Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 28 of 40

___***___

[Sumaimah a mahangar gani]

Yau kimanin kwana uku kenan da kaini asibiti da goje yayi,abubuwa da dama sun faru,ciki harda samun sauƙi danayi na hannuna,bana komai a gidan saidai nayi wanka na kwanta. Abinci kuwa kullum sau uku goje yake kawomin a rana,kuma dukka mai daɗi da rai da lafiyah,shikansa na kula shigarsa ta sanja ba kaman ta da ba,yayi kaya da yawa kala kala,mashinɗin daya kaini asibiti dashi ma ashe nasa ne,koda yake siyasa ta zo ai dole su samu kuɗi.
Hannayena sun warke sai sa'ba da sukeyi,kasancewar maganin mai tsada ne da kuma kyau.
A bangaren su gaji kuwa ko kallon rashin arziƙi basa yimin,saboda mungun gargaɗin da goje yayi musu,kullum da safe zan jisu suna faɗa akan wanke wanke,ko leƙasu banayi balle nasan mai sukeyi.
Yanzu ma a zaune nake ina kallon jikina,naƙara ɗan haske da kuma ƙiba,a iya kwana biyu kawai. Ashe dai hutu yanada daɗi,inaga tunda nayi wayo ban taba yin hutu kaman wannan ba.
Ledar dana gama cin indomie na É—auke da kuma kofin na fita da su.
Da gaji muka haÉ—a ido tana É—iban itace a wani fili dayake gefen É—akunan inna mairo.
Harara ta maka min amma batace ƙala ba,nima daga kallo ɗaya bansake kallonta ba na saka ledar a shara na wanke kofina.
Koba komai dai na huta da muguntarta koda na kwana uku ne,dan har yanzu ban daina tunanin wataƙila goje zai daina bani abinci idan na warke.
Tsintsiya na ɗauka na share ɗakin da kuma barandar,har zan tafi wata zuciyar tace da na gyarawa goje sashensa ai tunda na samu sauƙi.
Cikin kasada kuwa na nufi ƙofar tasa,tayi datti kam ba laifi,haka yake rayuwa a ciki,koda yake kanna zo ma ai haka yake,kuma dan ya kulada ni kwana biyu bashi yake saka cewa wai ya shiryu bane daga yanda yake wata zuciyar ta fadamin.
Randarsa kam a cike take da ruwa,kasancewar yanzu hamisu ne ƙanin kursiyyah mai wanann aikin.
Makullin daya bani kwanaki na saka na buÉ—e É—akin,hannu na saka ina kaÉ—e hancina,banda hamamin maza babu abinda É—akin yake.
Uhmm hali zanen dutse.
Na faɗa a raina,wangale windown ɗakin nayi dana ƙofar,kayansa daya zuzzubar a ƙasa na ɗebe na saka su a gefe.
Saidai na fara da gyara fasalin É—akin kafin na share shi,kayan daya 'bata kuma na fito dasu daga É—akin,shin zanyi iya wanki kuwa dana fito dasu.
Tunani nake hannuna a kunkumi ina kallonsu,duk da hannuna ya warke amma bai gama komawa daidai ba,idan nace zan murza kayan wanki toh sai koma baya.
"Dama waye yace kiyi aiki da kika tsaya kina tunani,ko shima salon gulamane kai kice bansan cinki ba ban san shanki ba,ballantana halin da kike ciki"
Zabura nayi na ɗan koma gefe,saboda na bashi damar shigs ɗaƙinnasa,danna tare bakin ƙofar,dama yana bayana tun ɗazu kenan?.
"Kayi haƙuri,kawai naga zan iyah shara ne shiyasa"
"Eh to kuma shi wanki da bazaki iyah ba sainace saikinyi koh?"
"Ahah ..uhmm...."
"ÆŠauresu ki sakasu gefe zan bayar a wanke,sannan kizo ki zauna akwai maganar da zamuyi"
Dumm naji kaina yayi,magana da goje? Uhm
ÆŠaure kayan nayi kaman yanda nace,kana naje gabansa na zauna,idon yana kallon tsakar É—aki,shikuma yana zaune a bakin katifa.
"Tunda yanzu kin warke saiki faÉ—amin dame dame kikeso na kayan abinci,kinsan dai bazan jure kullum in zan zubawa cikina abinci saina haÉ—o dake ba koh?"
ÆŠaga kai nayi alamar ehh,aikuwa naji wata tsawa kamar a sama.
"Nida kai nayi miki magana dabazaki buÉ—e bakinki ba,kodan nayi jinyarki saina zama abin wasanki kai?"
"Ahah kayi haƙuri,ehh na warke zan dunga girkin za'a iyah siyowa,itace ne saikuma kayan abinci,inda abubuwan aiki daban su tukunya"
Kaman mai aljanu jin abinda nace kuma sai ya maida muryarsa yanda take.
"Tom shikenan,zan aiko Tunga ya kawo in anjima,ba lallai yau na dawo ba,sannan inna tace na faɗamiki Yau zata dawo,munyi waya da ita da wayar ƙaninta"
Duk da a razane nake bansan lokacin da murmushi ya kubcemin ba.
"Dan Allah toh shikenan barinje na gyara mata ƙofar sosai"
Tashi nayi zan fitah da sauri,har na manta baice na tafi ba.
Saida naje bakin ƙofa naji maganar sa.
"Na sallameki ne?"
"Au ehh um toh"
Nafara shirin dawowa ina inda inda.
"Jeki kawai"
Yafaɗa yanayin wata ƙaramar tsuka.
Uhm kai kasani dai nafada ina yin sashennamu da saurina.

Bawani gyara ƙofar take buƙata ba,amma haka nasake gyarawa dai,saboda murnar dawowar innan.
Bayan na gama wanka nayi nasaka kayana na zaman gida.. Ina kwance har bacci ya É—aukeni.
Can kaman a mafarki nake jiyo sallamar mutum a baƙin ƙofar ɗakin.
Ɗan kwalina na ja na yafa na fito,himm naci karo da kaya a bakin ƙofar ɗakin.
Buhun shinkafah Æ´ar gwamnati,galon É—in manja dana mangyaÉ—a,katton É—in taliya ta leda,buhun gari na semo,macronni indomie harda su doyah da dankali.Sabon Risho a kwalinsa da kuma jarkar kananzir babba a ciki damm. Sabulai na wanke dana wanki masu kyau,harda macline.
Zare ido nayi ina dafe ƙirji,wannan kayan fah,wanene yayi batan kai ya shigo dasu haka?anyah bana gidan chairman bane ba kuwa.
Ina nan tsaye nayi suman tsaye tunda yashigo giɗan hannunsa riƙeda jakakkuna guda biyu,wani yaro ma yana biyeda shi da wata leda a hannunsa.
Dariyah Tunga ya tuntsire da itah ganin na ƙamekam kaman wata soja.
"Matar ogah wannan kallon fah,ogah yacemin dama kunyi maganar dashi ina,kan cewar za'a kawo. Ga wannan jakakkunan É—aya naki ne É—aya kuma na inna,wanann kuma wai ki soya shi ku dunga miyah dashi"
Jakakkunan na bi da kallo,sannan kuma da ledar da yaron ya miƙamin.
Har sannan ko ƙala ban ce ba,wasu kuɗaɗe yasake ƙirgowa ya miƙomin,hannu yana rawa na karba inaso naji su kuma na menene.
"Wannan kuma yace ki riƙe ki sayi abinda kikaga babu,in sun ƙare kiyi masa magana,ga yaronan zai dunga shigowa yana miki aika,inya kama sai ku dunga bashi abinci. Idan babu wani abin ni zan tafi"
"Ba.....bbbu komai ammmm....mmma kuwa ba mafarki nake ba?"
"Wanne mafarki ba mafarki,namune yake shirin hawa mulki,da kuma sabon ainkin ogah da yayi shima suka biyashi da tsoka,muma yanzu mun daina satar kajin mutane,gwangwajewa muke da daɗi,muma muka ci bareke matar ogah,ai ki sake jansa a jiki ki lashi arziƙi tunda Allah yakawoki a daidai sanda yayi kuɗi,dama ku kuke ganinsa kaman mungu,amma oga goje ai akwai kyauta,saidai in bata biyo ta kanka ba baya tunawa da shafinka. Inkika bi a sannu zaki gane kansa,kuma zakiji daɗin zama dashi,sannan akwai abu ɗaya danake son kiyi a rayuwarsa,in lokacin yazo da kanki zaki tambaya kuma nayi alƙwarin zan sanar dake.....zo mu tafi Yusuf"
YafaÉ—awa yaron suka fitah waje bayan sun barni a duhu tsulum da bayyanar tasu.
Ledar da take hannuna na buɗe,kaji ne Yankakku an gyarasu tass. Samun waje nayi na ajiyesu tareda ƙirga kuɗin dayake hannuna,dubu ashirinne ciff.
Komawa É—aki nayi na ajiye kuÉ—in da jakakkunan danaji kaman kayane a ciki.
Sauran kayan ma duk É—akin na kaisu na ajiye,da nayi niyyar kaisu É—aya É—akin inna ne wanda babu komai a ciki,saikuma na tuna akwai masu halin bera a gidan sosai,karsu yi É—an halin irin wanda sukamin a kuÉ—ina.
Babu abinda zan taba sai inna ta dawo,ko wanne lokaci nasna zata iya dawowa a yau É—in.
Dan har yanzu ban yarda Tunga da gaske yake gojene ya aikoshi ba tabbb wayaga duniya sabuwa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.