Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 13 of 52

"Ur over reacting bro, calm down mana menene yasa zakace kaine zakayi, open all wahalan daka sha akaina, tun yaushe kake tafiya dani a bayanka? Gaskia tunda naji sauk'i nine zan d'auketa" Sauke ajiyar zuciya hurairah yae

"Kaida Bakada lafiya yaya kuma zaka k'arawa kanka ciwo, dubi kanka fa har yanxu da sauran k'umburi ga k'afarka ma haka" Dawood ta kalla cikin damuwa sosai tace

"Kamar fad'a suke ko?" Girgiza kanshi yae yace

"Abu sufyan ne ya kafe akan ze d'aukeki kinga kuma bashi da lapiya, shine, Abu Huraira yace dakanshi ze d'auke ki amma fad'a suke ba zancen kenan" murmushi tae tace dashi

"Dan wannan aibama sesun wahala ba, zan iya tafiya ai sekace maciji?" Jinjina kanshi yae

"Da gaske zaki iya?" Ya tambayeta

"Allah zan iya, Barbo tayani in kik'e kawai, haka suka shige gaba ita da Barbo, tafiyar shiru kakeji wannan karon har duhu ya sauka basui magana ba, seda taradda fili sannan suka samu zaunawa sukai sallah, sukaci tufa da mango sedai ba ruwa, Haska fitila Abu Huraira yae yana nazarin wurin, tabbas Filine amma bame zaunuwa ba har a wani kwanta, ramukan dake wurin filin sunyi yawa ko ina ramuka ne gasunan burjik, kamar na macizai dan haka ya jagoranci tafiyar dauke da Adu'a a bakunan su suka k'ara nausawa cikin hanyar sunkai 11:pm na dare suna tafiya kansu tadda ruwa, badan huraira yasoba sukai masauki agun, ga dare gashi basusan me ruwan ya k'un sa ba.

**********
Haka tafiyar su General ta yiyu acikin kwana d'aya suka isa k'auyen, inda jiragen masu saukar angulu suka rigasu zuwa jejin suna me zagayar gun sun tabbatar bayan an tsallake ruwan akwai garuruwa kusan bakwai dasu kaga mutane suna rayuwa aciki, amma basu san wanne ne ba, da wannan suka koma akan idan ma me sh8ga jejin bazeje ba zasuwa jejin saukar aradu zasu fara da garin dake manne da ruwan dazaran an tsallaka, wannan ya sanya suka shirya helicopter har 4 suka nausa da manya manya bindigoginsu a garin.

Tunda suka sauka a garin suke shan mamakin yanda mutanen garin suke kallon su, wasu mamaki qarara a fuskar su wasu se rugawa suke sa gudu jin k'arar jirgin, haka sun kula yaren nasu yasha banban danasu, takawa sukai har cikin garin da k'yar wani ya tsaya yin magana dasu, sun fahimci yare yake kamar yarbanci sedai ba duka bame yarbancin da wannan ya jagorance su zuwa gun sarki bayan ya sanar dasu sarki yau kwana uku beda lapia sabida b'atan 'yarsa, wanini me suna geoge da wani kanu suke magana dasu dan sune yarbawa. Sun sanar dasu akan tabbas sunzo amma sun sace 'yar sarkin sun gudu

Kafin kace meye wannan sun nemi kawowa sojojin hari basusa meye bundiga ba, seji sukai an soma mayar da martani jini yana zuba gasu su qananun wuqaqenw dasu dana katako wanda ake feqewa, aikam lokaci s'aya k'auyen ya rikice aka hau gudu ana ihun cewar dama ance garin ya kusa mutuwa.

Sojojin basu b'ata lokacin suba suka juya gun general suna so su gaya mai cewar ga abinda sukaji daga garesu.

************
Washe gari da asuba sega wani me tuk'in jirgi koma ince jiragen ruwa sunkai 10 wasu sun kawo passengers wasu kuma empty sukazo, abin mamaki fulatanci suke wannan abun ya burge su Hurairah dan kuwa yarem momy kenan sunaji sosai,mutanen suka sanar dasu akwai rugar fulani a gaban kad'an kuma sannan akwai 'ya'yan itatuwa dasuke zuwa d'eba anan suna kaiwa cikin gari siyarwa, itatuwa a zube suke a jejin na Allah, haka suka shiga jirgi d'aya dama sunada kud'i a aljihunsu sedai bame yawa ba amma ba laifi suka biya ya gangara dasu bakin ruwan bekoda wani tsayi sosai, shisa mutane sukai yawa ba jimawa suka taradda rugar fulani ga shanaye nan burjik babu iyaka ga gonaki nan malale k'auye me yalwar ni'ima, anan akai musu iso gun me garin bayan sunmai bayanin abinda ya samesu yace a baiwa matan suturu yana mamakin dama anan kusa dasu akwai garin maguzawa har haka, acikin Nigeria nan ya dace aje musu da addinin islama dai kam...dattijo me karamci d'aki aka basu bukka d'aya sedai far sunada nisa da cikin gari, matsalar ma jiya mota ta tashi yanzu se bayan sati biyu zata dawo dama haka takeyi, bama wannan ba akwai garuruwa uku dazasuje dole kfin Allah yasa sukaiga inda motar take, wannan labarin be musu dad'i ba sam idan akwai abinda suke buk'ata shine su isa gida kafin wayewar garin gobe, amma koda wannan rufin asirin Allah ya barsu sun gode masa.

Lokacin da dare ya tsala sun shiga takura sosai, sabida da farko dai da k'yar suka samu suka iya shan zallan Nonon da aka basu susha sabida k'arnin nonon, sannan kuma bukkar kyasone kurun aciki gata qarama gasu susu biyar ne, Cikin tausayi ganin su Lawuri a takure Abu sufyan yace da Abu Huraira

"Mu kwanta a waje mana, inyaso da safe semu shiga ciki, yaya zasu samu nutsuwar bacci a tare damu?" Kallon shi Huraira yae

"Bakan tunani ne me kyau, mu basu wuri, haka suka fita ranar kuma aka sheqa ruwan sama, sunsha wuya, badan sun soba suka kwana a bukkar tare dasu, da Asuba bayan sunyi sallah Abu Hurairah ya kalli Dawood yace

"Naga kamar ana kamun kifi a bakin rafin cen, mezai hana muje mugani ni zaman tunanin duniyar nan ma ya ishen wlhy" kallon mamaki ya masa yace

"Kaida nasan bakasan k'arnin kifi kuma?" Mezaisa kaje wurin?"

"Nidai zanje, idan bazaka ba se naje ni"

"Bro Nima zanje zan bika" Atare suka mik'e Dawood na mitan kafiya irin na Hurairah, ya sani k'arnin kifi har amai yake sakashi amma ya kafe akan seyaje aise yayi tunda yaji yakuma gani...

**********
Mommy kam jiki yayi nisa, sam batada lapia ko kad'an, duk yanda taso tacire abun aranta lamarin yafi k'arfin tunaninta, Cyama da Hanifer sune suke jinyarta dan har ankwantar da ita ma, ita Cyama babu abinda yake damunta irin rashin lafiyan mamanta, batasan meya samu 'yan uwantaba gakuma momy a kwance, hanifer ma haka, Abu huraira take so kamar ranta ze fita, tunda ta nemeshibta rasa kuwa bata cikin nutsuwarta da kwanciyar hankalinta, haryau tana tuna yanda sukai sallama bayan daya bata aran motar sa, lumshe idanta tae kurun cikin tsananin damuwa.

***********
General yayi shiru yana nazarin jejin, tabbas yaranshi suna shirin tashin hankali mara misaltuwa, da wannan ya yanke shawarar ashiga jejin gadan gadan dankuwa shi kad'aine solution agaresu, da wannan sukawa wani fili saukar angulu suka soma tafiya da k'afa agaban jejin domin nemansu.

Sunyi tafiya me nisa harta kwana biyu dayike su sojojine basu sha wahala ba kamar su, suna iya yin tent na wuccin gadi su zauna, a hankali harsuka isa garin nan da ake cin naman mutane, da wannan suka samu damar tambayar en garin kosun gansu, amma ga mamankisu kowa sukai qoqarin yiwa magana baya amsa musu, ko kallonsu ba'ayi, sunsha mamaki sosai na wannan rayuwar to kodai aljanaine wannan garin, General ne yae umarni akan tunkan dare yae musu sui gaba dn wannan garin tabbas ba lafiya acikin sa, haka suka yi nisa wa garin sosai sannan suka yada zango awani fili me yalwar yashi, hankalin general be kwanta da garin ba still dan haka sukace zasu koma cikin dare sui bincike yana ganin kamar ko yaranshi suna garin ne, da wannan sukai shiga irinta soja suka nausawa garin cikin sand'a.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.