Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 1 of 40

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[01]

........"Goje ka saka mana menene haka wai?"
Uwaisu ya faÉ—a cike da jumuÉ—in yanda cacar yauÉ—in ke shiga masa zuciya.
Dular da take bakinsa ya kawar mai kauri anyi mata naɗin manya,banda tashin hayaƙi babu abinda yake,ga wata hula zungureriyah a kansa,ta fita daga cikin hayyacinta saboda bala'in dauɗar da tayi sosai. Gashin bakinsa duguza duguza kamar gazagi.
Cikin shaƙaƙƙiyar murya yafara magana,kana jinsa kaji tantiri ɗiban fari.
"Tsoho shin kana nan akan bakarka zakayi cacah dani,kasan fah ba'a wanyewa lafiyah,sannan idan nayi nasara ko ranka ne billahillaxi saika bani shi,babu abinda ya dameni,naga kuma da alama ko ƙwandala baka maganinta a jikinka"
Hantar cikin Uwaisu ta kaɗa da maganar goje,amma kuma ta wani bangaren yanajin ƙamshin samun nasara,musamman ganin yanda yataralakato asa iri ɗaya a hannunsa,gashi kuma bugu da ƙari goje yasaka shanunsa dayake kiwo jingina,idan ya cinye wasannan yana da shanu fah kenan sukutum.
Goce hular kansa yayi gefe É—aya tareda gyara zama akan buzun buga cacar,mutane maza da mata Æ´an duniya suna zaune kowa na harkar gabansa a wajen.
"Hhhhhh goje kenan ai tunda nake bantaba fara caca na tashi banƙare ba,ko a cini kona ci bana bata baya,gaba na bata bana tsoro kota mutu kokuma tayi rai,ai ninan uwaisu ɗan marka,dan caca muke rayuwa,caca da rufamana kuma da yaye mana bargon asiri,anci mana mutunci kuma an yabemu,a cikinta muka buɗi ido tun kai yana baƙi,gashi har yayi furfura bamu dainaba,dan haka babu jada baya shiga wasa yaro"
Uwaisu yagama faÉ—a cikeda gadara da kuma yarda da kai,abokinsa Manga sai kirari yake masa.
Shafa ƙeya goje yayi tareda rishe ido yana dariyar gefen baki,kana ganinsa kam kasan yaci dubu sai ceto.
Fara zarar katin yayi yana ajiyewa É—aya bayan É—aya har yagama ajiyesu a gaban uwaisu,babu musu kana kuma babu tada jijiyar wuya,kowa yaga wasan indai ya iya wasan yasan goje ya cinye wasan.
Fitar da kwarkwaron wiwi ɗin bakinsa yayi kana ya miƙawa uwaisu dafaffafen hannunsa gabansa.
"Tsoho rai kokuma dukiya,cikin É—aya dole zaka bada É—aya yanzunnan bakuma sai anjima ba,dan haka saika hanzarta"
Rawa jikin uwaisu yafara tamkar an jona masa lantarki,don ko ba'a faɗamasa ba daga ganin soyayyun idanun goje toh fah bazai taba haƙura ba sam.
Juyawa yayi ya kalli manga dayake gefensa,suna haÉ—a ido manga ya kalli wani gefen tamkar bai san Uwaisu na wajen ba.
Bai sare ba dai cikin razananniyar murya ya tambayi Manga.
"Manga yaka juya,domin Allah idan kanaga kuÉ—i a wajenka ka Taimakamin dashi,zan baka idan mukaje gida"
"Kai kaji wani zance a wajen Uwaisu inada kuÉ—inne zaka ganni anan ina hamma kaman wani É—an tsuntsu,sanin kanka ne a gabanka dai wancan satin nasaka injinnawa a caca aka cinyeshi,yanzu bana cass bana ass sai Ladi tagama abincin sana'arta take zubamin bayan tagama yimin tujara."
Duk maganar da suke goje yana jinsu bai motsaba,kana kuma bai ɗauke hannunsa daga miƙashi da yayi ba.
In ran uwaisu ana ganinsa toda kuwa ya sau fitsari a lokacin,gaba É—aya tunaninsa ya kulle,shin a ina zai samo kuÉ—i yabawa goje.
"Hehehe tsoho kenan,dan kaga ina maka dariya koh,to aradu da kake gani nan ba mutuncine dani ba,ko ka bani kuÉ—ina kwatankwacin kuÉ—in saniyar dana saka,wato dubu É—ari da hamsin,kokuma na tale ka nan wajen na sutale maka fatar jikinka,kuma banga É—an matar da zai iya hanani ba kaf garinnan,in kuma kana ganin wasa nake kada ka fito da kuÉ—innan yanzunnan"
Shuru uwaisu yayi yana muzurai,sai lalleƙawa yake yana rarraba ido ko zaiga wanda zai kwaceshi a hannun goje,amma babu alamar akwai wanda ya kulada mai suke a wajen.
"Wa kake kallo zatonka akwai mai ƙwatarka a wajennan ne heee,kanama bata lokacinka ne sannan kuma kai baka san dokar kuɗina ba ma,duk bayan minti uku idan ya ƙara toh zan ƙara dubu ɗaya akai,dan haka zaka bani kuɗina ko saina cire maka yatsu tukunna"
Yafaɗa yana ciro wata wuƙa ƙugunsa mai kaifi,har wani lashe baki yake kaman maye yaga nama.
Caraf ya canfki hannun Uwaisu yana shirin cire masa yatsu,wani ihu ya kurma tareda fara dadare,dama gashi da ƴar kibarsa ba ramamme bane kaman gojen,amma yanda ya riƙeshi yakasa kwacewa kasan goje bakaramin bushashshen ƙashi ne dashi ba.
"Wayyo wayyo do Allah ka ƙyaleni wlh zan baka kuɗinka amma kada ka ciremin hannaye,kafadamin bayan kuɗi mai kake so zan baka ka rufamin asiri"
Magana yake yana kururuwa mutane har an fara taruwa,amma kaman kurma yana nan rikeda hannun uwaisu,har yafara saka masa kaifi a hannun na wuƙa,dan dagaske yake haiƙan sai ya yanki hanunnan.
Taruwa akayi wasu na jan goje wasu kuma suna jan uwaisu daga hannunsa,banda huci babu abinda yake yana sake riƙo uwaisu,idanuwansa sun kaɗan sunyi jawur.

Ranar Uwaisu yaga hairazin kam,don yahada gumi shirkif ta ciki.
Cikin shaƙewar murya na mai taurin kai goje ya yunƙura tareda watsar da mutanen dake riƙe dashi,wawuro uwaisu yayi a karo na biyu tareda cewa.

"Ohh zatonku ina wasane,to duk wanda yafasa rabamun ma ya goya kura ba wando a cikinku,kuma duk mai son uwarsa da haifi wani kokuma ya kwana da pillown ƙasa bana matarsa ba to ya sake zuwa zai rabamu da wannan tsohon najadun"
Yana maganarne yana nuna dukkan mutanen wajen ɗaya bayan ɗaya da wuƙar hannunsa,ɗaya hannun kuma ya riƙe uwaisu camau baya ko motsin kirki,ko ya akayi ma yasamu wannan masifaffen ƙarfin oho.

"Kaikuma shin zaka bani ƙudina kokuma na karbi ranka yan........."

"Tsaya tsaya na baka ƴa ta Sumaimah a matsayin kuɗinka, dan Allah to ka ƙyaleni"

Shuru goje yayi yana zare ido kaman mai nazari,mutanen wajen sunyi mamaki da kuma sakarci irinna uwaisu,wanne irin abune zaisa uba ya dauki ƴar sukutum mai lafiya da kuma hankali yabawa mutum irin goje,hakan ma bata hanyar dadai ba wai fansar kansa yayi da ita a wajen caca. Saidai kuma ta wani wajen hankalinsu zai kwanta,dan da alama goje zai ƙyaleshi da ransa.

Bayan yagama nazarin É—agowa yayi da sauri kaman zaucacce tareda sake kallon uwaisun,saikuma ya buÉ—e baki yana jijjiga kai.
"Kai shashasha ka maidani dan kaga ina shaye shaye,a tunaninka ni marar hankaline,taya Æ´arka zata fanshi saniyata buleliya da ita ta kiwatu,ina kaita kasuwa kuÉ—i za'a bani,Æ´ar ka fah uban wa zai siyeta idan na karbeta,ko sadaki da masu aure ke bayarwa ma dubu ishirinne,saboda ka maidani bunsuru bari ka hadani da mace koh,na maka kama da wanda yahaÉ—a hulÉ—a da mata iyeee"

Wannan karon uwaisu kasa magana yayi,sai mutanen wajenne sukayi ta maza.
"Haba goje ba girmanka bane haka ai,tunda har yace zai auramaka ƴarsa a maimakon kuɗinka kayi haƙuri mana,ai mutum yafi kuɗi koh,kaga tunda innarka tafara tsufa basai tana yimuku girki bah?"
Wani a cikin mutanen wajen yafaÉ—a ta sigar lallashi,da alama kuma hakan yafara tasiri akan sa,dan yaÉ—an saki wuyan uwaisun ba kaman É—azu ba.
"Ehh kuma mutum kace wani abun,dama inna kuwa ƙafafunta suna ciwo,bata gama mana tuwo da wuri mutum sai yunwa taci ta cinye masa,saita samu mai mana girki,nizan wuce madakatarmu daga nan,ku wanketa ku kaita gidannamu gobe,idan kuma kasake wata rigimar tasake haɗamu.....hmmmm feɗeka zanyi na bawa su durwa,tsohon banza kawai,gobe ma kasake kasadar shiga caca babu kuɗi,idan ita sa'ar wasanka ce,gajaman kawai"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.