Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 50 of 52

*********

Tunda suka shigo gidan hankalin Zuhrah ya tattara zuwaga gogan nata, tarasa dalilin tsorata da ciwon nasa da tae ga uban cikinta daya k'ara girma sosai daka ganta ko ba'a fad'aba kagan maman biyu, hidima take dukda ta kula da take take hanifer nason ta shiga tsakaninta da mijin ta,komai seta wani mak'ale yaya kaza yaya me kakeso, d'aki ta kai abinta ganin isha ta wuce har anci dinner, tunda wannan ta kanainaye ta kafesu a parlor

"Yaya mage shigewa zakayi tun yanzu bazaka bari muyi hira ba?" Kallonta sukai dukkansu Zuhrah cikin qufula tace

"Bakiga be gama warwarewa ba, ai gwara ya kwanta da wuri ko?"

"Anty zuhrah kwanansa nawa a kwance? Ai gwara ya zauna kar bayansa yazo yana masa ciwo"

"A d'akin aini nasan mezan masa daze sanya jikin nasa bazeyi ciwo ba, so karki damu" taja hannunsa shikuwa babu wani wadattacen k'arfi ajikinsa se binta yae sekace rak'unmi da akala....

Seda sukai wanka sannan suka kwanta lokacin tara ta gota ma, kwantar da kanta tae asaman k'irjinsa

"Yaa hurairah da gaske kuwa da Dr. Yace yana da kyau kake gayarda yaranka da mamansu, sunyi kewarka sosai muna maka fatan samun lafiya me d'orewa" Hannunsa yakai acikin duhun ya shafi fuskarta yana murmushi

"Allah ko Zuhrah?" Gyad'a kanta tae "Sosai mana yaa Hurairah" murmushiya k'arayi ya sumbaci goshinta kawai, ganin tana shafa bayansa ya sanya ya kamo lips nata ya ciza had'e da lak'uce mata hanci

"Haka ake renon zaki hanani bacci" shagwab'ewa tae gaba d'aya

"Haba mana yaa hurairah " bakinta ya cura a nasa ya soma kissing nata passionately, banda numfarfashinsu dake sauka sauri da sauri, ko wannensu ya fita hayyacinsa se shafar jikin juna suke tamkar zasu yaga jikin juna, seda suka gama birkicewa sannan hurairah ya tuna alk'awarinsa akan baze k'ara kusantarta zuwa cen ba, zame jikinsa yae ya juya mata baya dukda azabar dayakeji ajikinsa na tsananin buk'atarta, matsawa tae a kusa dashi ta rungumeshi ta baya

"Yaa Hurairah dan Allah kayi hakuri" daga cen be waigoba yace

"Me kikamun kike bani hak'uri ne Zuhrah?" Kuka ta saka masa

"Ka taimakeni ka kusance ni yaa Hurairah, wlhy ina buk'atarka, idan laifin danama abayane na tuba kaji bazan k'ara ba har abada" be juyoba be kuma ce mata komai ba haka tayita masa kuka kusan mintun 10, ganin baze iya hak'ura da wannan kukan ba ya sanya ya juyo mata suka k'ara afkawa juna ya kula tana cikin tsananin buk'atarsa beso ya cutar da ita har haka ba, seda akazo kashe boss sannan tutsun ciki yace besan wannan ba, murmushi yae

"Maman twins, ga alama bazasu barki ki mora ba yau, sunce mission impossible" Rufe fuskarta tae da tafukan hannayenta, bashida zab'in daya wuce ya sauya musu style na kwanciyar wanda da hakan aka kashe boss....

Hanifer wacce ta musu lab'el da kuka ta koma d'akinta, tajiyo suna kukan dad'i ita kuwa ta koma na bak'in ciki.

*Nibansan mesa har yau dawood ne kadai besan dawan garin ba lolx....*

Mom Nu'aiym.
[11/26, 6:19 AM] Maamah twins💕❤: 37****Tunda ya fara maganar shi take kallo harya kai k'arshen zancen sa, malam ne me isar da sak'on general akan zancen oga shamsu, yaso yae jihadin auren ta amma yanaga hak'ura zeyi yae jihadin da Barbo inhar zata amince masa akan wannan tafiyar, ba shakka Lawuri yanzu data soma sanin menene musulunci ta yarda da k'addararta kenan, bazata ma ta iya tuna waye OGA shamsun ba amma dole haka zata hak'ura ta barwa Allah akan lamarin, ta sani koda tayi galabar rayuwa da d'aya daga cikinsu bazasu tab'ajin dad'in zama da junaba kodan sabida mahaifiyar su, haka tace babu damuwa ta hak'ura ta barwa Allah nasa ikon.......

*******
A parlor hanifer da zuhrah zaune suna kallon wani film na india, haka nan hanifer ta d'auki remote tana shirn sauya channel zuwa wani b'arin, arewa 24 ta mayar inda ran zuhrah be mata dad'i ba, kobazataci darajar zamtowar ta mata a wurin yayanta ba aitaci darajar gidanta ne ko, kallonta tae da kamar ma bazatae magana ba sekuma tace

"Hanifer inaso in k'arasa kallon film d'in nan ki mayar mun mana" harara hanifer ta aika mata

"Ban ganeba? Nikuma wannan nakeso?" Ta fad'a cikeda tsiwa yau dai zuhrah takai mak'ura wurin jin takaicin wannan wulak'ancin na hany

"Amma ya kamata kisan cewar nan d'in gidanane ko? Kuma kayan dasu nazo bawai anan nazo na samesu ba, haka kawai kinzomun gidan mijina kin hanani rawar gaban hantsi?" Wani mugun kallo hanny ta wurga mata

"Mijin da ake cin amanar sa? Ana waya da wani gardin ana masa alk'awarin za'a kashe wannan auren aje a auresa? To wane kuma daren ne jemage be ganiba?" Wani yanayi zuhra ta tsinci kanta aciki

"Sharrin dazakimun kenan?" Harararta ta k'arayi

"Sharri a ina? Nan nan ko sanda yaya bashida lapia zaman waya kike dashi agidan nan ba dare ba rana, wlhy sekin shiga taitayinki dani danni nan har recorded audio inadasu na conversation naku, kije ki bud'e wayanki kema zaki jisu ai, ana d'auke da igiyr auren wani ana zuba shashancin bin maza a waje, andaiji haushi wlhy ina tantama idan wannan cikin ma na yaya nane, tunda an iya waya da gardawa agidan miji" shiru zuhrah tamkar ruwa ya had'iyeta, batasan ya zatayi da yaa Faruk bane, tayi tayi ya d'age mata k'afa har su rabu da Abu hurairaih amma yaqi, kira naci kodawane lokaci, yatasan zatayi dashi, dariyar hanny ce ta katse mata tunanin ta

"Idan mutum ya isa daya musa dan gyatumar sa, wlhy kifi yana ganinka mejar koma, abu d'aya zaki ki tsira da sharrukana shine kafin kibar gidannan ki sanya yaa Hurairah yae ta biyu dani, nikuma zan taimakeki ya sakekin yanda kika buk'ata dazaran kin haihu, kinga daganan kema kyaje ki auri wanda kike so" wani abu zuhrah taji ya daki k'irjinta dabatasan yana duniyar bama, mekenan taji da wannan kalaman na hanny? Koda take cewa ta kamata tana waya da wani da zancen waiko cikin bana yayanta bane hankalinta danqirjinta basu doka kamar wannan maganar datake yanzu ba!!!! Da k'yar ta mik'e tsaye sabida nauyin cikinta ta kalleta

"Duk wani abun da zaki fad'a akan yaa faruk bana tsoron ki gayawa koma ubanwa zaki gayawa, abu d'aya nakeso ki sani shine mijina ko mutuwa naga zanyi bazance ya aureki ba, bakizo a kishiyaba ma kinzo da salon iskanci kala kala balantana kinzo a kishiyar?" Wani shak'iyar dariya hanifer tayi

"Yarinya zakisha mamakin abinda zan miki wlhy, muje zuwa" tana kai nan ta wurgar da romote tae juyawarta zuwa d'akin ta....dafe kanta tae tana mejin duniyar tana juyawa mata, yaya zatayi da Hanifer? Ina zataje da wannan nauyin da xuciyarta ke mata?...

**********
*Bayan sati biyu*

Anyi nasarar zuwa garin nasu Lawuri sedai anci bak'ar wahala, inda fiye da rabin mutanen sun karb'i musulunci bayan da bayarben malamin nan da mahaifinsa suka jagoranci tafiyar, abubuwar da dama sun faru inda daga bisani Sarki k'uru me sunan (ABUBAKAR) a wannan lokacin ya tilastawa sauran karb'ar addining na islam, had'e da rufe duk wani abu daya shafi tsafi a garin dakuma mugwayen al'adu, wasu marasa rabo sun gudu yayinda fiyeda rabi da kwatar mazaunan yankin suka karb'i addinin islam, k'auyen dake cin naman junansu ma bawai an barsu a baya bane, inda seda aka gano sud'inma yarbancin suke sedai su tasu rayuwar mara 'yancine, cin naman junan ya samo asaline tun kafuwar garin, Allah yayisu wasu irin dabbobin mutane marasa dabara, yunwa data soma addabarsu sesuka soma yakutar naman jikin juna daganan kuma se abun yazama al'ada duk wani abu daza'ayi indai aka kamaku kuna magana me tsayi ta kanku akeyi..... Shisa zakaga garin tsit, da abinci da sauran abubuwan jin dad'i aka rud'esu take suka bi addinin islam.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.