Complete Hausa Novels

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 39 of 52

**********
Zaman shiru tayi a hotel d'in data kama da kud'in da hurairah ya bata acikin na b'arayin nan, ina zata dosa ko sokoto zataje? Mesa Al-hassan ze mata haka? Meta masa ne arayuwa ze aikata mata hakan? Koda tamasa uzurin nesan tanada ciki ba amma ai yasan bazata dauwama da igiyar aurensa ba, yanda yasan ba santa yake ba haka itama Faruk ne zab'in ta, batasan dalilin daya sa take jin tamkar baze iya aikata mata hakan da sanin saba, wannan rayuwar k'unci da bak'in ciki baze iya taba sanyata aciki da gangan ba, Al-hassan mutumin kirki ne baze aikata mata hakan ba.
Idan tace sokoto zataje tonon asirinta ne, babu yanda za'ayi Faruk ya amince mata, yaya ze d'auki maganar jin cewa tayi aure? Beside bata tashi zancen tayi aureba seda ciki ya bayyana, ko alama bazata iya zubar da cikin taba koda shege ne bare da d'an halas ne da ubansa, toko gun k'anwar mamanta zataje kaduna? Cen d'inma dai tonon asirinta ne tunda tak'i auren kamal yaron k'anwar mamanta bata k'ara samun jittuwa da ita ba dariya zasu mata, wane wawan ne ma ze aminta da maganar ta dama huraira yana kusa ne watak'il daya kareta, kuka kam ta shhi ba adadi, Abuja garine me tsadar gaske babu ta yanda za'a yi wannan d'an kud'in ya rik'eta a hotel, babu k'awar dazataje gidansu da ciki kobe fitoba yanzu ze bayyana ne bada jimawa ba, itakam yazatayi.

**********
*Bayan sati shida*

Babu inda ake neman mutum agarin abuja inda Abu Hurairah beje neman zuhra ba, shi sabida tsabar son ganinta ma harya manta da wata aba wai ita Lawuri, hankalinsa in yayi miliyan toko atashe yake sabida neman zuhra, agun megadin gidansu yakejin bata k'ara dawowa ba tunda ta tafi, yauma kamar kullum tare da Al-hussain sukazo, bayan sun gamajin bata zo gidaba suka dawo mota suka zauna, Abu sufyan ya kallesa cikin kulawa yace

"Abu Huraira so tari mutane suke mun kallon me kafiya da akan al'amura amma azahiri ninasan kafini kafiya akan komai ma, babu abinda iyaye bazasuyi ba, kazo muje mu samu su dad nida kaina zan musu bayanin komai yanda ya kamata nasan zasu fahimceka semu tuntub'i iyayen yarinyar nan susan me ake ciki, wannan b'oyon baze k'are mu da komai ba, kodan tausayin wannan yarinyar ka taimaka ka bayyana gaskiya, bamusan halin datake ciki va ga ciki ajikinta ya dace ayi wani abun gaskiya" Jinjina kanshi yae

"Muje to gidan seka musu bayanin komai"haka suka rankaya zuwa gun dad.

*******
Tunda Lawuri ta dawo hayyacinta ta tariyo duk abinda ya faru se hankalin ta ya mugun tashi, tanaso taga Abu Hurairah ko yaya ne, da gaske tayi murnar ganin iyayenta amma bata farin ciki barin su Abu hurairah tana me aka dawo da ita gidan? Ta tuna komai ta gane komai ta fahimci komai daya faru rad'am!! Ina zataje taga haske, tundaga sannan kullum seta yiwa mahaifinta kuka akan ya sanya a mayar da ita ta masa alk'awarin zata dawo, da wannan yace babu damuwa ze bada dama taje wani satin, tunda tasan hanya inyaso gardawa sesu rakata....... Tofa!!!!!!

**********
Dad shiru yae yana tunanin wannan zancen dasuka zo masa dashi, mom ma tarasa ta cewa, sunyi shiru na wasu en dak'ik'u kafin General yae gyaran murya cikin b'acin rai yana me kallon Huraira yace masa

"Kai yanzu da hankalinka da komai Abu Hurairah zakayi wannan sakarcin, ni bama zancen auren ya dameni ba, na tabbatar bazakayi aure da gangan ba abu mafi ban haushi da takaici yanda ka b'oye mana 1, 2 kuma yanda ka cutar da yarinyar mutane, wani shegen ne yasanya ka tara da ita bayan kasan basanta kake ba, idan ma hakanne bazaka sauwaqe mata iymgiyar aurenka ba batare daka koda tab'a taba se tsabar rashin hankali ka daddage kawa matar ka ta sunna ciki sannan ka barta da ganin garari? Ni yanzu me kakeso nayi? Idan da siyama aka mawa zakaji dad'i ne? Eh nace zakaiji dad'i ne?" Hakuri ya hau bayar wa, ita kuma mom ta wani b'ata rai

"Haba Ganeral yaran nan sunmaka bayani akan cewar itace da kaud'in d'aura auren ma, bayaga haka aisunce maka so d'aya ne wani abu na auratayya ya gifta a tsakanin su? Abu na k'arshe kuma baya santa koda ganinta akai ni zan saka ya saketa" wata uwar k'ara ya saka irin ta tsofaffin sojoji

"Kee!! Adama wlhy duk rabar daya rabu da ita kema nan gidan zaki bari, kuma seya nemo 'yar mutane, ni zaku kawowa rainin hankali ku mayar dani k'aramun mutum, duk kanin abubuwan dasuka faru kece sila, an kawo yarinya yaranki suna so kince arniya ce babu wanda yazo a musulmi dan gatan sa, Allah ne yaso ya kuma zab'emu, dan ya zab'i wasu bawai illa bane ba, shibe guji bayin sa amma ke duk kin jagula maganar, tun Anan zaki gano cewar Allah mabuwayi ya nuna miki ikon sa, danma be bashi bamaguzar ba, kikakai aya, daya ya bashi musulma yarinyar dayake magana zuhra nasan mahaifinta farin sani, case na b'atanta ma nasan dashi harni anje nemanta dani, Allah ne ya nuna miki abinki kuma wlhy na bashi sa'o'i 72 ya nemo 'yar mutane kona mai hauka nima, zanje in gana da ubanta yanzu shima ya b'ata raina da wayon sa da komai aida ya tuhumeta yaji". Mom shiru tamkar ruwa ya cinyeta d'anya ko motsinta baka ji ko kad'an tsit kakeji.

********
*Bayan kwana biyu*

Daga asibitin ta fito sun koreta akan batada kud'in magani bazasu karb'eta ba,fitowa tayi abin duniya ya dameta, ga d'akin datake zama a hotel kaf har kud'in sark'arta data siyar ya cinye tunda hotel ne, gashi batada lafiya scaning ma takeso amata amma abun ya gagareta asibiti sun gaji sun koreta, asibitin datazo da hotel datake zama ma akwai jayawa gashi 600 kad'ai ne a hannunta ga yunwa, yaudai ta yanke shawarar komawa gun iyayenta hatta wayar da aka siya mata ma ta siyar ta cinye kud'in, da k'afa take tafiya gashi tarasa dalilin kumburin jikinta, cikinta yayi saurin girma wataninsa dudu nawane hud'u fa amma kaman gobe zata haihu, jiri ne yasoma kwasarta adaidai sanda tazo tsallaka titin dashine ze sadata da gidansu General kuwa adaidai nanne yake shigo layin yana k'ok'arin kaiwa mahaifinta ziyara domin su nemi mafita dan tun ranar ya taresa da maganar ma, Kad'an ya rage su bigeta seda koda basu kad'e tanba fad'uwa tayi a k'asa warwas!!!

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

*Book nawa na kud'ine, idan kinsan baki biyaba dan Allah karki karantamun kokimun sharin book nawa a groups, idan kina buqatar siya ki nemeni ta wannan number 07084161619.*

28

Sauka sukai daga kan titin suka fito da sauri duk sukai kanta, basu b'ata lokaciba wurin sakata a mota su juya akalar motarsu zuwa asibiti bayan da suka dire General agidan yabasu umarnin su kaita asibiti cikin gaggawa.

Wayar ya zaro a daidai sanda yazo shiga k'ofar parlor bayan an masa iso, Abu Hurairah yakira

"Hello Dad" cikin dakakkiyar murya yace

"Kana ina ne?" Saisaita nutsuwar sa yae

"Dad ina kan hanya da zanje gidana"

"Kaje National hospital na tura wata patient dana kusan bigeta a titi amma seta suma kaman fad'uwar gabane,tare dasu umar take da sauransu u contact of them, kaje ka biya Bill nata ka tabbatar duk wata kulawa ta samu, ka jira a wurin idan ta farfad'o ta gaya maka gidann su asanar da mijinta ko iyayenta halin datake ciki" kafin yae wata maganar harya kashe wayar... Juya akalar kiransa yae zuwaga Abu Sufyan yace a sanar masa yazo ya sameshi gidan zasu koma gida atare.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.