Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 48 of 52
"Amma ai ya kamata kasan menene suke cewa, yanzu ace anan nahiyar akwai abinda ze gagari tsafin ka?" Shu'umun murmushi yae
"Ada babu amma yanzu akwai!!!! An samu a wata duniyar da damu bamusan dashiba me burgewa kalli yanzu suke rayuwa ma, dolene sena hallak'ar da yaran nan biyu saura musu kwana uku duk aljanan jikinsu su gama cinye musu hanji su gama tsiyayar musu da jini inyaso duk su mutu!!" Murnushin mugunta k'uru yae
"To Lawuri fa zata dawo?"
"Zata dawo dole ma, tunda farko kaine ka turata baka gayamun ba ai" cikin takaici ya kalleshi
"Ainasan kanada k'arfin ikon dawo da ita koda ta mutune, sabida haka nace taje danaga ta damu yanzu kuma suka dawo da ita, kuma ka kafeta anan bata sha'awar k'ara zuwa wani wurin su kuma a kashesu dukansu uku har wannan dasuke cewa Dawood" Wak'a da hauka ya somayi take hoton dawood ya bayyana yana zaune yana shan tea a hannun shi, wata k'ara ya k'walla ya nunashi da bindin dokin dake hannunshi yae wasu hauka sekuma ya kalli k'uru
"Su mutu a rana d'aya?" Da sauri k'uru ya d'aga kanshi alamar e, wani shirme ya somayi take agun Dawood ya soma tari tamkar tea d'in ya sark'eshi daga haka se aman jini bako k'akk'autawa, momyn sa dake zaune kusa dashi tana shan tea a take ta rik'eshi ta soma tambayar sa menene, ganin abun ya wuce wuri ya sanya ta soma kiran k'anwar sa, da gudu tazo, alk'ur'ani me girma ta d'akko ta soma karatun sa da k'arfij sauti, bata gushe agunba seda ta tabbatar ya dena, duk wannan abun dasukeyi Boka dasu k'uru suna kallonsu acikin k'warya, ihu suka k'walla ganin k'waryar ta boka ta koma koriya shar, wannan abu shine na farko daya faru a garin tun bayan samuwar mafarin al'ummar su, haka ya dinga gunji cikin k'araji da surutai bako k'akk'autawa bashiba hatta su k'uru sun rud'e da wannan al'ajabin.
*******
Babu shakka su twins suna cikin tashin hankali, abun ya soma wuce tunanin general ido ya k'ura musu yana tunanin mafita yanzu kam, sabida ba shakka akwai damuwa a wannan hatkar duba da yanayin su a wannan lokacin idanuwan su sun kad'a sunyi jajir tamkar an zuba musu jini ajiki ga fatar jikinsu ta soma tamurewa tanayin fari sekace wanda ya shekara be sgafa mai ba a lokacin da ake kwarara uban sanyi!!!!
Wayar sa ya zaro ya kira malam, bayan sun gaisa yake snar masa yazo asibiti, shisam yama manta da wata Lawuri ya kula kamr wannan damuwar da yae da ita soyayyace yanzu kuwa ya dena ji mezai damesa?.
Koda malam yazo yashiga rud'u sosai, umarni ya bayar akan a mayar dasu gidansa, wannan abun koba menene iskane kuma a haka yakeso ya kashe su, da wannan shi kanshi malamin seda ya kira mahaifin sa sabida yana ganin abun yafi k'arfin sa.......
Dawood kuwa sedaga baya abun ya k'ara tashi masa, inda atake mommynsa ta tuna da zancen su Twins,kai tsaye mom twins ta kira suka tabbtr mata ga inda aka wuce dasu, ita kanta alfarma ta nema na wucewa da Dawood shima a tallafeta a dubashi san gaskia baida lafiya.
******
Lawuri kuwa tana zauna aka kawosu, sam ko alama bata gane suba sedai ta gane daddy ta kuma gane Oga shamsu wanda idansa ke kanta, yana mamakin yanda hasken musulunci ya gama karb'ar fatar jikinta!!! Tayi sumul abunta dukse yaji ta burgeshi haka aka kwana ana abu d'aya karatun alk'urani ake yi da adu'a ana tofesu dashi amma se a hankali sauk'i d'ayane daya zamana yau duk basuyi aman ba, amma bnda haka babu abinda ya sauya na dangane da halittar da suka dawo su dukansu, haka haka dai aka bar su kwana anan, Lawuri jin cewar sune tasha kuka dan Dawood kurun ta gane ita kanta duk wata soyayyar datake ma Abu Hurairah jin take a irin yanayin datakeji yanzu badai soyayyar aure take masa ba, gaba d'aya hankalinta da nutsuwarta sun karkarta akan ciwon su itama adu'a tashiga yin musu babu k'akk'autawa.
Boka ya fusata dan haka yau yace aje lallai a kashesu, dan aljanan tsafin sa sun sanar dashi lallai suna samun barazanar wannan littafin dasuke karantawa ko yanzu ma da k'yar suka sha, umarni ya basu akan su kshe su yau har Dawood yaga tsiyar shi d'an sarkin tsafin k'asar ne kuma ya jima yana gagarar kowa yaya za'ace mutanen wata k'aramar al'umma su fishi iya tsafi!!!
An je sallan azahar an barsu se lawuri dake salla a d'akin tare dasu, gunjin kukansu da gurnanin da suke shine ya sanyata zanzarin son ta kammala salla taji menene? Da gudu gudu ta idar da sallar, abinda tagani ajikinsu susus uku yafi komai bata tsoro, tunawa tae da azaban da mahaifinta ya saba baiwa mutane idan sun masa laif agarin, tabbas duk sukai haka daganan zasu shek'a lahira da gudun fanfalak'i, waje tae tana ihun kiran malam su kuwa har lokacin sallah sukeyi, gashi ta tabbatar cewar daga garin sune wannan mugun abun!! Ilahirin jikinta tsuma yake ganin basu idar da slla ba ya sanya ta koma d'akin da gudu abinda ya saura su gangara shine jini a baki!!!! Ko shakka batayi wannan mugun abun ne ze kashe su, ga jikinsu yanata tsagawa jini na fita duk sun dawo sekace wasu fatalwa! Tana nan tsaye har su malam suka shigo da daddy malam ma ya rikice haka a saki radio sa sautin karatun alk'urani me girma, sukuwa adu'a kowa keyi yana faman tofa musu ana nan har suka soma tari a tare jini ya soma fita daga bakinsu susu ukun...Lawuri kam k'ofar waje ta nausa da gudu tana ihu lallai k'uru mugune me suk masa? Haka nan tana ganin jinin ta tabbatar sunma mutu shine abu na k'arahe dazatayi arayuwarta indai ya kashesu seta koma gida ta kashe har ubanta har bokan!
*Nazata munbar labarin doguwar hanya tuni, ashe k'afafuwan mu da gangar jiki kurin ta baro hanyar amma ruhin mu yana cen har yauu be baro doguwar hanya ba!!! Ko zasu kub'uta?****
*wannan book nawa na kud'ine me buk'atar siya seya biya 200 kacal a sakashi a group..nemi wannan lambar 07084161619*
Mom Nu'aiym.
[11/21, 8:21 AM] Maamah twins💕â¤: 36**** lokaci d'aya jikinsu ya soma tashi daga farin da yae zuwa kore shar!!! Hankalin malam ya tashi ga malam babba ya d'aga, dad ma haka ya kira mahaifin zuhrah take yazo shima ya taradda wannan mummunan tashin hankalin,mahaifin Ayusher shine yazo da wani malamin na daban inda yasoma nashi adu'o'in acikin ruwa yana tofawa haka ya dinga watsa ruwan ajikin su na tsawon lokaci, a hankali abubuwa suka soma sauyawa zuwa samuwar lafiya daga barin aman jinin da kuma sauyawar fatar jikinsu zuwa asalin fatar su ta halitta, basu gusheba daga yi musu adu'a dakuma karanto ayoyi daga alk'ur'ani me girma har sanda suka fahimci nutsuwa ta saukarwa dukkansu!! Har suka soma bacci cikeda nutsuwa.
Ihu boka keyi yana guje guje daka ganshi kaga hauka sabon kamu tuburan!!! Gabaki d'aya gidan sa seda ya qone da duk wani abu daya shafi tsafinsa da mugun bokancin sa, haka ya dawo tsirara ya ruga da gudu se waje, haka mutanenngarim suka d'auka cewan boka ya haukace gidansa ya qone k'urmus ana haka k'uru yazo ana rirrik'e da Bokan, ya shiga tashin hankali shi kanshi sabida jin me ya faru, acewar en garin duk sanda wani abu ya samu boka toko tabbas masiface zata afka musu dukkansu, haka suna kallo jikin bokan ya soma ci da wuta dole suka sakeshi ya dinga gudu yana ci da wuta har inda ya dena motasi ya mutu a sandare!! K'uru se kuka yake ga 'yan gari hankalin su duka a tashe yake.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.