Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 40 of 52
*********
Kai tsaye asibitin ya nufa yaje ya tarar sun karb'i patient d'in nurse d'in se mita takeyi
"So nawa zan gaya muku bazamu karb'i patient ba kud'i ba, gata da hawan jini ga k'aton ciki agabanta da 4month, tarasa duk duniya wanda ze biya mata kud'i a duba lafiyan ta dana babyn ta, wanda suka kawota idan bazasu iyaba su koma da ita gaba d'aya" matsowa yae dan sojin sun gayamai patient da suka kawo ce akewa wannan izgilin ya kalli nurse d'in
"Meye bill nata duka abinda take buk'ata?" Kallon shi tayi amma bataga alamar wasa ba
"72500 duka kud'in ta ta gagara biya se sintiri take anan" hararata yae
"To zamu biya ki kula da ita cikin gaggawa" ya juya batare daya jira cewar taba, rashin zuhra yana neman hallakar dashi ma gaba d'aya zata bashi haushi akan wasu tsirarrun kudad'e.....Befi 1 hour dazama ba nurse din tadawo gunsa
"Sir likita yanason ganin wanda yazo da patient d'in d'azu" kallon ta yae kafin yaja gajeran tsaki ya mik'e
"Muje" haka suka rankaya har gun likitan, sun gaisa sannan ya zauna
"Dama kane mijin waccen yarinyar, a gaskia kun kusa kasheta yarinyara batada lafiya ga juna biyu amma baku kulaba, ita batacin komai na gina jiki ga yara biyu acikinta ga pcv d'inta yaje down sosai yanzu haka 24% yazatayi surviving da shi gabyara biyu ga hawan jini? What on earth were u doing daze sanya kabar iyalanka su shiga fitina har haka" kallon mamaki yama Dr. D'in amma kfin ya samu damar magana likitan yaci gaba
"Thank God yaran suna lafiya, sedai basuda wani nauyi sabida yunwa basuda kuzari sabida babu wadataccen jini ajikin uwar, yanzu zamu baku cross marching na jini kaje a gwada naka idan zeyi da gaggawa muke buk'atar sa idan bazeyiba ku siya kawai sabida bamuda lokaci wannan ze iya sakawa ta rasa rayuwarta har abada" Mik'ewa likitan yae bayan ya tura masa takardar gwajin ya shige ban d'akin dake cikin toilet d'in nashi, mik'ewa yae jikinsa a sanyaye yakira dad yake sanar masa
"Kaje a gwada jinin naka idan zeyi ka bayar" kan yae magana har Dad ya kaste kiran, yaya ze bayar da jininsa ga wacce beko santa ba? Ko ganinta be tab'a yiba haka yake yaja soja uku akaje gwajin a lab duk nasu baya yi senashi, haka aka eba se qunquni yake aka bashi gado domin ya huta na 1 hour koda yazo har an soma d'ura mata jinin, shiko kallon tama beyi ba yace zeje ya dawo da dare.
***********
"Maganar auren nawane bakyaso kuma Ayusher? Mena miki yanzu wai kika tsaneni haka?" Kallon sa tae tana murmushi
"Ba abinda kamun nikam kurun dai nabaka damane ka wofintar yanzu kuma kaga Raubil ma yazo yace ze gabatar da manyan sa ya kakeso nace masa? So tari abinda muke rainawa shine yake mana wahalar samu wataran, kayi hak'uri kawai kaje gun Lawuri ka koma doguwar hanyar dazata sadata da garinsu ka aurota tunda Abu Huraira be samu ba" sumar kanshi ya shafa
"Ayusher pure heart d'in ki nefa? Wani kallon banza ta masa
"Pure heart d'in kuwa to sai me?" Shiru yae maganar tafi k'arfin sa yace
"Zan koma sena kiraki a waya" murmushi ta k'arayi
"Base ka kiraba idan na nutsu zan kiraka da kaina" murmushi shima yae
"Ba damuwa nagode" daga haka ta juya shima yabar gidan zuciyar sa ba dad'i.
********
"Me kake tunani game dani ne wai Al-hassan?, tun jiyan dama baka koma ba? Haka mukai dakai? Bance ka bari ta farfad'o ka nemi iyayen taba, kasan dama ina cike dakai ne fam ko? Wlhy ka kiyayeni maza katashi kaje ka duba ta, zancen yarinyar cen kuma anduba duka dangi kaf bata cen sekasan nayi" godiya yae ya mik'e jikinsa a mace zuwa gunta.
Anyi nasarar fitowa daga jeji su Lawuri sedai en riga sun kafe akan bazasu rakasu wajen gari ba, da k'yar me gari danya sanya ya basu kud'in jirgin dazasu hau su tsallaka ruwan na garuruwa uku, gasu dai a inda zasu hau mota amma ko anini basuda shi, ta rik'e sunan Abuja rad'au sedai bazata iya kai kanta gidansu ba, abu d'aya ta sani kota halin yayane setaga Abu Hurairah, kwanansu hud'u suna kwana a tasha, har lokacin motar ma taba tashi se bayan sati biyu kuma, mutanen garin sun soma gajiyawa dasu suna yaren fulani suke jiba.
*********
Kai tsaye wurin gadon patient d'in yaje ya kalleta tana baccinta cikin nutsuwa, wutsiyar hannun ta ya kalla ya tuna last maganar su sanda suka kwana hotel data karb'i wani agogon fata daya siya dasuka isa garin tace tanaso, shine rad'au a hannunta, d'ayan hannunta na dama sanye da ruwa ana k'ara mata, murza idansa yae cikeda mamaki, lokaci d'aya maganganun likitan nan suka dawo masa, kenan dukkaninsu akan shi yakeyi, dama zuhra ce ke cikin wannan mawuyacin halin lallai ya aikata zunubi Allah ma baze barshi ba........ Zama yae a d'akin har kusan sa'a fiye da d'aya seda ta farfad'o sannan ya tashi da azama yae kanta
"Zuhra sannu ya jikin?" Kallon mamaki take binsa dashi, runtse idanta tae gagam cikin rashin fahimtar komai, kafin ta bud'e su ta zuba su akansa
"Al-hassan inane nan mafarki nake?" Girgiza masa kanta yae
"Bakida lafiya please save your strength basekinyi magana ba, basekinyi tunani me yawa ba Al-hassan ne" rufe idanta tae kurun tarasa tunanin me zatayi.
*********
*Bayan sati biyu*
Babu yanda iyayen ta basuyi ba amma ta kafe ita lallai idan ta haihu yaransa zata bashi su rabu, yama sauwaqe mata auren sa itakam inyaso yama haihuwa tayi iddah kenan, anyi anyi taqi, taji zafin abinda ya mata sosai taji zafin tozarcin daya janyo mata yaci amanar ta fiye da k'ima, ya tona mata asirinta dan haka ta kafe
"Ina ga zmu baku sati biyu nan gaba, ku sasata kanku, idan har kayi galaba akant ta hak'ura shi kenan amma idan har Zarah tace bazata koma ba a gaskia ni bazan tilasta mata aurenka ba, kaima shaidane akan abinda kayi sam sam baka kyautaba wlhy" shiru yae daganan aka basu wuri, mik'ewa tayi
"Idan da zakabi shawara Ko Al-hassan karka wani jira sati biyu suzo danko shekaru biyu suka zago nida aurenka har abada" kanma yace wani abin tayi ciki, gabaki d'aya duniyar juya masa take, shi yama rsa dalilin daya sanya yakejin sonta har cikin b'argon sa yanzu, ya tabbatar Allah ne ya jarabcesa da sonta dan ya wulak'anta aure.
**********
Su Lawuri dai se gasu asaman lodin yaji, sabida rashin kud'i yunwar cikinsu ma ta ishesu ga gardawan garin su sun koma dama haka akai dasu, bamusan yanda zata kaya ba idan suka isa OGUN state gamu gani dai.
Mom Nu'aim.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐โค: *๐๐DOGUWAR HANYA....๐๐*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*please idan kinsam baki siyaba bakida haqqin sharing ma family and frnds, idan ma kin siya ban yarda ki tura a groups ba indai ba k'awarki ba, idan kika tura a groups kina kashemun kasuwa ne, me buqatar siya 07084161619*
29
Lawuri tunda suka shigo garin OGUN STATE take rarraba ido, duk wanda suka gani zasu masabyare sama Allah ya taimakesu akwai yarbawa sosai a garin, idan tace Abuja take so suje se ace akwai nisa sesun hau mota, sunyi yawo harsun gaji, atasha ma cewa sukai a sakasu koda saman motar ne amma aka koresu akan basuda ko k'wandala.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.