Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 29 of 52

"Dama akan abinda kakeyi da yarinyar cenne, kaga ka zire mata da yawa fa pure heart, bama wannan ba kaifa ka hanani hugging naka, shaking hand dakai amma yanzu se inga kana rik'ewa yarinyar cen hannu, kana matse wurin zama da ita anya hakan daidai kuwa?" Wani yamutsatsen kallo yabita dashi cikin hargitsi

"Me kenan kike nufi da wannan maganar? Zargi na kike da yarinyar kome?

"Wannan wace irin magana ce Yaa Sufyan? Ni yaushe nace wani zargi anan? Kurun ina gaya maka gaskia ne, mom ma tayi magana akan zaman yarinyar agidan nan, tunda an sallameta daga asibiti ka kaita gidanku kurin" cikin takaici ya kalleta

"Sabida na nemi alfarma agunki shine zaki zomun da hauka? Mesa zakimun haka ne wai? Ni yanzu kin rainani idan da inason ta zauna gidan mu daban kawo ta nan ba ai sabida kanki ne cewar munada muhallin ajiyetan" Yanzu kam itama ta fusata

"Sabida ina bautawa sonka seka mayar dani baiwarka? Sabida ina jarabtar sonka seka laftamun wata jarabawar, mayar dani wawiya kakeso kayi ko wacce batasan metake ba, idan hakane na dena damunka da zancnm soyayyata koda hakan ze zamo ajalina, ada roqonka nake kazo gidanmu amma sekayi wata kanamun yawo da hankali tunda kazo da wannan dangin mayun kake ziyartar gidannan wani zubin agunta kake wuni, an gayamaka banida zuciya ne? Daga rana me kamar ta yau na yafe duk wani abu daya dangance ka koya shafeka aiba kai kad'ai bane autan maza amma ka kwashemun dangin maguzawan cen daga nan gidan kaje dasu koma inane" yaukam mamaki Ayusher ke bashi iya mamaki, har wanda be tab'a tsammani ba, kwantar da murya yae

"Karkimun haka mana Ayusher, ki tallafeni ki k'aramun lokaci wlhy dik abubuwan da kika lissafa bawai haka bane ba, tausayi kurin suke bani" k'ura masa ido tayi

"Zan barsu su zauna, zan kuma yiwa mom magana akansu amma daga rana irin tayau karkai tunanin zan kula maka dasu, ka neki me aiki zasu koma b'angaren ma'aikata, karkuma ka k'ara zuwa inda take ka nemeni, ni bana mason ziyarar nabar mata" rarrashin duniya yayi amma haka ta kafe akan idan be yarda da hakan ba ya kwashe su agidan, badan yasoba yace ze duba me kulawa dasu d'in.

*********
Seda suka zo k'auyen fulanin dazasu hau ruwa sannan sukai shiri suka ajiye motocinsu suka kama hanyar wacen garin fulanin na biyu, basu kwana ba suka kara tsalaka ruwa suka shige d'ayan garin inda aka musu karamci, sosai sukayiwa dattijon hakimin k'auyen bayanin dalilin dawowar su, jinjina kansa yae cikin jimami

"Bana tunanin yaran nan sun dawo ta wannan hanyar gaskiya, kuma kunce basusan waccen hanyar ba, akwai gari idan an tsallaka ruwa anan yamma damu da suke cin naman mutane, abinda ya hanawa garin yawa ma kenan, sabida naman junan su ma ci sukeyi, yazamana aka shard'anta atsakanin su duk gidan dasukayi magana da juna so biyar arana agidan za'a d'auki mutum a yanka, idan baku manta ba na sanar daku kuma arziqi kukayi sabida zamansu matsafa, zakaga ko kallonka ma ba wanda zeyi a k'auyen ya kamata suma ku kula dasu sosai, rayuwarku da lafiyar ku itace tafi komai muhimmanci agareku, zancen musulunci dakukeso ku yad'a bazan hanaku zuwa isar da sak'on Allah ba, amma idan ba haka ba ku hak'ura wad'an nan matan dai basu dawo ta wannan hanyar ba sam" Abu sufyan ne ya tare da cewar

"Babu damuwa Ranka ya dade, dukda hakan zamuje mu duba su, hankalina baze kwantaba sena tabbatar basuje d'inba, kuma na isar da sakon Allah" jinjina kai dattijon yae

"Bari na baku aron mutane dasuka san kan jejin sabida tsaro" haka ya had'asu da fulani su hud'u suka shirya tsaf bayan sun basu ajiyar muhimman kayansu ciki jarda wyoyin salula suka lula doguwar hanyar....

*********
Cyama yauma kamar kullum se rarrashin mom take amma abun yanaso yafi k'arfin ta, general ya sanar mata inda Abu Hurairah yaje se kuka take akan ya cutar da ita, yaya zebar yaronta yaje wannan mugun wurin akan wad'an cen yaran

"Cyama tun shigowar yaran nan arayuwata nake ganin jarabawa iri iri, wlhy halinsu ya isheni, nagaji da mugun abun dake bibiyata, daddynku kamar bashi ya haifi yaran nan ba, duk wata musiba ita yake jansu ya kaisu aciki, shi mesa bejeba in hakane?" Rufe mata baki Cya tae

"Hana mom, mesa kike hakane wai? Ya dace kisan me kike fad'a gaskia, dad daya dage wurin ganin ya inganta rayuwar mu da taki ma, shine kuma yanzu kike zancen yayi kaza yayi kaza, sam be dace ace hakan daga bakinki yake fitowa ba gaskia, ki masa adu'a Allah yasa ya ganta kuma su dawo lafiya" wani hargitsatsen kallo mom tayiwa Cyama

"Su dawo dawa? Idan ma mafarki kuke kedasu toku farka indai ina numfashi a doron duniyar nan wlhy kinmaji na rantse d'aya daga cikin yaran nan baze aure wannan shaid'aniyar 'yar maguzawar ba, koda bazasu auri matan dake sonsuba toko tabbas wannan shegiyar ma bazasu aureta ba" kame baki siyama tae sabida sanin halin mom tasani indai ta kafe akan abu ta kafe kenan, haka dai ta ringa rarfashi harta sakko.

**********
Daren da yae musu ne a hanya ya basu damar kafa tent irin na soja suka kwanta aciki, Abu Huraira seya rasa meyake yawan fad'ar masa da gaban sa a wannan lokacin, da k'yar da sid'in goshi bacci b'arwo ya sace sa badan yaso bama, baccin sam bawai yana masa dad'i bane wannan ya sanya gari yana soma haske alamun sanyin asuba ya farka, shiya soma fita fitsari domin yasamu damar yae alwala yae sallah ya tashi sauran musulman dam tafiyar akwai arnan soji acikinta susu biyu, seda ya lula duniyar wasu itatuwa sannan ya tsaya ya soma fitsarin, kaman daga sama yaji an k'wala mar abu akai seda yae wata uwar k'ara daga nan ya some besan me ake ciki ba, Oga sufyan dayaji ihu ya duba tent baya nan seya fargar da sauran suka lula jejin nemansa.

*************
Abu Sufyan tunda yabar gidan su Ayusher se wani zazzafan zazzab'i ya rufe shi, tunanin sa ya tsaya cak akan yanzu idan kuma garin wannan tafiyar Abu Huraira ya rasa rayuwar sa fa? Yace masa me? Mesa sanda sukai waya be sanar masa Lawuri tana nan ba yasan inda take? Tunanin d'an uwan sa sosai ya addabesa harya saukar masa da zazzab'i shi yasan yana son Lawuri amma ganin yanayin d'an uwansa kurin ya isa ya nuna maka cewan beko kama k'afarsa ba a soyayyar ta Lawuri, amma bayaji ze iya bar masa ita kam, sedai yanaso ya ganshi tare da d'an uwan sa, duk sanda ya tuna yanayin tsoro daya shiga a wancen lokacin dakuma wahalr dayasha se taimakonsa da Abu Huraira keyi seyaji zuciyar sa tana masa zafi akan abinda ya masa, ya tabbatar da Huraira yasan yana son Lawuri baze ma nuna masa yana santa ba sedai ya mutu dan nashi farin cikin kawai, abubuwa sun taru sunwa Sufyan yawa duk inda hankalin sa yake atashe yake...

**********
Yanayin mutanen dake kan Abu Hurairah abun ya tsoratar dashi, duk jikinsu fenti ne, ja da fari, idanuwansu ma abun tsoro ne ja jajir anja musu layin bak'i a k'asansu, gasu suma k'arti bak'i k'irin dasu, yama rasa shi tunanin me zeyi, an tub'e masa kayan jikinsa gashi tsirara, besan wannan wace kalar al'umma bace kuma? Shidai yaga rayuwa se wasu surutai suke da sam baya gane komai akansu, hankalinsu yakai k'ololuwa gun tashi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.