wlhy, amma inshaa Allah zanyi qoqari in dawo friday kinji" godiya sosai ta masa sannan suka rabu.
**********
Lawuri babu wanda takeson gani sama da sufyan a wannan lokacin, takasa gane me take a nan, tanaso ta kalli TV ma taci shinkafa da spag ba kullum.naman jeji ba, kullum setawa iyayenta kuka sedai su rarrasheta akan tayi hak'uri, haka dukta lalace Barbo dai tana nan tana aikinta na bauta, memory ya gagareta tunano komai sedai zare ido da take, saurayinta kuwa anan nan ana shirin d'aura aurenta dashi.
*********
*Bayan sati hud'u"
*menene yake damunki kike b'oyemun Zuhrah? Sekin sanar dani dalilin ki nayi ramar, na amaye amayen nan dana yawan bacci, alamomi sun nunar mun cewar ciki ne dake, abinda kika mana kin kyauta kenan Zuhra? Cikin shege kika dawo mana dashi?" Sadda kanta tae k'asa cikin hawaye
"Ummana kiyi hak'uri wlhy ba haka bane ba" Wanka mata mari tae
"Ba haka bane ba ubanki ne? Bari Daddynki yazo wlhy asibiti zan kaiki" ta rasa ta cewa, yaya zatace aure tayi a ruga? Yaua zatace hakan bayan zuwa yanzu ta cire ran zata k'ara sanya Huraira a rayuwarta, ga yaa Faruk zancen aure yake shida iyayen sa, ina zatabi taga haske
."baki kyautawa kanki ba zuhrah, kin cucemu wlhy kuma kema kin cuci kanki" Kukan tane ya tsananta ta tashi da gudu zuwa d'akin ta.
**********
Yanzu kusan watanni biyu kenan, duk sanda ya d'aga takarda da biro ya rubutawa zuhra saki seyaji baze iya ba, tayaya ze mata haka batare da shawararta ba? Dole yaje ya gaya mata niyyan sa, to amma idan ta nemi alfarmar ya bar mata igiyar aurenta fa yacewa su dad mene? Ya rasa ta ina ze b'ullo, wannan doguwar hanyar har yanzu yana cikinta tsundum, ina ze kallesu yace yayi aure? Shi dama ace be keta mata haddin taba da abin yazo masa da sauk'i amma tausayinta yakeji, Anya Allah ze barshi da wannan nauyin kuwa? Hakk'in aure ko d'aya baya sauke mata, yanzu katsam se ya aika mata da saki? Yarasa tudun dafawa yarasa dawa zeyi shawara ga zancen hanifer ana masa, ga Lawuri zaune rad'am akan sa ina ze tsoma rayuwar sa shikam?.
*******
Tunda akazo asibiti aka tabbatar cikin ne na watanni biyu da kusan sati uku hankalin iyayen na zuhra ya tashi, duka kam ta shashi agun umma
"Banza dabatasan darajar kanta ba, kinje kin zubar da k'imarki, baki tashi dawo mana gidan ba seda tsarabar shege, me kika nema kika rasa? Wane gatan bama baki? Nasoma tunanin k'arya kike babu wasu mutanen dasuka saceki, damacem yawon duniyar kika zab'a, yanzu me zamu cewa Faruk da iyayensa? Me zamucewa duniya? Kin gama wulak'antamu zuhrah, ban tab'a tsammanin cewar ke d'innan zaki aikata mana abinda kika aikata mana ba, kin sanyamu a rugun tsimi wlhy bakiyi 'yaba zuhra, acewai ke da cikin shege" kuka ta sakawa uwar
"Mom ba haka ya dace kimun ba, kiji tausayi na wlhy ban tab'a aikata zina ba, ba cikin shege bane ba" wanka mata mari tayi
"Baki tab'a aikata zinaba a ruwa kikasha dan ubanki? Ba cikin shege bane cikin uban meye? Idan baki dena magana ba sena hallakar dake wlhy anan, shak'eki zanyi kuma ki sani keda kika lalata rayuwar ki ke zata kwab'ewa ki jira hukuncin daddy wlhy sekin gane shayi ruwane banza mara hankali" duk yanda taso sun gagara saurararta dad ya kalleta cikin qunan rai yace
"Zuhra bari kiji, wlhy bazaki haifen shege agidana ba, kije cen wurin ubansa ki haifa masa shi idan kika haifeshi kika damqawa uban ki nemi wasu iyayen bamu ba, ashe dawowarki ba alkhairi bace agaremu? Ashe ke d'in nan tauraruwace me witsiya ina yabonki salla ki kasa alwala zarah? Lallai kibar gidan nan yau base gobe ba"
Kallon sa tsae
"Daddy wlhy bam tab'a aikata zinaba, ba shege bane ka saurareni kaji" dukanta ya shigayi ba shege bane inaga ubanki ne ko?, zaki tashi ki tattara kayanki ko kuwa?" Haka ta mik'e tanata sharar k'walla, taje ta gama had'a kan kayanta da dama ta bari batasan me duniyar yanzu ta k'unsa ba, hatta wayar da aka bata tana dai dannawa ne, ta d'auki zinarinta da kud'in b'arayin nan da Huraira ya bata ajiya tabar gidan cikin bak'in ciki.
*******
Yaudai Huraira se munanan mafarkai yakeyi da zuhrah, da wannan ya shirya ya d'auki hanyar dazata sadashi da gidansu Zuhran......
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐โค: *๐๐DOGUWAR HANYA....๐๐*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Book nawa na siyar wane, idan kinsan baki biyaba karki karatamun kuma karkiyi forwarding ma wasu groups, idan kina buqatar siya ki neki wannan number 07084161618 kokuma 08030811300
27
Yayi kyau sosai, ya d'auki wanka iya wanka, ya shirya zuwa suyi magana ta fahimtar juna, so yakeyi ya sanar mata cewar ga abinda ya shirya, yayiwa kanshi alk'awarin idan zuhra ta zab'i zama dashi a matsayin mijinta amaimakon su rabu ze karb'i k'addarar sa, a yanda yake gani Lawuri ba Alkhairi bace arayuwar su shida d'an uwansa dukda har yanzu yanajinta k'asan zuciyar sa, Hanifer kuwa se yanda Allah ya tsara be tab'a dama soyayya da itaba itane take k'aunar sa ya zeyi?.
Ata wajen gate na gidan yae parkin motar sa ya fito kai tsaye wurin me gadin gidan ya nufa, yana zaune san benci na katako, hannu ya mik'a masa suka gaisa sannan ya zauna akusa dashi
"Malam dan Allah Fatima nake nema" kallon sosai me gadin ya masa sannan ya waiga ya kalli gate yaga bame zuwa
"Bintu wai kake magana?" Tunawan da yae sunan data gaya mai mahaifiyarta na kiran ta dashi kenan ya sanya yace
"Ea ita nake nema gunta nazo" tab'e baki yae ya jinjina kai
"Aikuwa malam dama ka dena wahalar da kanka indai fatima ce dan kuwa da cikin shege ta dawo, nima me aikin gidan ke fesamun tamusu lab'el taji komai, inda na tabbatar da cewan hakanne ganin ta fito janye da jaka tanata sharb'ar kuka, Allah na tuba kowa ya zata saceta akayi ashe yawon duniyar ta taje se yanzu gashi ta dawo wa iyayen ta da tsarabar shege" Cikin hargitsi Abu Huraira ya kalleshi
"Ban fahimce kaba malam?" Ya tambaya yana kallon gate man d'in a yamutse
"Bawan Allah, yarinyar nan gidan Bintu wacce ta b'ata shekaru uku bata nan daga sunan zuwa bautar k'asa, watanni biyu da suka shud'e ta dawo sega ciki yanzu ya bayyana ajikinta rad'am na shege, an tambayeta uban tayi shiru shine aka korata ubanta ya koreta, idan matar aure kake nema tun wuri ka sanyawa dokinka linzami" zuface ta shiga tsatsafo masa tako ina, mekenan ake nufi, tarawar da yae da zuhra kenan rabo harya rantse kumama wai har ansoma zargin ta agidan su shi yanzu mezece a yarda dashi, waye shi dazeje yace dasu shine uban yaron kuma aure aka d'aura musu, godiya yawa me gadin kurin yabar gidan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.