Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 22 of 52
"Hanny am so sorry kinji" k'wallan datake ta rik'ewa ne ya silalo mata tace muryanta yana mata rawa
"Yaa Mage nifa ba fushi nai ba" nutsuwarsa ya tattare a gunta
"Meta miki hakan nan to?" Cikin sheshekar kuka tace
"Yaa Huraira tunda sukazo gidannan nake wahala dasu akan komai ma, baka ganin yanda nake kulawa dasu shine yaran nan zasu mana wasa da kashi a bayi, naje da kaina na nuna musu yanda zasu gyara mana gun shine duk suka gama b'atawa, rainane fa ya b'aci kurun sena daketa shine fa kaikuma kazo ka dakeni" hannunsa yakai ya shafi gefen kumatunta, ga yatsunsa nan sun kwanta akan farar fuskar ta rad'au gun yayi ja sosai
"Am so sorry pretty hanny, bazan qara ba, kuma zan kaisu gun horo kinsan ba yaranmu sukeji ba dole se hak'uri" batace masa komai ba yakuma cewa
"Ki sanyo mayafi kizo muje ki rakani wani gun" batae musu ba ta d'akko yalolon mayafi dama wanka ta gama ta yane kanta dashi, har lokacin kuka takeyi, hannunsa ya sanya ya share mata hawayen nata
"Haba k'anwata? Yanzu ni laifin daban sabayi ba dan nayi so d'aya seki dinga kuka anata zubamun fushi haka to kiyi hak'uri inshaa Allah bazan k'ara ba" Murmushi tayi tana hawayen
"Yaa huraira nifa na dena ruwan idona ne ya gagara denawa" murmushi yae
"To suma ki basu hak'uri zan siya miki New phone shikenan fushin ya k'are" murmushi tayi ta sanya hannunta ta share k'wallan duka
"Laptop fa mukai magana dakai, ni wayana befi 4month inajin dad'in amfani dashi kurun ka siyan Laptop d'in" jinjina kanshi yae
."ba dakuwa zan siya shikenan?" Gyad'a masa kanta tae alamar eh
"To bansan ganin kukan kinnnan, maza maza ki share wannan k'wallan" haka ta share suka fito seda ya janyo Lawuri da Barbo sannan suka bar gidan, mommy dai fushi take ta zama amaryar kulle a d'aki komai acen ake kai mata, dama zaman babban parlor bawai ya dameta bane ba bare yanzu dabatasn ganin fuskokin maguzawan cen.....
*************
Shop na wata mata yaje dasu bayarbiya, bayan sun gaisa da turanci yake kora mata bayanin sa nason susan rayuwar cikin gari da yaruka biyu Hausa da Turanci, kallon sosai tae masa sannan tace
"Ni shop nawa salon ne kawai kuma kaga hausan be wani rik'eni ba, amma akwai wata 'yar uwata dakejin hausa sosai, inaga cen zaka kaisu setana rik'a musu yarbanci ta fassara da Hausa, from dia seka kaisu sechool" Jinjina kansa yae alamar gamsuwa
"Wane school za'a karb'su ai sunyi girma" shiru tad'anyi kafin tace
"Ka nemi nursery school anty, ka roqeta tamusu na 6month with extra care, ana kammalawa ka kaiwa parimary 1 anty for 2 month haka haka dai, kafin ka kaisu na gaba" kallonsa hanifer tae cikin takaici tamkar zatayi kuka
"Yaya wainikam yaran nan ba garin su zasu koma bane? Menene na cewa sesun iya hausa kuma ko wani turanci?" Wani kallo ya wurga mata daya sanya tasha jinin jikinta
"Amm kozaki tayani yin mata magana da kanki, hausar ce damuwata ni yanzu ba turancin ba" jinjina kanta tae
"Idan zaka dawo dani shop zan raka ka mana, sema muje yanzu" haka suka rankaya rayuwar hanifer ba dad'i ko kad'an, yayinda matar kewa Lawuri bayani da harshen Yarbanci akan abinda yakeso su iya da inda zasuje, takula yarukan sunada banbanci sedai ba cancan ba.
**************
Kaman wani wawa haka yashigo gidan a sukwane, kai tsaye kuma d'akin su Hanifer ya wuce, Lawuri yakeso ya gani akwai inda yakeso suje yau,a hanya yaci karo da mom tafito daga d'akin kallon sosai ta masa fuskar ta ba yabo bakuma fallasa
"Ina xakaje ne?" Ta tambaya, shida kanshi yau yasha jinin jikin sa da yanayin tambayar ta da kallonta harma da fuskarta
"Gun Cya zanje mom"
"Zakaje gun bamaguzar cen kai, yanzu Sufyan adalci kenan dakake ganin zakumun? Haka muka saba daku, kashigo gidan amaimakon kaje guna yanda kuka saba shine zaka zo neman wasu Arna" Jikinsa ne yae matuk'ar sanya ya matsa sosai kusa da ita ya d'aura kanshi saman kafad'arta ya rik'e hannunta d'aya
"Kiyi hakuri bazan k'araba mom kinji" kawar da kanta tae gefe d'aya
"Amma yaushe zakuwa Daddyn ku magana ya sanya soja su mayar dasu garinsu nifa sam hankalina be kwanta dasu ba"
"Idan haka ze baki nutsuwa ki bari ya dawo zan mai magana a mayar dasu kinji mamana?" Murmushi tae
"Naji kamaci abinci kuwa?"
"Yanzu na dawo mom, Cya dama zance tazo ta dafan chips" Murmushi tae
"Cyama bata nan hanifer ma haka, har baqinku ma sun fita da Huraira inji Baba ladi, kaje zan maka, with fried egg zakaci?"
"Ea, nagode mom" ya furta had'e da sake ta ya juya zuwa part d'insu, zama yae ya zaro wayarsa ya danna wayar Hurairah ringing biyu ya d'auka
"Twin ya akai?" Jingina jikinsa yae da kujerar dayake kai
"Seka gudu baka nema na sam, narasa meke d'auken hankalin ka kwata kwata" murmushi yae
"Kayi hakuri Twin, zanzo ma gida yanzu idan kana nan" shafar sumar kansa yae zuwa bayan k'eya
"Ina gidan kazo da sauri" murmushi yae kurin ya ajiye wayar, tunanin Lawuri yana damunshi soyake tazo sui hira, dukda yaren kurame suke amma yafi buk'atar yin hira da ita fiye da kowa a duniya.
***********
Dawood kam mahaifiyarshi ta gama k'ank'ame abunta a gida, ta tsorata sosai da Lamarin daya faru, yauma kamar kullum zaune yake yana cin abincin sa cikin nishad'i suna hira da mahaifiyarsa, kallon sosai ya mata yace
"Momy yaran nan damukazo dasu aina gaya miki yaren mu d'aya ko? Banbancin kad'anne kawai" murmushi tae
"Yarena dai, kokabar hausan na Baban ka kuma?" Cikin raha yace
"Auu hakane yarenki mom sorry, ni inaso su shiga hasken musulunci wlhy, gashi narigada na had'a alk'awarin aure da Cyama dabadan hakan ba daba abinda ze hanani aurarta in musuluntar da ita" kallon mamaki tae masa
"Amma wasa kake ko? Ina haukane dazan barka ka auri er jeji, beside kai waye dazaka b'ata mu'amalan gidan nan dana gidan General? Cyama duk halaccin datama?" Sadda kanshi yae a k'asa cikin damuwa
"Mom nifa bance haka bafa, nace daze yiyu kawai ko?" Harara ta wurga masa
"To baze yiyu ba kaji na gayan maka, har abada wlhy, kamazo da salon raini" bece komai yasan halin mom, akan Cyama seya nemi d'aga masa hankalinsa gwara yae shiru kurun.
************
Yau tun 12:noon ya tashi daga office, beko lek'a ofishin Cyama ba ya wuce kanshi tsaye gidansu, yasan yanzu har mom tana gun aiki bakowa agidan nasu, A parlor gidan ya zauna sunata kwasar hira shida Lawuri, taji dad'in ganinsa har take masa bayanin Abu Huraira ya kaita wurin koyon hausa, kuma tana ganewa sosai ba kad'an ba, dan yanzu hartasan gaisuwa ma da wasu abubuwan yaren ba wahala sedai rubutu ne bata iyaba ko kad'an, anan take gaya mai rayuwar su akwai dad'i ba'a wahala kaman su, itafa noma take dukda zamanta 'yar sarki amma anan bataga gona bama, to ina suke samo abinci da nama, tunda bataga suna fita farauta ba" Dariya sosai yae har yana rik'e ciki, nan take ya mata bayanin komai dangane da rayuwar birni an dad'e sosai da barin wannan yamayi mamaki da ace duk wayewa bata kai musu ba har yanzu, aranshi yace watak'il hakan baya rasa nasaba da tsafin su waze iya zuwa garin... Sunsha hira sosai se raha suke
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.