Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 37 of 52

Abu hurairah yayi matuk'ar bak'in cikin abinda ya auku tsakanin sa da xuhra, dukda yasani matarsa ce amma beso auren nasu yaje ko inaba, yasone ya sauwaqe mata igiyoyin auren sa dazaran sunbar nan, yanzu babu wanda yasan tayi aure ya soma sakin yarinya azo kuma amata aure miji yaga fanko, shikuma harga Allah be tab'a ze iya aikata mata hakan ba ko a mafarki.

*********
*Bayan sati uku*

Zaune suke dukkansu durk'ushe aganan sarkin rugar ard'o kamar yanda sukaji 'yan rugar suna kiran garin dashi, bayan yagama jawabi yace ya aminta dasu su shirya jibi su kama hanyar dazata sadasu da garin se sanya dai a rakasu su hau motar jalingo, dan nanne babu nisa ko kad'an da k'auyen nan, sunsha mamakin jin wannan zagayen dan itama dama OGUN aka turata wani k'auye a wara makarantar gwnati yin bautar k'asa....godiya sosai sukayi yace,kud'ad'ensu suna nan ze basu su tafi dashi nanma godiya sosai sukayi kafin su koma bukkar su.

Dukkaninsu shiru sukai suna tunanin duniya kowa da abinda yake sak'awa, daga ranar da wannan abin yashiga tsakaninsu Hurairah be k'ara kwanciya a d'akin ba, ita kuwa tsabar kunyar sa ya sanya ko magana ma bata iya masa se dole......

"Zuhrah nasani kina kallona akan na aikata ba daidai ba amma ina me baki hak'uri akan hakan, banyi da niyyan cutarwa agareki ba haka Allah ya tsara mana, idan mun samu fita lafiya zanyi k'ok'ari in kaiki gidan iyayen ki kinji" batace masa komai ba harya k'araci zancen sa dai......

********
*Bayan kwana hud'u*

A jalingo ma a hotel suka kwana kasancewar sunyi shigar dare bayan ya siya musu suturu irin nasu sunci abinci irin nasu, zaman d'akin hotel d'in ma shiru shiru kake jinsu kowa tsit, har sukai bacci, itace akan gadon shikuwa a saman kujera, sallan asuba sukai sabida yanayin sauyin wurin kwanciya suka k'ara kwantawa koda suka farka ma azahar, sunsha mamakin baccin dasukayi koda yake hakan baya rasa nasaba da yanayin gajiya da sauyin masauki bayan wani dogon lokaci, sanda sukaje tasha ma babu motr abuja a wannan lokacin sabida rana tayi, haka suka koma kwana se washe gari suka tashi.

K'arfe 3:pm a abuja ta musu suka samu kansu cikin yanayin jin dad'i mara misaltuwa, haka suka kwashi jiki zuwa gidan su Zuhra duk garin ya gama sauya mata kwata kwata, da wannan suka samu kansu da tarba cikin murna da tsananin mamaki ga ahalain zuhrah, mahaifiyarta ta samu nutsuwa yanzu kam jin komai suke tamkar a amafarki bayan dogon lokaci harsun cire rai da samun 'yarsu, Hurairah ya samu tarba me kyau inda ya tafi akan labarin me tsayi ne saji komai daga bakin zuhra kafin ya dawo tukunna.

A babban parlor su zuhra dukkansu sunyi tsaye sabo turken wawa zuhra idan nan yayi narai narai yana shirin kawo ruwa, matsawa yae ya rik'e mata hannunta d'aya

"Karki sanya damuwa a ranki, da kaina zan musu bayanin komai kedai ki nutsu ki kwatar da hankalin ki, zanje gobe zam dawo tunda gari d'ayane" batace komai ba dai sabida yace bayason surutu, sake hannunta yae

"Nizan tafi sena dawo tukunna kinji" da k'yar ta iya furta

"To Allah ya tsare hanya Al-hassan seka dawo goben" harya juya tace

"Al-hassan?" Waigowa yae yana saurarenta, so take ta gaya masa cewar kusan lokacin al'adarta ya wuce da sati biyu amma batasan ina zata soma ba, murmushi tayi na yake

"Ka gaishe da mutan gidan" shine abinda tace, murmushi shima yae ya juya yana matuk'ar jin tausayin ta, ita dashi har abada, bazata k'ara ganin saba, idan ya nutsu ze dawo acikin sirri ya baiwa me gadin gidan takardar ta sabida ta samu freedom.

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

26

Ihu sosai kakeji yana tashi daga wajenngate d'in gidan da sowar sojojin dake k'ofar gate d'in gidan, sunata wak'ensu irin na soja idan abu ya musu dad'i ganin Huraira, kallo d'aya suka ganeshi dukda ya rame sosai sabida sunsan yau Sufyan yana ciki kuma shi kamar ma bashida lafiya, General dake daga ciki da hanzari ya sakko k'asa cikin mamakin wane abu ne yawa sojin dad'i har haka suke zuba wannan uban ihun kamar ba gobe, Wanda ya ganine ya sanyashi yin mutuwar tsaye cikeda mamaki, daga wurin Abu Huraira kuwa da gudun fanfalak'i ya ruga zuwa jikin dad yana k'ugin murna da ihu sosai, rungumeshi dad yae duk yanda yaso ya hak'ura seda ya zubar da k'walla irin na d'a da mahaifi, yana sake Hurairah kuwa anan ya zuba yanawa Allah sujjadar godiya da amsa masa adu'ar sa da yae cikeda farin ciki, Cya da Hanifer da mom ma da gudun su suka sakko, suna ganin huraira dukkansu suka rungume shi, lallai wannan shine ikon me duka, se kukan murna ke tashi, Sufyan dake kwance a parlor na side d'insu jin sowar tayi yawa ya sanyashi sakkowa cikin kasala.... A parlor yae karo dasu cirko cirko sukai suna kallon juna ya gagara k'arasa sakkowa daga kan benen ma, a hankali Huraira ya taka gunsa cikin mamaki, hannayensa duka biyu ya d'aura akan kafad'un sufyan

"Al-hussain lafiyan ka kuwa meya sameka haka ka ganka kuwa?" Rungumeshi sufyan yae gaba d'aya

"Wlhy ba mafarki nake ba kaine Al-hassan, na zata mafarki nake ashe zan ganka a rayuwa Bro ashe kana raye?" Ya saka wani gunsheqen kuka me ban tausayi.... Hurairaha ma kuke yakeyi

"Twin duk ka sauya, meya seka haka ne wai? Hankalinanya tashi daganin ka haka" Takaici ya tasowa sufyan na ganin yanda d'an uwansa ya damu dashi f8ye da yanda ya damu da kansa, be bashi nsaba se janyoshi da yae suka zauna sosai acikin parlor.....

***********
*Bayan sati uku*

Zaune take tana nazarin halin data tsinci kanta aciki, dukta gama gayawa mahaifanta yanda akayi dakuma meya sameta amma ta gagara sanar dasu zancen auren datayi a ruga, acewarta se Abu Huraira yazo aganansa sesu gayan musu, amma ga mamakinta yau kimanin satuka uku kenan ba Abu hurairai babu labarin sa, ga al'adarta har yau shiru babu labarin ta, ko ba'a fad'aba ta sani ciki ne da ita, sallamar me aikin sune ya k'atse mata tunanin ta ta d'ago ta kalleta

"Anty wai Daddy yace kije parlor ga Faruk yazo" k'irjinta ne yae mugun dokawa ta kalli Hafsat din

"Faruk wanne kenan?" Murmushi yarinyar tayi

"Anty ban dad'e nan gidan ba amma ina yawan ganin sa, duk juma'a yakan zo gaskia" hankalinta ya tashi sosai ta mik'e taje ta sanya hijab ta wuce parlor d'in.....kallon juna sukeyi basako k'iftawa kowa gani yake tamkar mafarki yake dayaga d'an uwansa, runtse idanta tae kafin ta k'araso cikin parlor d'in

"Yaa Faruk Barka da zuwa" shine abinda ta furta masa cikin sanyin jiki yana murmushi sosai yace

"Rose kece kuwa? Kenake gani agabana yanzu? Ina sokoto sanda labarin dawowar ki ya sameni, bansan sanda na ganni a Abj ba, nayi matuk'ar farin cikin ganinki, har kukan rashin ki nake Rose" Zama tae shima ya zauna ya janyo hannunta

"Rose kinyi bak'i, kin sauya kin fige kin zama wata kala bani labarin meya faru dake?" Murmushi tae
"Labarin da tsayi sosai yaa Faruk, amma dai rayuwar jeji ce bako d'aki se bukka, bako suturu se ganyaye da fata, ba komai najin dad'i basu masan annabi ya faku ba" Jinjina kanshi yae

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.