Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 8 of 52
" kai waye dazaka mana k'aud'i, ka isa kaciyar dashine?" Dafe kuncin sa yae cikin mamaki ya bita da ido beyi aune ba yaji dirar k'asa a idan sa
"Ni wannan abun ze kalla ido cikin ido? Kai d'an iskan inane dazaka kalleni ido cikin ido? Tabbas inaga kaine zamu yankawa Raminus a wannan shekarar" murza idanshi ya hauyi ga k'asar ya shiga masa sosai haka ya dinga murzawa ya rasa inama ze sanya rayuwar sa, Abu sufyan ne ya rik'oshi ya soma hure masa idan sa, haka yae ta masa kowa yae tsit daga k'arshe ya janyo roba daga jakars ya bashi ya wanke masa fuakarsa da idansa seda yaga ya samu nutsuwa sannan ya rik'e hannunshi yaja yayan shi bayan shi ya had'e hannayensa gu d'aya alamar rok'o kan cewar suyi hak'uri, wata mahaukaciyar dariya ta kwashe da ita sannan ta sanya hannu ta d'auki robar ruwan daya ajiye takai bakinta ta k'wankwada, wani iri taji daban kaman an sanyawa ruwan rake lumshe idanta tae ta shanye duka sannan ta kalli Dawud, tace dashi cikin yaren data fahimci yana ganewa
"Ruwan meye wannan?" D'agowa yae ya kalleta amma be bari sun had'a idoba yace
"Ruwan shane" atak'aice. Murmushi tae masa
"Amma ba irin namu bane, ina ku kuka samo?" shid'inma kafirar k'ishi yakeji seda ya hadi'yi bushashen yawunsa sannan yace
"Dashi mukazo daga garinmu, ku taimaka kubarmu mu koma gida, badasan ranmu mukazo nan ba, hanya ce ta b'ace mana" Hannun ta takai taja gashin gemunsa seda yae k'ara sannan tace
"Wannan zan saka a soma askewa, kaf garin nan babu wanda yakeda daman ajiye wannan se Sarki k'uru naka yayi yawa" Bece komai ba se jakar shima daya janyo ya zari robar rowan da itace ta k'arshe ya kwankwad'a sosai yakusa shanyewa ma kanya ajiye, warcewa tae ta k'ara shanyewa kamar wata mahaukaciyar zakanya. Matsawa tae kusada Abu Huraira ya k'ura mata ido, Dawud dayaga kowa baya iya kallonta sosai ya fahimci ba'a kallonta seya sanya hannu ya rufe masa ido, hannun nasa Abu Huraira ya bige ya sake sanya idanshi a nata, matsawa sosai tae kusa dashi tace da macen dake gefenta
"Wannan nakeso abayar wannan shekarar, banason yanda yake kallona, na tsaneshi sosai, da inada hali bazasu sako musu zakiba, shi zan tura" murmushi tae mata
"Lawuri aike ta dabance, koma wani zakin ya zab'a semu mayar wannan" Murmushi tae daya mugun k'arawa fuskar ta kyau ta tab'e baki had'e da d'age kirarta d'aya
"Muje" tafad'a bayan ta juya tana takun k'asaita babu ko takalmi a k'afarta kafatanin garin ma bame takalmi harshi kanshi sarkin, harsun juya ta kuma waigowa ta kalli jakar su dake wurin tacewa d'aya
"D'akkomun abinda ke jakar cen nacikin irin wancen seki bar musu abunsu agun" dubawa tae bame fari seme baqi haka ta d'akko coke d'in d'aya tabar jakar anan, bayan sun gama maganganun dasuke suka ruf'e qofar cake d'in bayan da suka sako musu wani qaton zaki wanda ya sanya Abu sufyan sakin fitsari a wando ya koma bayan tawayen shi, se ihu mutanen garin keyi ganin yanda suka rud'e anata zabgawa zakin kirari, lokaci d'aya ya soma rura yana zagayen su, yayinda su kuma suka had'e gu d'aya suna adu'a had'e da kukan zuci haukace suke dukkansu.
Wurin Abu huraira yae gadan gadan, shi kuwa yae maza yana k'araso jikinshi ya kwanta k'asa ya dakarwa zakin ciki ya hankad'ashi bayan shi seda ya mulmula, tasowa zakin yae ya karkad'e jikinsa ya k'arayi kansa, nan ya soma adu'a dakiran sunan Allah ya k'ara kaimasa naushi ajikin wuya inda ya kuma zubewa, koda zakin ya d'ago sega idanshi yakoma ja kaman jini jikinsa ya koma kalar baki qirin, atake suka fahimci zakin na tsafine
"Ku d'auki ayar Allah Dawood wlhy ba zakin asali bane ba" haka suka had'a baki suna rero ayatul kursiyu da duk wata adu'a da karatun alk'ur ani me girma dayazo bakin su, hakan ce ta sanya zakin ya gagara dogon motsi ya zube agun yana zabga rura, daganan ya soma shure shure, itaciya d'aya Abu huraira ya zaro daga cikin wanda aka kafe akai cage dashi yace
"Allahu Akhbar!!" Ya dab'a mai aciki take agun zakin ya mace beko shura ba, mik'ewa tsaye sarki yae ya kallu k'uruwa yace
"Bala'i ya samemu ance me tarwatsa garin nan shine me kashe zaki, wannan akashesa da ruwan jikin zakin shine kad'ai maganin sa" Itad'inma rikicewa tae tace
"Hakane, daya tarwatsa garinmu gwara mu kashe sa, tunda susu ukune akashe makashin Lamme" haka suka d'auki kuka gaba d'aya garin ana wak'a aka kwashesu suda gawar zagin akai cikin gari dasu, a hanya sukejin labarin za'a jiqa Lamme (zakin suke kira haka), seya kwana ajik'e se'a baiwa wanda ya kashe zakin ruwan yasha shima ya mutu idan ba haka ba, garin ze kama da wuta danme tarwatsa gari ya karkashe su ne yazo idan be mutuba su zasu mutu...... Dawuda dakejin wannan yaren ya sanar dasu me ake cewa suka hau adu'a, yanzun ma a cage d'aya aka ajiyesu akaje domin aje a jik'a gawar lamme akashe Abu huraira.
*Littafina na kud'ine idan kinsan baki biyaba karki karanta dan Allah, idan har kinaso ki siya akan farashin 200 kacal ki nemi wannan lambar 07084161619*
*********
Da sassafe sauya agogon hannunsu sukai da sufyan da zobe harma da rigarsu dayake dama ba kala d'aya bace ba, suka shirya idan an kawo yayi bismillah so 21 shi yasha sun kula tsafine kawai Allah ne kawai ze kub'utar dasu.........
Lawuri duk yanda taso tayi bacci abun ya gagareta, abinda taji suna karantawa da k'arfi shine yake mata amsa kuwa acikin kunnuwanta, ko shakka babu so takeyi ta k'ara sauraren wannan abun, bazata iya bacci basam so take ta rik'aji sunayi koda mutum d'aya ne yana mata, mesa takeson ta saurari wannan abun? Mesa ma takeson yanda wannan yake kallonta? So take taje ita yama k'ura mata idanshi, kodan sabida ba'a saba kallonta bane ba takejin hakan? Tana tsananin son taga idanshi a nata, Kalmar sa ta karshe itace tafi kowacce yi mata yawo sabida yawon datake mata harta haddace "Allahu Akhbar!!", matsafane ko shakka batayi wannan ruwan datasha sun mata wani stafin ne aciki amma bari tabi daren nan taje gunsu ya mata wannan karatun dayake koma su duka su mata.
********
Shirinta tsaf tayi taje inda aka ajiyesu a sace, akwai masu gadinsu a wurin amma setayi magana akan zata gansu ne, suka bata hanya tashiga bukkar, tunkan ta k'arisa gun kage d'insu take kiyo sautin muryoyinsu suna wannan abin irin na d'axu, zama tayi batare data k'arisa inda suke ba tafi 3 hours seda taji shiru sannan tabar wurin, jikinta yana mata wani nauyi mesa bataso suka dena ba? Mesa batajin bacci, ya akayi acikin muryoyin nasu take gane muryan me kallonta ido cikin ido? Mesa ya tsaya mata arai, tsafi ko? Ta ayyana a ranta idan hakane zata gwada cin ubansa tun kafin dare yae mata.
*************
Washe gari dabino sukaci da cookie's da lemo roba d'aya kowa ya kurb'a, gwara sui manage kafin k'aryarsu ta k'are, sunaji ajikinsu cewar tabbas da yardar Allah zasu kub'uta.
Da shirinta tsaf tazo gunsu, itada muqarabanta, fitowa dasu akasa tayi dukda ya sauya kaya kallo d'aya sukawa juna ta gane cewar shine, dariya sosai tayi kafin tace amayar da sauran shi abarshi, sosai suka tsorata naba gaira ba dalili, suna mamakin yanda ta gano lagonsu da wuri haka, kodai wani yaga sanda suke sauya kaya ne? Kai tsafine dai danba wanda ya gansu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.