Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA.txt
Chapter 33 of 40
Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[25]
[Goje a mahangar gani].
A yanzu walwalarta da farincikin da take ciki yafi na lokacin baya.duk da koyaushe batada lokacin kanta.Kullum tana kan hanyar makaranta,ga kuma aikin gida wanda naga babu wanda ta tsaya dayi,amma babu alamar nuna sarewa fuskarta,da alama hakan shine ra'ayinta kuma burinta.
Gobe nake shirin sake komawa ƙungiyar BC sun nemeni wani aiki mai hatsarin gaske,mutane tarane kacal zasu tafi yin aikin,kuma ina ɗaya daga cikinsu. Haka kawai saina tsinci kaina ta rashin son barin gidan,bansan meyasa ba.
Yanzunnan shigowata gidan mun gama waya da Don3 sannan a wannan aikinne idan muka dawo zamu haÉ—u da Don2 kasancewar har yanzu sunansa kawai mukeji.
Wayace a hannuna ƙarama nokia,wacce zan dunga waya da su inna,duk da wani bangare na zuciyata yasan danna na dunga magana da Sumaimah ne. Haka kawai yanzu nakejin bana gajiya da ganin wannan fuskartata idan tana tsorona.
Gidan shuru kakeji da alama wannan gajin itada iyalanta basanan,sun samu gardama da mijinnata akan zuwansa wajen mata. Aikinsu kenan ai.
Kasancewar anyi isha a daki suke hirar,dan haka nima nan na shiga..
Sumaimah tana kwance akan ƙaramin gadon innan,itakuma tana tsakar gida da carbi a hannunta.
Karatu take a littafinta ta kunna fitila,wanda hakan yasaka hasken ya haska fuskarta..
Ban kalleta ba,itama iya sannu tayimin kawai,ƴar hira muka taba da inna kafin na ciro wayar na miƙa mata..
"Inna zanyi tafiyah irinna wancan karon,dan haka ga wannan ki riƙe saboda ko zamu dunga gaisawa"
"Ahah ahah kacan matarka ka bani,maza bata gatacan...idan gaisawar ce inka ƙira saita bani,amma ni ina zan iya wata waya"
Ɗagowa tayi da idonta jin maganar da ake,da tayi niyyar ɗauke kanta,amma ganin na miƙa mata wayar yasa ta taso ta karba da hannu bibbiyu.
"Nagode"
"Toh inna ni zan tafi ko ya ake ciki duk zan sanar daku"
Fitowa nayi daga ɗakin na nufi nawa,kayan aikin nagama shiryawa a jaka,kana na saƙalota.
Ina cikin kulle É—akin naji takun Sumaimah a bayana.
Hannayenta a saƙale suke a bayanta,tanayimin kallon mamak,na gane hakanne saboda farin watan daya haske wajen.
"Wajen fashinnan zakaje?"
Muryarta tana rawa tayi maganar,haka kawai na tsinci kaina da kasa bata amsar tambayartata,komai yasa oho.
"Shin dolene sai kaje,kasan fah babu kyau hakan bai dace ba,inda zakaje ka tarwatsa suma sunada iyalai,ko ya kabamu zai ishemu basai ka É—ebo da yawa ba wanda ba naka ba"
Matsawa kusada ita nayi na miƙa mata makullin hannuna,har a zuciyata nasan zancenta gaskiya ne,amma bashine abinda zuciyata takeso ba.
"Ki kulada inna,akwai number Tunga a ciki,ki ƙirashi in kuna son wani abun,aikin dazanje wannan karon yanada hatsari,dan haka idan ban dawo ba harkika gama karatunki,to kiyi rayuwarki yadda ya dace tun farko takasance"
Hannuna naji ta riƙe tareda makullin,jijjiga kai take wannan karon ta kasa cewa komai,shin yaushe kusanci yashiga tsakanina da itah bansani ba..
Zare hannuna nayi tareda yin hanyar waje ina saƙale da zakata. Can ƙasa ƙasa najiyo ƙaramar muryarta ina shirin fita daga gidan.
"Ka kulada kanka,zamu jiraka harka dawo"
Runtse idona nayi,bantaba jin irin wannan yanayin idan zan bar gidaba sai yau,wanne irin abune yake shirin faruwa danine. Koma menene kawar dashi nayi na maida hankalina ga aikin dayake gabana,wannan ne aikina na ƙarshe daga nan zan zama shugaba a bangarena,zasu bani kayan aiki da komai danake buƙata.
Kaman koyaushe baƙar motar da take ɗaukata ce ta tsayah,ina shiga kuwa taja zuwa cikin dajin.
Kwananmu uku muna training da shirye shiryen yanda wanann harin zai kasance,tun daga sannan na gane wannan dabanne da sauran aikin danayi da ƙungiyar.
Sai a kwana na ukun aka taramu domin faÉ—amana abinda zamu je yi.Kuma yauÉ—inne zamu tafi.
Mu tarane kaman yanda suka faÉ—a a tsakiyar filin.
Don 2 Ne a zauna kan kujera,kaman koyaushe sanye yake da suit baƙaƙe,yafara manyanta amma kana ganinsa kaga tantiri,ya runa gashin kansa gefe gefe fari,sai tsakiyar kuma ja.
"Barka da wannan lokaci ya gwarazan jarumanmu,a yau zamu faÉ—amuku menene abin harinmu a wannan aikin,sannan in mun gama bayani zaku hau jirgi zuwa babban sansaninmu na garin abuja.
Munason Sace Bayanan Nuclear da za'a kawo ƙasarnan a ranar 23 ga watannan,wato nanda sati biyu kenan.Wannan kundin yanada matuƙar muhimmanci,kuma za'a kawoshi cikin tsaro sosai. Zaku sake samun horo a wajen babban member ɗinmu na can,shine mai kulada harkar hacking da gano mai ke Iya zuwa ya dawo. Kuma shine zaija ragamar shirin a can,ku naku aikin shine abin abinda yace.
Ina fatan kun fahimta"
Dukka a tare aka bashi amsa bandani,dan haka kawai bansan meyasa ba yake bani haushi,kuma nake jinsa kaman na sanshi.
"Wannan aikin yanada hatsarin gaske,wanda ya samu nasarar dawowa za'a bashi maƙudan kuɗaɗe,sannan a lokacinne zaku haɗu da Don1 kafin kuma shugaban ƙungiyar,wannan shugabana ne zai faɗamuku mai zakuyi ya haɗaku da shugaban wannan ƙungiyar"
Hmmm dama nasan za'a rina,aikin gamu kashemu zasu turamu,bakomai dama kasada gaba muka bata ba bayaba,sannan zuciyata bata rayamin tsayawa daga haka tunda na riga na fara.
Ƙarar sauƙar helicoper muka faraji,hakan yasa muka shirya domin tafiyah.
Layi muka yi zuwa wajen jirage guda biyu wanda suke ta diri,toh satar ma a jirgi za'a je kenan,kai kaga sata mai aji.
Announcement aka fara bayarwa bayan mun shiga cikin jirgin.
"Daga nan zamu tafi secret domain ne dayake cikin abuja,anan zamu zauna na tsawon sati guda mu Shirya komai kafin target É—inmu ya iso"
Yana gama faɗan hakan aka rufe ƙofar jirgin muka tashi sama,belt naja na saka a kunkumina,abinne yabani mamaki,taya akayi nasan inda belt ɗin yake,sannan na gefena sai diriricewa suke suna rirriƙe duk inda hannunsu yakai lokacin da jirgin zai tashi,amma ni banji komai ba,ji nake kaman na saba ma da shiga jirgin,mai yake faruwa ne?.
Tafiyah muke tayi a saman,har muka iso inda jirgin zai sauƙa.wani gidane daga waje iya rufune,amma muna shiga naga ashe a can ƙasa aka yi ginin.
Wajen ya ƙawatu matuƙa,idan ba naga lokacin da muka shigo ba,bazan taba yarda cewar a ƙasa wajen yake ba,gashi tarau tarau duk da hasken da wajen yayi kaman da rana.
Dukkanmu kowa ɗakinsa daban aka bashi da kuma duk wasu abubuwa dazai buƙata,sanann duk safiya zamu dunga fitah training da yanda zamu tsira idan jamian tsaro sun taremu. Nidai banajin abinda suke cewa ina sai zuwa gobe,tunda suka nunamin ɗakina nashiga nayi wanka,wai goje zayyi wankan arziƙi kenan bana sabulu ɗan yanka ba.
NafaÉ—a a raina ina murmushi,tsuke fuska nayi tareda É—an ja da baya a gaban madubin ina kallon fuskata,wai ba dole ma a dunga gudu idan an ganni,haka Sumaimah take kallona ashe??.
Kaya Nagani a cikin ƙaramar drawer,bayan nasaka ina fitowa naga dukka sauran suma irin nawane kayansu.
Bayani aka farayi yanda tsarin sace abun zai kasance,sai koyon harbi da kuma juriya. Shi mukayi ta koya har ranar 23 ga watan tazo ta.
Tofah abin yazo inji mai tsoron wanka,cikin daren yau zamu kai farmaki babban gidan tsaron a nan abujan mu É—auko bayanan wanda yake a wajen da aka killace shi.
Bindigogi aka bamu manyan manya cikeda bullet ɗinsu,kai dolema wannan ƙungiyar tanada saka hannu wani babba,in ba haka ba taya zasu samu irin waɗannan makaman haka.
Ta wata ƙofa muka shiga ta sirri wacce tabi ta cikin ƙasa,har muka shiga cikin ginin a haka.
Nidai abinma kaman film haka naganshi.
Tafiyah muke babu wata matsala a nawa rukunin da nake ja har muka isa É—akin da bayanan suke ciki.
An ce mana bayanai ne,amma ni ban yadda da hakan ba,in bayanai meyasa baza'a turo ta na'urar sadarwa ba. Sannan kuma abin yayi matuƙar bani mamaki,ganin har mukai ga ɗakin da akwatin yake amma kuma babu kowa a cikin ginin.
Hasalima ƙofar da abun yake a buɗe take.
Wani abokin tafiyarmu ne ya tafi gafa gafa zai ɗauki akwatin,har zan hanashi sai naji ɗakin yafara wata ƙara,wutar wajen takoma ja mai walwali,shikuma wanda yaje kusada akwatin dake shoking ya daskararshi..
Ƙarar taku na tahowar jami'an tsaro mukaji,ga ƙofar ta kulle baza'a fitaba saidai a shigo.
Munanan mutane da yawa cikin kaya na sojoji suka fara shigowa,suna harbi muma munayi,kafin wani lokaci anyi raga raga da É—akin,sojojin da mutanen mu sun ji rauni wasu kuma sun mutu.
Idona ne ya kai kan akwatin,wanda a garin harbi aka jajjage na'urar rezar wajen.
Cikin zafin nama na fizgeshi nayi wani window da gudu,wajen kusan hawa uku ne,ina faÉ—awa nafara gudu,naji alamar faÉ—owar wani ya biyoni,duk da buguwar danayi amma bna tsayaba na cigaba da gudun.
Munyi ƴar tafiya kafin naji ya bangajeni. Akwatinne ya faɗi gefe muka fara faɗa nidashi,yanada ƙarfi sosai da alama sojane mai zafin nama.
Saidai nima na nunamasa nawa zafin damtsen,ganin nafara cin galaba akansa yasa nafara dan sararawa, Hular kansa na yage,saurayine fari,na shagala da kallon fuskartasa wacce takemin kamada ta wani naji wani zafi ya ziyarci cikina. A hankali nakai idona wajen,inda ya cokamin wata wuƙa a ciki,hakan bai isheshi ba saida ya jata yayimin mummunan rauni,dishi nake gani a haka ya samu nasarar cire min nima hulata,zaro ido kawai naga yayi yana shirin magana,kafin yace wani abun wata mata sanye da baƙaƙen kaya ta buga masa ƙasan bindiga akansa. Tare ni dashi muka zube a wajen,na saddakar tawa ta ƙare kawai. Ina jin lokacin da jinina yake fita daga jikina.
BuÉ—e idona nayi naganni a cikin wani kogo wanda yayimin kama da wanda nasani,wato na garinmu.
To waye ya kawoni nan wajen? Nayiwa kaina wannan tambayar.Yunƙurawa nayi zan tashi,wani azababben raɗaɗi ya jiyarci inda sojan ya soka min wuƙa. Kai sai yanzu ma na tuna kenan komai ya faru a gaske kenan.
Idona nakai kan cikinnawa wanda aka naÉ—eminshi da farin bandeji,gefe kuma audugane wanda akayi ta goge jinin wajen.
Koƙartawa nayi na zauna ina haki na wahala,wata takarda nagani na gefena an naɗeta an ajiye.
ÆŠauka nayi duk da dishi dishin danake gani nafara karantawa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.