Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 35 of 52

**********
Bayan kwanaki hud'u ma sega wannan mutanen akan sunkai su Lawuri har gida sedai basu isa cikin garin ba suka juyo amma tabbas har hayewar garin sunyi dan har suna hango mutan smgarin suna sha'anin su da wannan dai suka dawo abunsu, godiya yae ya saka da abinda ya alqawarta ya juyo zuciyarsa babu dad'i ko kad'an.

Kafin kace meye wannan har an zagaye su kaf, ana zuba musu ihu akai da ababen makamai a hannu, da k'yar Zuhrah ta samu wani ya saurareta tamai bayani sosai akai abinda ya fito dasu daga wancen rundunar ta songai harta fulatancin dasuke ya sanya aka yarda da ita tayi bayani akan Hurairah sam baya jin fulatanci sabida shid'in mutumin k'abilar hausa zalla ne, ita kua mahaifiyrta en mutan fulanice kuma bata musu magana ta hausa, gun sarki aka kaisu ta qara koromai bayani, yace shisam be yarda dasu ba se idan zasu amince a d'aura musu auren dasukace shiya fito dasu, nan tamai bayanin cewa dama kosun d'aura babu auren nasu tunda maguzawa ne basusan Allah ba, su kuwa musulmai ne kuma basusan juna ba se agun, cikin harshen fulatanci ya furta

"Kinga yarinya dole fa semun d'aura muku auren nan zamu yarda daku, idan kuma ku masu lek'en asiri ne fa? Indai har hakane menene zesa ku gudu kuku biyu mace da namiji ba muharamman juna ba, so ake amana wayau, aini inada ilimi na, shekara nawa jama'ar songai suke hallaka mana en uwanmu da dukiyoyin mu? Basuda mafaka d'aya sedai su cutar damu su gudu, ko yanzu wlhy kasheku zamuyi annuyarku ta biyu" murya na rawa tace

"Kayi hakuri ka yarda damu sarki me adalci, yaya za'a samu fulani a jama'ar songai? Wlhy kamamu sukayi suka riqemu bamusan manufarsu tayin hakan ba" Kallon shek'ek'e ya mata

"Yarinya kasheku fa zanyi" Durk'ushewa tae agun

"Na yarda ka d'aura mana aure, na yarda zamu zauna harna tsawon lokacin daka ambata tare daku lokacin daya maka a matsayin miji da mata,idan har kaga wani abu a tattare damu na rashin gaskia ka kashe mu, amma yanzu kamun rai ka bamu wannan damar" seda yae magana da en fadawansa sannan yace zasu d'aura aurensu zakuma su basu wurin zama su zauna dasu na watanni biyu, idan songai da jama'ar sa suka kawo musu wata ziyarar to suma sesun kashe su har lahira, a garin su kuma baliga girmanta da baligi seda aure bazasu lamunta ya lalata musu yara mata ba, dan Haka dole sesun d'aura musu auren koyayane" Shiru tae tana kallon Al-hassan dankuwa tasani besan me ake cewa ba sam

"Ranka ya dad'e sadaki nafa" kallon kunkurunsu yae yace

"Kamar ba'a nigeria muke ba? Ai ga kud'inan a hannun ku?" Kallon Al-hassan take

"Muma ba damu bane ba kud'in" tsaki yaja

"Kuyita rik'ewa nine zan biya sadakin amma ko bakwaso yanzu zan had'a shaidu a d'aura muku aure" haka ta zauna ta baiwa Alhassan labari duk hankalinsa ya tashi babu yanda ya iya dole ya amince, sunaji suna gani tsohon nan ya biya sadakin su suka kuma d'aura musu aure!!!!.

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

******

"A tunninki zaki iya ne? Kina ganin hakan daidaine ya dace kenan wannan auren?" Kallon sa take cikin wani yanayi me matuk'ar wuyar fassara

"Kayi Hakuri kaji, bamuda zab'in daya wuce hakan, kuma ai dakai nayi maganar seda muka yanke shawarar atare idan ba dan ka bada bakin yin hakan ba babu kalar k'aud'in daze kaini in fad'a hakan kona zartar da hukunci kaina tsaye" Shiru yae

"Lawuri itace ta janyomun akanta na shiga wannan halin danake ciki, nazo neman wata dan in musuluntar da ita itada ahalinta amma na fahimci Allah be turo anan dansu ba, Allah ya turo ni anan ne danke dakuma wata k'addarar rayuwata, ban tab'a tunani akwai ranar da za'a d'aura aurena batare da iyayen da uwana ba, bansan me Allah yake nufi da hakan ba Amma ina matuk'ar godiya agaresa duk yanda yae dani, nasan hakk'in aure nasan hakk'ok'in ki dake kaina zan zamto me cikasa hakk'ok'in ki akaina gaba d'ayansu se wanda yafi k'arfina" Shiru dukkansu sukai koda ya duba Zuhrah kuka takeyi cikin murya mara sauti, besan meya sakata kuka ba, sedai tabbas ta bashi mugun tausayi,har yake gani ko kalaman same sukai mata zafi

"Babu abinda nake nufi da kalamaina se Alkhairi zuhrah, banyi magana ko d'aya danna ci miki zafari ba, kiyi hakuri nasani kema bakiwa kanki wannan burin ba, nasani kema had'uwata dake agareki k'addarece ta rayuwarki kiyi hak'uri kinji" Bata ce masa komai illa tashi datayi tabar masa d'akin da aka ware akace nanne mallakin su zuwa watan nin dazasuyi subar garin idan har ba'a kawo musu wani harin ba.......

Shiru yae yarinyar tana bashi matuk'ar tausayi, duk da bawai ya santa bane ba acen baya amma tabbas tana bashi matuk'ar tausayi, danya kula tasan hutu bata mik'e acikin wahala ba ko kad'an, yana tunanin rayuwa dakuma halin da Lawuri take ciki, shin kota koma gida? Kokuma itama wata k'addarar ta tsayar masa da ita akan hanya, yanzu kam ya gano kuskurensa na k'ara dawowa wannan hanyar mara b'ulllewa, be nemi zab'in Allah ba ya bazamo neman ta kaman dole shisa Allah ya jarabcesa da wannan matar.

***********
*Bayan sati hud'u*

Kallo d'aya zaka yiwa Abu Sufyan ka gano samsamsam baya cikin hayyacinsa, rashin Abu Hurairah yafi damunsa fiye da rashin Lawuri ayanzu, duk wani tashin hankali yana zaune daram a zuciyarsa da kansa, yana gani idan har yau akace d'an uwansa ya mutu ta wannan hanyar meze gayawa Allah? Son zuciya kome? Yanzu da wanne zeji ne wai?, haka yake wuni a damuwa mussaman idan yaga yanda Mom duk tayi wani iri ba ita ba ba dad ba yanzu rigima ta k'are banda adu'a babu abinda sukeyi yanzu, yakanfi shiga damuwa fiye da kullum

"Amma yanzu baka tunanin cewar mom hankalinta ze k'ara tashi idan taga cewar ka sh8ga wannan yanayin kaima? Duba fa kaga yanda ka dawo Yaa Suf, duk kayi wani fayau dakai ba kyaun gani, da wanne kenan zataji?" Kallon ta yae

"Cya yazan samu nutsuwa bayan atadalilin son zuciyata Twin ya b'ata, bamuda tabbacin yana raye ma koya mutu, irin wannan tashin hankalin yaa ze barni in rayu cikin walwala da farin ciki? Ki dubafa ki gani su dad sun hana inbi bayansa, acewar su bazasu salwantar da rayuka da dama irin haka ba, ina cikin tsananin damuwa CYa" tausayin sa sosai taji ya kamata

"Bakada laifi Yaa suf, sharrin shaid'an ne dakuma yanda Allah ya k'adarto zata faru, so just pray for him inshaa Allah ze bayyana" bece komai ba sam shi bashida nutsuwar hankalin sa ko kad'an.

**************
Tunda ta soma rawar d'arin yake kallonta cikeda tausayawa, besan meze mataba yanzu kam, an bata magungunansu na gargajiya amma jikin ko alama beyi nufin sauka ba, dukda a rufe take ruf da zani irin na fulani hakan be sanya ta dena rawar sanyin na, matsawa yae akusa da ita cikin tsananin damuwa ya yane bargon yakai hannunsa akan goshin ta yaji zafi rau, d'ago idanta tae cikin hasken na fitilar k'wai dake d'akin idan ya kad'a yae jajir ta kallesa

"Kaina yanamun ciwo sosai, kozaka kamamun dan Allah?" Gyaran zamansa yae ya kama mata kan nata had'e da mata wasu adu'oin

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.