Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 32 of 52
Abun kuma seya dami Hurairah, yaudai da kanshi yaje gunta amma ko kallonsa batayi ba harya zauna
"Musulunci dai ya hana gaba ko?" Batako kalle saba ya qara cewa
"Assalamu Alaikum" shareshi tae
"Amincin Allah ya tabbata agareki ya bint" waigowa tae suka kalli juna cikin takaici ta amsa
"Amin wa Alaikassalam"
"Nazone yau mui maganar mafita, yau da dare nakeso mu tsere amma ke me kika gani, naga ke kinsan hanyoyin da suke bi, naga kuma suna shan burkutu duk dare kuma ni sun dena d'aure ni yanzu" kallon sa yanzu kam tae sosai
"Idan kuma suka kama mufa? Kasan hukuncin wanda ya gudu da mace anan gun?" Kallonta yake shima ido cikin ya girgiza mata kai alamr aa, taci gaba
"Kashesa akeyi idan an kamashi, ni kuma bnso maka mutuwa yanzu ba" haka dai ya kafe akan se sun tafi dole ta amince masa, cikin dare kuwa suka had'e inda yace suka nemi sulalewa....
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐โค: *๐๐DOGUWAR HANYA....๐๐*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Book nawa na siyar wane, please karkui sharing wasu groups kuma karki karantamun idan baki biyaba,meso ya siya ya nemi wannan lambar 07084161619*
22
Tafiya me nisan gaske sukai dan kuwa basu suka sararawa tafiya ba se kusan asuba, seda sukai sallah sannan suka kalli juna, zuhrah tace
"Nagaji wlhi" cikin hasken dabe gama wadata gun ba ya furta
"Aikuma baki isaba Zuhra, yaya zakice
Kin gaji, karaya da wuri haka?" B'ata fuska tayi
"Ni gudun damukene ya ishen, bakaga ba har bayana ya soma mun ciwo" murmushin takaici yae
"Mutanen cen fa kinsan sunsan kan jejin, zama su fimun sanin shortcut daze iya had'asu damu batare da wani b'ata lokaci ba, bama wannan ba aiba su kad'ai bane mutanen wannan jejin macuta akwai dubun dubatar su miliyoyinsu ma suna nan, bamuda wani makami se adu'a idan zaki tashi muje ki tashi muje" mik'ewa tae cikin takaici da gasken ta gaji, istigfari yae Allah yaga zuciyar sa sannan ya damk'o hannunta suka soma gudu baji ba gani.
************
Abu sufyan kuwa duk wata damuwa damuke tsammanin yana cikinta tawuce hakan ma, sabida kwata kwata mom batada lafiya gashi bata kulashi akan ya bata kunya ya cutar da d'an uwansa, yauma kamar kullum durk'ushe yake agabanta yana xubar hawaye
"Mom dan Allah kiyi hak'uri ki tallafeni ki gafartamun, wlhy sharin shaid'anne" kawar da kanta tae daga dubanshi, tana fushi dashine kurun amma dukkanin laifin general ta d'audawa shi kacokam, sabida koba komai shine ya kafe akan yin tafiyar tun farko, dabe tura subin wannan doguwar hanyar ba dababu abinda ze rarraba kan yaranta har haka, seda ta share k'walla sannan tace
"Zan hak'ura amma da sharad'i" Da sauri yace
"Na amince mom, duk girman sharad'in dazaki gindayamun zan jura zan d'auka inshaa Allah namiki alqawarin komai girman sharad'in zanbi shi batare da wani tunani ba" Gyaran kwanciyar ta tae
"Ka tabbatar nanda kwana biyu yarinyar nan ka d'aurata akan wannan k'auyen na fulanin garin dakuka b'ulla bayan da kuka baro muguwar hanyar nan, akwai garada da OGA shamsu yae sun rakasu ka basu kud'i Maira dubu d'ari biyar su d'auki yarinyr nan da kuyangarta su kaisu garinsu, ka kuma manta da ita har abada wannan shine sharad'in nawa, sabida Abu Hurairah bamuda tabbacin qara sanyashi a idanmu har abada" Jikinsa har rawa yakeyi tsabar firgici yana cikin tsananin rud'u da tashin hankali, har ya mik'e ya qara durk'ushewa
"Mom Dan Allah ki duba lam......"
"Wlhy kaji na rantse ka sanya wannan yarinyar akan hanya tayi garinsu nanda gobe ma na dawo sa abun baya" Yama rasa meyake masa dad'i haka ya kasa ya tsare ta da ido cikin rud'ani bashida bakin magana haka yabar d'akin jikin sa babu k'wari ko kad'an.....
Kallonta yakeyi bayako k'iftawa harta tsargu da kallon dayake mata, cikin bak'in ciki da takaici yace
"Lawuri zan sanyakai a hanya ki koma gida badan raina yana buk'ata koson hakan ba sedan yin biyayya wa mahaifiyata nasani ba dole bane ki fahimci yarena amma ko ba yanzu ki sani kina raina har abada ina miki sonso bana wasa ba banida wani zab'in dai daya wuce in hak'ura in barki ki tafi" bata gane sosai ba amma ta fahimci maganar ya shafi shi da ita kuma maganar tafiya yake mata, kuka ta saka dan batasan mekenan yake nufi ba, ya hau aikin rarrashi, washe gari tunda safe yazo gidan kai tsaye Ayusher ya nema ba musu tazo suka gaisa yace
"Zanyi tafiyane, zanje OGUN STATE" kallon mamaki tae masa ganin sam baya walwala
"Wurin me kuma Yaa Sufyan?" Ta tambayeshi cikin kulawa
"Lawuri zan sanya a hanyar garinsu, kuma daga OGUN STATE D'in ake dauke hanya zuwa garin, ga tafiyar da nisan gaske ina barar adu'ar ki" Sadda kanta tae a qasa cikin tausayin sa
"Mesa zaka mayar da ita?" Kawar da kanshi yae daga dubanta
"Hakan shine daidai dear, so karki damu fatana kimun adu'a kinsan yanda hanyar nan take" jinjina kanta tae
"Allah ya tsare hanya ya kaika lfiya yakuma dawo dakai lafiya" godiya yae mata sannan ya shiga se mamaki Lawuri keyi ya gama tattare musu kayansu yace su fito, haka suka kama hanya bata fahimtar komai sabida batare kai, se Barbi ce me gane inda aka dosa....
**********
Tunda mutanen songai suka gano guduwa sukai se suka shiga nemansu, koda suka fahimci hanyar dasukabi bame b'ullewa bace sesuka dawo suna
Dariya sun tabbatar bazasu yau ba sesun juyo dan kuwa akwai makasansu a hanyar bila'adadin, idan ma sun samu sun dawo kenan kafin a kashesu acen ba.
Kallon tausayi ya sake mata sanda suka iso hanyar data rabu kashi uku abun mamaki acikin jejin nan
"Zuhrah menene?" Duqar da kanta tae
"Yunwa nakeji" Ta bashi amsa a tak'aice, shida kanshi daurewa yake amma yunwa yakeji
"Kiyi hak'uri Allah baze barmu haka ba, indai har munada rabon sake ci da shan wani abu agaba zakiga mun samu, babbar damuwa ta shine hanyar nan, bansan wacce mafi alheri agaremu ba, sabida haka zan d'auki duwatsu k'waya uku, zan sanya qanana biyu da babba d'aya zan yi adu'ar neman zab'in Allah sena jefa a tare, duk inda babban yatafi anan zamubi" Kallon satek cikeda gamsuwa da bayanin sa, runtse idansa yae ya soma kwarara adu'a yakai tsawon 30mns yanayi sannan ya jefa duwatsun, hanyar data kalli hannun damansu ta gabas anan dutsen babba yabi sauran kuma suka watse, kallon ta yae
"Ki shiga da Bismillah nima haka da ita zan shiga" haka suka shige sunata adu'a, yanzu bako waya bare ya saka karatun Alk'urani sedai yanata rerosa abakinsa har mamaki yake baiwa Zuhrah yanda sam baya kuskure sekace akanshi yake kaf, haka yae yae shiru sabida k'ishiruwa danma lokacin sanyi ake sosai dase sunsha azaba.
Sunyi tafiyar wuni d'aya cur har dare ya taradda su, anan suka nemi mafaka taimama sukayi suka sallaci magrib harma da isha sannan sannan suka k'arayi gaba acewar hurairah inda suka tsaya d'in shi sam be masa ba.
Ta gaji iyakar gajiya shi d'inma a wahalrce yake, haka har asuba tae musu, wayewar garin ne ya basu matuk'ar mamaki ganin su a inda basu zata ba, akwai yalwar Bishiyoyi sosai tare da manya manyan 'ya'yan itatuwa tamkar wani ne ya shhukasu a gun, wurin sekace wata fad'ama, dan komai na lambu akwai, zuciyar Abu Hurairai sam bata kwanta ba, dan haka duk irin kukan da Zuhra take masa hakan be saka ya barta taci komai agunba, haka yana ta adu'a yajata suka bar wurin tate da d'aukar hanyar gabas domin neman mab'oya.....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.