Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 4 of 52

*Washe gari*

    K'arfe bakwai na safe suka fito, inda suka tarar Baba azumi harta rigasu bakin motar, sunyi breakfast awurin inda suka biya wani wurin suka kwashi kayan snacks musamman cake dai suna sanshi sosai babba d'aya suka siya da qananu se donuts da sauransu, Baba Ladi kam har bread tasa aka siya mata kusan k'waya 4 da kayan shayi akan idan taje tariqa yin kalacin safe, komai sun tanadarwa kansu, daidai da ruwa sun nemi carton na faro me 24 aciki, drink ma haka, daga nan gidan mai suka nufa sukayi wa motarsu full tank, hadda siyan wani a jarka, dukda kuwa Abu sufyan yana ganin had'arin d'aukar fetur a hanyan dabasu san yama take ba, haka Abu huraira yace dashi basusan nisan wurin ba, ya tsani short na mai a mota, kuma sun samu anwa jarkar d'aurin kazar kuku an d'aure sosai, beside bama boot bane ba irin haka ai a bud'e bayan  yake kayan Babane kurun da en tsarabe tsarabenta se suka rufe da k'yalle sabida k'ura....da adu'o'in tsari d'auke abakunansu suka d'auki hanyar k'auyen na b'ingirau dake cikin jeji  me nisan gaske.

************
Sosai suka gajiya da nisan hanyar dasukebi, gashi dai garin maman ba cikin wannan nahiyar ba, ace tafiya tun bakwai na safe sukeyi har yanzu k'arfe biyu da rabi ta gota, sukam yaushe suka ajiyeta har suka juyo zuwa masauki, Tsaki kuwa Abu sufyan yayi yafi so hamsin, har ita Baba ladi da kanta ta kula da k'osawar da yae, ita da kanta taso General ya barta ta hau motan kasuwa amma ya kafe, sassanyan ajiyan zuciya ta sauke ganin sunzo hanyar dazasu yanki jejin daze sadasu da K'auyen na B'ingirau, da hannu ta nuna musu suka kuma karkata akalar motarsu zwaga wannan b'angaren Abu huraira ya juye baki da harshen turanci yace da Abu sufyan

"Abu Takobi kaga wannan jejin kuwa, kasan wai jikina ya soma mutuwa, a gaskiya dazaran mun ajiyeta mu juyo sabida ina jiye mana yin dare a wannan muguwar hanyar" Kawar da kanshi yae gefe d'aya ya kaiwa agogon hannunshi kallo

"Dama munsan hakane aida yaseen a motan haya zamu d'urota, yanzu fa uku saura mintuna biyar kacal, dama mun juyo ne mu soma timing amma wannan masifar har ina?" Dawud ne ya karb'e zancen da cewa

"Ba masifa bane ba kadena kira mana ita, idn dai kan wannan hanyar ne ai inaga zamu juyo dare be mana ba" shiru dukkansu sukai, zuwa hud'u saura kwata sun k'arisa garin, mafiya yawancin mazauna garin fulani ne kamar Baba ladi, harkokin su suke gudanarwa cikeda aminci, sun gaggaisa da mutane kansu tsaye suka nemi yin salla azahar da la'asar kansu ce zasu koma, duk yanda akaso suci abinci sun gagara tsayawa se wuraren biyar da rabi ma sukai shirun tahowa duk saurin dasukayi...wani mutum ne me tsananin kamanni da Baba ladi yazo ya kalli Abu sufyan daya karb'i tuk'in motar ganin kamar Abu mage ya gaji yace dashi

"Yaro dazaku bi shawarata dakun hak'ura da tafiyar nan zuwa asubahi, komu damuke da garin nan bama yi masa fitar yamma, koba komai kuna baqi seku saki hanya ai" kallon Abu Sufyan yae cikeda takaici yace

"Kamana adu'a lafiya lau zamu fita mun gama haddace hanyar inshaa Allah" jinjina kanshi yae alamun gamsuwa yace

"Idan kuka miqi hanya zuwa gabashin nan, karku neki ko washe hanya sheta kudu, kunayin kudu kuka raba jejin masarau biyu seku yamma kuyi arewa se titi kuma, kushkure d'aya jal je sanya ku shaki hanya, kuma shakin hanya a wannan daren baze muku da kyau ba, ina muku fatan alheri kaji ko" jinjina kanshi yae yana sakaya murmushin yak'e kansu d'aga musu hannu subi hanyar daya dace...

**************
Shiru dukkansu sukayi kowa da abinda yake sak'awa aranshi, jin kafewar tayar motarsu ne ya sanya suka kalli juna shida Dawud dake gaba yayinda Abu Huraira ke kwance abaya yayi matashin kai da wani trow pillow daya zame masa abun yawo duk inda zashi, shi d'inma d'gowabyae yace yadai?" Cikin sanyin jiki yace

"Ga duhu ya soma sauka, ji nake fa kaman laka ne muka mak'ale aciki, amma ai d'axu bamu bi wata hanya me laka haka ba ko?" Wasu yawu Masu d'acin gaske ya had'iya kanyace

"Ko kusa bamu wani shiga laka ba gaskia, amma kaja da kyau mana" Iyakar dagewar shi yaja ya taka totor amma sam motar taqi ta motsa, kashewa yae suka fito dukkansu, babu wanda jikinshi be b'aci ba, lakar ce kuwa tsaki Abu Sufyan yaja ya koma cikin mota sukuwa suka ja baya suna me karkad'e k'afansu daya lalace da tab'o, giya ya sauya zuwa me iya fitar da motar daga wurin, dama Allah ya imakesu Hilux ce seta fito daga cikin Lakar lafiya, duhu ya soma sauka wannan ya sanya dawud ya ciro wata k'atuwar waya a aljihunsa ya kunna torchlight dake jikinta me hasken gaske, kai tsaye ta mamaye lakar da haske arziqi ma sukayi irin me zurfin gasken nan ce, cikin damuwa Abu Sufyan yace

"Dawud anya bamu sake hanya ba kuwa? Nifa sam babu wannan lakar a inda muka biyo ni gaskia na tsorata" Dafe kai sukayi dukkansu kansu d'akko ruwan faro dasukai guzurinshi su wanka k'afansu dashi sannan su koma kotar, sunyi adu'a kafin su d'auki hanyar dasuke tsammanin ita zata fitar dasu kan titin dabeda maraba da babu....

K'arfe takwas ta gota sanda Dawud cikin damuwa yace

"Abu sufyan ka kwatanta ka gani, uku saura mintuna biyar muka yanki jejin nan d'azu, kuma koda hud'u saura kwata tayi fa mun isa qauyen kaga tafiyar 45 mns ta kaimu, yanzu kuwa tun biyar da rabi muke zagayar jejin nan, ko shakka banayi wlhy b'atan hanya mukayi" wani dogon burki yaja ganin k'aton maciji agabansa gudun karya taka shi, bakinsa har rawa yake ganin macijin ma yaja burki ya d'ago kai yana kallon haske fitilar motar sekace yana ganinsu

"Abu Huraira maciji" Lek'owa shima yae shida Dawud, lokaci d'aya suka shiga ambaton mahalicci, basuko matsaba kuwa kaman yanda basu d'aga da motar ba konan dacen ganin yanda macijin kr kallon su kaman wani mutum.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: 🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

*Littafina na kud'ine dan Allah idan baki biyaba karki karanta, idan kinaso ki biya kudi ki riqa samu a kud'inki*

02

Adu'ar tsari dukkansu ke karantawa har suka ga macijin ya wuce abunshi batare dayayi ta kansu ba, dukda Ac dake kunne a motan hakan be hanawa dukkansu tsiyayar da zufaba

"Abu sufyan ina wannan kalan macijinne ke had'iye mutum?" Wasu yawun wahala ya had'iya kafin yace

"Ni gaba d'aya na rikice ma, jikina yae sanyi sosai da tafiyar nan, ina roqon Allah ya mana shamaki daduk wani abun k'i" cikin damuwa Abu huraira yace

"Yanada girma amma da wannan macijinne aida motar gaba d'aya xe had'iya sedai fa aganina mu juya gwara mana kwana a k'auyen nan da mu lula acikin wannan jejin, ko shakka banayi mun sake hanya sosai" Nisawa Abu sufyan yae

"Bazan iya tuk'in nan ba, mu juya kawai kaikaja" cikin damuwa Dawud yace

"Kai yanzu seka sauka ku juya, kana ganin wannan mucijin, idan kuma be tafi bafa, kaidai ka juya kurun" haka ya juya akalar motar sa sukaci gaba da tafiya........

**********
"Bana samun number yaran nan koyaya na gwada, rabon danayi wayama dasu tun da rana dasukaje ajiye Baba ladi, ga garinsu babarma ba Ntwrk inaga dan wayanta itama a rufe" Kallonta General yae cikin takaici

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.