Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 25 of 52

Lawuri tafi Barbo shan azaban dan ita batako san wake kanta ba, Barbo kuwa ta k'arye a k'afa, ita Lawuri ba'a san iyakan ciwukan datajiba har yanzu, matashiyar budurwar data kad'esu se kuka take tana mamakin sanda sukazo gabanta batai auneba, kamar aljanu? Gidansu ta kira waya lokaci d'aya asibitin ta cika fam da mutanen gidansu.

***********
   Hanifer ta kula yaran basa d'akin su da dare amma tana mamakin ina sukaje? Taso ta ankarar da mutan gidan amma setayi tunanin suna garden, tunda k'auyawane ko tsakiyar dare saje garden ai, wannan ya sanya tana kammala ayyukanta tae shirin kwanciya, tana sakaran ta koma gidansu ma nanda 2days.......Cyama ma tayi mamakin rashin ganinsu amma hakan be sanya ta wani damuba dan itama tunani d'aya tae suna garden suna hira cox haka sukeyi dukda basu saba kai dare ba, da wannan ta watsar da tunaninsu tae shirin kwanciya abunta kamar yadda Hanny tae.

***********
   Duk mutan gidan sun hallara dining kasancewar General ya dawo, k'a'idane idan yana gari ko bakaso se dole ka fito cin abincin safe a dining dake babban parlor na gidan, sun shirya sosai abinci kala kala, ita kamma mom bata ko damu da rashin suba tama manta dasu, seda aka nutsu ana cin abincin kowa yayi tsit sannan General ya kalli Adama

"Ina bak'in gidan ne ko kunya suke?" D'ago idanta tae ta kalleshi had'e da tab'e baki

"Oho, ni yau duk ban gansu ba" Cyama ce tace

"Dad jiya da dare ma basu zo d'aki da wuri ba, nazata ko suna garden sabida cenne gun zamansu shisa banyi magana ba har bacci ya kwasheni, yanzu mun wayi gari basa d'akin na tambayi hanifer ma tace bata gansu ba" Duka ya kaiwa table d'in da k'arfi

"What?!!!! Kuna haukane shine bazaku sanar da wuri ba? Bama wannan ba da ban tambaya da bazaku sanar ba kenan" tsoro ya kama su Hanny tace

"Dad na gayawa mom tinda na idar da sallan asuba, setace badai inda zasu waiko a garden suka kwana tunda sun saba kwanan jeji" Wani kallo ya wurgawa adama daya sanya ta sadda kanta k'asa ba shiri sannan ya kalli twins

"Kai Huraira jeka ka duba mun lungu da sak'o na gidan ina yaran mutane suka shiga" A tare suka mik'e da sufyan dukkaninsu cikin tashin hankali mara misaltuwa, neman duniya sunyi agidan basu gansu ba, sedaga baya suka tambayi securities na gidan anan sukejin wai tun jiya da kusan isha suka fita babu kuma wanda yaga dawowar su gidan, hankalinsu ya tashi suka koma ciki suka sanar, mom dai ko gezau su hanny ma ganin dad a wani yanayin duk se ya rikitar dasu suka shiga taitayin su

"Mesa nida gidana bazan kawo ajiyar abinda nake so a kular dashi ba? Shisa Captain yace zeje dasu gun matarsa bayarbiya na hana, yanzu a matsayin ki na uwa me kenan kikai? Kin burge kenan? Kin cinye kike gani? Yaran mutane dasuka fice dalilin masifar wlhy tlahi na baki awa ashirin da hud'u duk inda sukaje ki nemosu inba hakaba kinsan sauran" Mik'ewa tae cikin b'acin rai

"Haba Muhammad, se yaushe zan girma ne a wurinka wai? Nina koresu? Koni nace su bar gidan? Banko san sun tafi tayaya zan nemosu? Idan har kace akan yaran nan zaka mun haka wlhy sena bar maka gidan, kaida ka kawosu sekaje cen ka nemesu danni babu ruwana" Kallonta yae cikin b'acin rai

"Yanzu dama kafin na fita nakeso na duba CCTV nawa, an sanar mun har dukanta kikae a dining, suma securities sesunsha wuya a hannuna, yanda zasu bari su fita ba tare da sanin kowa ba, dan sunga shamsu baya nan" Juyawa tae rai a b'ace ta haura sama tana mejin zafin abinda ya mata agaban yara.

***********
   Lawuri unconcious take har washe garin, anma rasa gane meke damunta, dole yanzu ct scan za'a mata tunda yake ta samu rauni aka.... Yarinyar data kad'esu duk a rikice take tarasa nutsuwarta dukda kasancewar ta likita hakan be hanata shiga tsananin rud'u ba, musamman ganin wannan kamar zata mutu ma.

    Neman duniya anyiwa su Lawuri ba labarin su, Abu sufyan daren ranar bekoyi baccin kirki ba, yayinda Abu Huraira ya gagarayin baccin ma kwata kwata, hankalinsa ya tashi sabida yasani tabbas hanyar gidansu zata nema kuma bawai tasan hanyar bane ba, sedai ya kula tanada basira tabbas inda suka biyo tanan zata nemi komawa, sedai ta yaya? Tunda yake jirgi suka hau daga babban garin dasuka sauka zuwa nan garin Abuja, yashiga rud'ani sosai ya rasa tudun dafawa hankalinsa in yayi dubu to tabbas a tashe yake kuwa.

************
   
Banida zab'in daya fi in koma garin su Lawuri, banida zab'in dayafi inje garin nasu in binciketa inji kota gane hanya tazo, ai taji ana anbatar sunan garin dasuka hau jirgi sukazo wato OGUN state in hakane mota zata hau, taje cen sekuma ta nemi hawa wannan motar dasuka hau suka tafi wannan k'auyen na fulani, duk yanda akayi gida zataje amma bari ya bada sati d'aya idan ba'a samu labarin suba dole yaje garin koyaya ne kuwa!!!.

*****Bayan sati d'aya*

Har akayi sati d'aya babu neman dabasu musuba amma shiru kakeji, bame hotonsu bare su saka a media, general yayi bk'in cikin wannan abun, yanaso yarinyar ta karb'i musulunci yana so ya nuna mata cikar musulunci abun arziqi amma anzo an tilastata guduwa tabar gida sabida wani ra'ayin banza, damuwar sa d'aya ma besan hannun dazasu fad'a ba, nagari ko mugu?, yama rasa tudun dafawa!

*********
Hankalin Twins baya jikinsu, Abu Hurairah be fahimci tsananin so da illar dason ya masa ba se yanzu, hankalinsa ya matuk'ar tashi ainun, har 'yar rama, wannan wace irin masifa ce wai? Yana cikin dubun tashin hankali akan wannan abun, sabida ya shirya sosai akan yanda ze shawo kan iyayensa ya musuluntar da ita ya aureta, amma shine za'a wani ce ta gudu? Lallai wajibine ya koma wannan *Doguwar hanyar* yasan abunyi akan Lawuri idan ma batacen duk inda tashiga aduniya seya nemota yaga cewar sun sake had'uwa itace farin cikin sa, itace komai na rayuwar sa yakeji dai........

A b'angaren Abu sufyan kuwa shisam bama shida lafiya, wani ciwo ne ya sameshi me wuyar magani, ya tabbatar rashin ganin Lawuri a rayuwarsa abu ne me shirin kasheshi har abada ba shiri, mesa yarinyar nan ta masa katutu a zuci ne wai? Meke damunsa game da ita? Ne kodai haukacewa yake shirin yine be shirya hakan ba? Duk iyakar tunaninsa ya rasa abinyi.

Dawood yaji zafin wannan abin sosai
Sedai shi bekaisu damuwa ba kasancewar ba wani d'ad'ashi da k'asa tayi ba, shidai kawai yana mata kwad'ayin musulunci ne, bayaga haka kuma yaso ya aureta ya sanyata a rigar musuluncin gaba daya, abu mafi damunsa shine besan hannun dazasu fad'a ba, sun shigo garine kurin batare dasun san waye mutanen birnin ba? Yana musu fatan alheri.

*********
Duk wani shiri daya kamata huraira yae yayi abunshi na zuwa garin su Lawuri, babu wanda ya gayawa, se Sufyan daya kula tamkar da abinda yake b'oye masa yamasa shiru ne kurin yaga iya gudun ruwan sa.

Ranar da ya fita aiki kuwa bekoma waiwayen gida ba ya Lula *Doguwar Hanya* wacce besan wane tanadi tae masa ba yanzu..........

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.