Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 21 of 52
Wanka yae a sukwane ya kimtsa cikin kayansu na yamma, yana mamakin yanda Huraira baya gidan, yasan halinsa seyaje tile making company d'inan dukda yace dashi ya zauna shi zeje da kanshi tunda ya sani k'arfin hali kurin yake amma bashida lafiya.
Sakkowa yae yazo ya zauna suna kallon atare, ya fahimci baya gane komai dan haka ya mayar musu tashar yarbawa lokaci d'aya yaga ta mayar da hankalin ta har tana murmushi idan akayi abun murmushin, kallonsa tae tanaso ta tambayeshi abu game da film d'in batasan ya zatayi ba, ga yunwa tun safe bata qara ci ba, kalma d'aya ta rik'e da ake yawan ambata
"Baba ladi kawomun abinci" kallon sufyan tae tace
"Aboo Shufyan Baba ladi kawonun abinshi" duk yanda yaso ya b'oye seda yae dariya me sauti
"Lallai Lawuri anji garau, kirawo Baba ladi yaje yae ya dawo tare da ita, ya nuna Barbo da d'an yatsa yace
"Barbo" ya k'ara nuna Lawurin yace "Lawuri" ya nuna kansa yace "Abu sufyan" sannan ya nuna Baba Ladi yace "Baba Ladi" murmushi tae sabida lokaci d'aya ta fahimci abinda yake nufi, k'ara nuna ta tae tace
"Baba ladi" murmushi yae yana tafa mata alamar ta haddace, sannan ya zauna itama ta zauna bayan ya gayawa baba ladi ta kawo mata abincin, koda ta kawo shiya karb'a ya kalleta yana nuna abincin yace da hausa
"Abinci" jinjina kai tae Ta maimaita kalmar abakinta, ya kuma tura plate d'in agabanta yana murmushi, gyara zamanta tae lokacin Barbo tabi Baba ladi kitchen kasancewar ta mata alama da hannu akan tazo, ta sanya hannu ta ebo shinkafar tana shirin kaiwa bakinda ya rik'e mata hannu da hannunsa na hagu, ya ebo abincin da spoon da aka kawo mata ta janyeshi gefe ya Furta
"Bismillahi" kafin yakai bakinsa ya tauna, tare da sake mata hannunta, bata fahimce saba ta k'ara yunk'urin kai lomar bakinta ya rik'o hannun da sauri
"Bismillahi" ya fad'a da k'arfi kad'an, nuna kanta tae da d'an yatsanta
"Bishmillahi" sake mata hannun yae ta kai lomar bakinta murmushi ta msa sanda ta k'ara ebo wata lomar ta k'ara cewa
"Bishmillahi" kafin taci murmushi yae ya nuna d'an yatsansa manuni yace
"Bismillahi" bata gane ba dai sabida haka ya k'yaleta duk loma d'aya setayi Bismillah ya zauna yana zuba mata murmushi harta cinye tatas sannan ya tashi ya haura sama gun mom.
************
Wani kallo hanifer ta watsawa Lawuri cikin tsana, b'ata rai sosai tayi cikin baqin ciki, tamkar zata saka kuka ta soma yayyafa masifa tana nunata da d'an yatsa
"Ke wace irin jakace wai? Jahilar inace kene ehhh? Mesa bakida hankali so nawa zan nuna miki yanda ake amfani da kayan toilet d'innan, kalli wani salon iskanci yanda kikai wasa da kashi, kashi a k'asa dan bala'i, wannan yarinyar nan ji nake tamkar in shaqe ki shegiya kowa ya huta" kuka wiwi Lawuri ta saka, koba komai a k'alla Hanfer zatayi 22yrs yayinda ita take teenage age nata sam sam bazata shallake 16 yrs ba inma tayi
"Wuce muje wlhy sekin tattare kashin cen da tissue, dan bawai gyara shi zanba, er mutan jeji shegiya kawai" Bata fahimceta ba seda ta nuna mata hanyar toilet da hannunta, sumsum ta wuce tana sharar k'walla, Barbo ma tabi bayanta tana jan jiki, tissue ta ebo ta mik'a mata tace
"Kwashe shi?" Bata fahimtar hausar ta sabida ha ta karb'a tayi mata tsuru da ido kurun, wata tissue ta yaga ta nannad'e hannunta da leda ta tsuguna ta kwashe d'an kad'an d'in kashin dayake gun ta hurga tissue d'in a WC na toilet d'in tana mejin qyanqyamun hannunta,sannan ta nuna mata ta duk'a ta kwashe, tsaye tsayi k'yam seda ta gurfanar da ita, ta juta tana yayyafa masifa akan lallai ta tabbatar ta kwashe shi itada baiwar ta ta barmusu tissue anan, haka ta fito tana yamutsa fuska, su kuma suka tsuguna Barbo tana cewa ta bari tayi amma bata bati ba, garin kwashe kashin duk suka bar layi layin kashi dasuke ja da tissue basu goge da kyau ba, kuma wurin wurga kashin a WC suka b'ata WC (water closet) d'in, seda suka wanke hannunsu sannan suka fito dama wanka zatayi da towel d'aure ajikinta tashiga da zmar tae flushing na waccen qazantar tae wanka, kurun taji warin yana tashi koda ta duba gaba d'aya basu wanke gun ba gashi farin tile ne, basu kuma goge da kyau ba hasalima garin goge war sun shafa hadda inda babu da, a fusace ta fito daga toilet d'in ta soma wankama Lawuri mari tana zage zage, fita tae da gudu tana hargowa yanda yarbawa keyi tana bada hak'uri Baiwarta ma se rarrashi take, amma ina se wanka mata mari take da duka tako ina, wannan yayi daidai da shigowar abu huraira, cikin tashin hankali yae kanta, da lafiyayyen mari
"Hanifer kina haukane? Meta miki dazaki dinga dukanta, ko baiwar gidan kuce aka gaya miki?" Dafe kincinta tae cikeda mamaki take kallon sa, tazo iya wuya baqin ciki da kataici sun mata katutu, harta soma k'walla, murya na rawa tace
"Yaa Huraira wasa fa tae mana da kashi a toilet" cikin qarajin dabata tab'a yayi ba yace
"To sai me? Is that reason enough to beat her like this? Are u mad? Sekace bakida hankali?" Kalmomin sa sun mata ciwo ainun, dama yanada zafi sosai shi kam, hanifer ranta yayi zafi ita kanta, tunda take da Abu Huraira be tab'a kwatanta yi mata tsawa haka ba, ko duka, duk azababben son nan datake masa wanda harta kasa b'oyewa ya sani kuma tasni itama shi bata gabansa amma beta nuna mata qiyayya ba, kome take so yana mata, daidai da zance ma idan ta roqa zuwar mata yake, bata tab'a ganin fushin sa akanta ba, duk akan wannan banzar Lawurin? To akan me wlhy setayi sanadin barinta gidan har abada....
*Inshaa Allahu zan riqayin post biyu a rana, kuyi hakuri masoyana yanayin jikinne ke hanani sukuni.*
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Book nawa na siyar wane idan kinsan bki biya ba karki karanta dan Allah, idan kika karanta baki biyaba kuma Allah yana kallonki, masu taya masu fitarwa yad'awa kuma kuji tsoron Allah, me buk'atar karantawa ya nemi wannan lambar 07084161619*
14
Hannu ya sanya ya tashi yarinyar tsaye duk jikinta rawa yakeyi tashiga rud'ani tunda take 'yar gatace ba'a tab'a dukan ta ba, ko yaya duka yake seta shiga tashin hankali, jiyake tamkar ya rungumeta k'irjinsa, dukda yake yasani k'aramar yarinya ce amma ya tabbatar ta wuce ya rungumeta matsayin sa na musulmi, tana rik'e a hannunsa ya haura saman sa da ita, a bakin kujrar parlorn su ya ajiyeta ya shiga ciki ya watso ruwa ya sanya qananun kaya ya dawo ya zauna kusa da ita, hannayensa duka biyu ya hard'e alamun rok'o akan tayi hak'uri, murmushi tae ta shiga nodding kanta alamun ya dena mana, Abu sufyan yafishi iya magana da ita dukda haka tanajin dad'in yanda shima yake kulawa da ita sosai, bata gajiya da kallon sa ko kad'an, yanda yake kafe ta da ido abun yana narkar da ita batasan metake jiba amma takan kasance cikin nutsuwa. Da hannu ya mata alama akan taje tae wanka, jinjina kanta tae cikeda tsoro, mik'ewa yae yana mejin zafin dukan da aka mata, kai tsaye d'akin su cya ya wuce, acen ya tarar tana zaune ta rafka uban tagumi kallo d'aya zaka mata kasan ranta a jagule yake, kusa da ita yaje ya zauna ya rik'o hannunta
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.