Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 18 of 52
*************
Su Lawuri agun wanka ma ansha fama dasu dankuwa Hanifer har mamakin wannan gidadancin take, to suwaye ga basajin Hausa, se Sighn language (yaren kurame) suke amfani dashi, da k'yar ta tsaya sukai wanka ta basu dogwayen riguna na material nanma tasha fama seda ta saka musu kuma sesuka kasance a takure dan basu saba ba, abinda ma takula dashi shine basa jin dad'in kayan, abinci kuwa ansha fama dasu, shinkafa da miyane amma ko yanda zasuci basu sani ba, gaba d'aya kan Hanifer ya d'aure seda ta zauna ta ebo nata tanaci suna gani sannan suka ci, bazasuce basuji dad'i ba amma dai basu sababa kam, hakan datakula basu maci da yawa ba ya sanya ta kawo musu 'ya'yan itatuwa ba laifi sukam sunsha sosai, bayan nan kuma d'aki ta kaisu suka kwanta sabida rage gajiya, ita baiwar komai d'ari d'ari takeyin sa, danko gadon kasa kwanciya tae kusa da uwar gijiyar tata se a qasabta kwanta babu wanda ga mayar da tsawon 30mns acikinsu batare da yayi bacci ba.
********
Sufyan kuwa bayan nan Gidansu Ayusher ya wuce, a waya yae kiranta tafito tana tafiya cikeda yanga ta d'aukar hankali, sanye ajikinta farar doguwar jallabiya ce da mayafinta ja, agaban rigar ko ina an rubuta Ayusher da manyan haruffa da jajayen duwatsu, agogon hannunta ma fari ne qal, shima jikin fatar rad'am zaka hango an rubuta masa Ayusher da jajayen duwatsu takalmin k'afarta jane gaba d'aya, ta zuba asalin kyau dan har bayan rigar ta Ayusher ne zane da red stones, tana tafiya tana taunar cingom, se wani murmushibtake fesa masa yayinda ya kawar da kanshi gefe d'aya azuciyar sa yana jin haushin halayen Ayusher, bud'e mab'allin motar tae tashiga gefen me zaman banza ta zauna, k'amshin turarukansu suka daki hancin juna kowannen su seda ya lumshe idan sa, watsa masa kallo tae
"Yau da kanka a gidanmu pure heart?" Gajeran tsaki yaja cikin takaici
"Kewai when zakiyi hankali ne?, kinzo mun ba sallama kin shigo ba gaisuwa kin soma zuba surutu akaina" Sadda kanta tae, mantawa take dawa yake gabanta ta manta masifar shi
"Am so sorry , Assalamu Alaika kuma ina wuni?"
"Alaikissalam, sorry dama kud'in nan na kawo miki sauri nake da inda zani" cikin mamaki ta kallesa
"Wane kud'in kuma pure heart?" Murmushi yae
"Look Ayusher banzo nan mui wasa ba, kud'in dakika turamun nagode sosai, shine na dawo dashi" a yamutse ta kalleshi cikin hargitsi
"Haba Father sword mesa ni kome zan maka arayuwa bazan burgeka bane ba? Kud'in kaman banida shi zakace zaka dawomun dashi?" B'ata fuska ya k'arayi
"Nasan kinadashi shisa nace ki bani aro ai, Ayusher plss karki b'atan lokaci, nagode sosai da kulawa da kuma taimako, so ki karb'a kud'in nan" Jikinta yae sanyi inda sabo tasan halin Sufyan kozata mutu tunda beso karb'a ba baze karb'a ba, cikin takaici ta karb'a tace
"Thank u" murnushi ya sake mata
"Zan kiraki anjima idan na nutsu, karki kirani dan Allah da kaina zan kiraki" kallonsa tae yanxu kam har k'walla ya taru a idanta
"Amma sufyan kasan yanda mutane ke sona, kasan yawan samarin dake tururuwa akaina kaine kad'ai kake wulaqanta ni, yanzu meye laifi idan ni na kiraka fisabilillah" abinda yake had'ashi da ita kenan
"Kin iya jinjina yawan masoyanki, kinga Ayusher dan Allah jeki" Cikin fusata tabar cikin motar, tsaki yaja shikan yae gaba da motarsa zuwa gida.
*********
Abin duniya ya soma damun lawuri, tarasa inda zata tsoma ranta, baccin ma datayi da tulin mafarkai barkatai tayishi, dukda mahaifiyarta hankalinta ya koma gida, gida takeso taje taga me suke ciki amma batasan hanya ba, lallai seta koma gida bazata juri rashin mahaifiyarta ba, amma ko Wancen ze bita kuwa?.
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Littafina na kud'i ne idan baki biyaba kika karanta keda Allah, idan kinaso ki tuntubi wannan number 07084161619*
12
*Bayan kwanki biyar*
Har akai kwanaki biyar Lawuri bata cikin nutsuwar ta sam, komai baya mata dad'i ga yawan yin mafarkai da mahaifiyarta, mafarkin datayi yau yafi komai firgitata, sabida mafarki tae da mahaifiyarta an cinna mata wuta tana ihu tana neman taimakonta amma ita ta gagara zuwa ta tallafeta, ganin haka ya sanya ta soma tunanin lallai tabbas iyayenta basu samu wanda zasu bayar matsayin sadaukarwa ga abin bauta ba,kuma tabbas an kashe su. A bayan gidan take zaune ita da kuyangarta Barbo furanni da 'yan shuke shuke dake gun suna d'ebe mata kewa, Kuka takeyi na abubuwa kala kala, na farko tunda suka dawo bata k'ara sanya mutanen uku a idanta ba dukansu, tarasa to zamanme take ne, ga wannan yarinyar da wannan tsohuwar ma yaransu sukejiba ga rayuwar takura su a jejin dasuke ko rijiya babu a kogi suke ebo ruwa, a jeji suke kashi, amma wannan komai ya sauya komai basu iyaba hatta yanayin cimarsu daban da tasu, bakinta be saba ba sam! Kallonta barbo tae cikin kulawa tace
"Lawure shugaba ya dace mu koma gida fa, yanzu nasan K'uru da k'uruwa suna cikin damuwa kamar yanda kema kike ciki yanzu"
"Barbo wataqil ma an kashe su fa, idan fa basu samu sadaukarwa bafa sune za'a kashe, anya Barbo na kyauta kuwa" sadda kanta k'asa tayi
"Nasan Baki kyautaba amma ni inaga kaman zuciyanki kika bi, kuma akwai abinda kikeso agun mazan garin nan" D'agowa tae suka kalli juna
"Inaso insan halinda Iyayena suke ciki, amma banso na koma cen, so nake nasan menene ake ciki bansan ya zan ba" Barbo batace komai ba sega Abu Sufyan akansu, murmushi d'auke a fuskar sa ya kallesu
"Sanunku" shine abinda ya fad'a yana kallonsu, ganin yana murmushi ya sanya ta sakar masa murmushin itama, cikin ido ta kalleshi tana share k'wallan idanta, da hannu ya mata alamar tambaya akan menene yana b'ata fuskar sa akan menene yake sanyata kuka, nanma take ta fahimcesa dan haka da kanta ta masa alamar ba komai lokci d'aya k'walla yana kwaranya daga idanta, b'ata fuska yae yashiga nodding kansa alamar bayaso ta dena, bayan hannunta ta sanya ta share k'wallan daya silalo tana k'ok'arin sanya murmushi a fuskar nan, da hannu ya mata alama akan tabiyo bayanshi, haka suka rankaya har babban parlor gidan, zama yae ya nuna mata da hannu akan ta zauna, zama tae ya nunata da hannu sannan u
Yakai hannunsa a bakinsa alamar cin abinci yana tambayar ta ko taci abinci? Lokaci d'aya ta fahimci meyake nufi ta shiga gyad'an kanta alamar taci, jinjina kansa yae ya mayar da dubanshi akan TV yana jiran k'arasowar Dawood dakuma Abu huraira yau an sallamaeshi a asibiti mommy ce kawai basu sallama ba acewar su jinin keda sauqin hawa amma saukar se'a hankali, suna nan jigum jigum har sukaji sallamar su, zamanta a gidan na kwanaki biyar ta fahimci cewar idan Akayi wannan maganar shigowane za'ayi haka harta soma haddace yanda suke amsawa dan haka kafij yae aune harta furta
"Amin wa Alaikumussalam" da sauri dukkansu suka kalleta suna mamakin dukda kalmar tayi wani iri abakinta yanda ta iya furtashi, yaushe tazo harta iya ansa sallama hakan nan rad'au a bakinta, Mik'ewa tsaye tayi tana kallon Abu Hurairah tana zuba masa murmushi, kallonsu take shida Dawood har suka k'araso acikin tsakiyan palon, seda tayi jim kantace dasu "Sannunku" kamar yanda Abu sufyan yace dasu d'azu, sannan yanda taga Cyama da Hanifer suna gayarda Baba ladi kullum shine itama tace
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.