Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 3 of 40

"Ammi wlh kasheni zayyi in kuka kaini wajensa,wayyo nikam tawa ta ƙare wlh dana sani ba dana amince da Bashir dayazo neman aurena wansan shekarar,duk tsiya gwanda mai neman mata da mahaukaci wlh,wanda a kowanne lokaci zai iya kasheka"
Hannunta Ammi ta jawo ta rike cikin nata,saida ta tattara nutsuwarta kafin tafara cewa.
"Kiyi shuru haka Sumaimah,Inshaallah bazai kasheki ba,Allah ma zai kawo rabuwarku dashi kina zaune,dan kame kanki da kikayi da kuma Addu'arki bazata sauƙa kasi a banza ba,dan haka ki kwantar da hankalinki kinji."
Suna nan zaune Uwaisu ya shigo ƙofar tareda bankaɗa kyauren ɗakin,rarraba ido yafarayi akan su kamar marar gaskiya,ganin basu ɗaga ido sun kalleshi ba yasa yace.
"Ke amminki ta faɗamiki mai yake faruwa koh,da gobe zanmiki aure tunda ƙinki kawo miji,amma yanzu shi yaron innarsa tace a bari sai wani satin,dan haka ki shirya nan da wani satin zan miki aure"
Cikin É—aga murya da borin kunya yake maganar,daga ammi har Sumaimah babu wanda ya tanka masa har yayi ya gama.
Har ya saki labulen sai kuma yaƙara buɗewa.
"Yawwa Ammin yara ni akwai abincinnan ne,É—azu ina waje naga Sumaimah tashigo da botikin da sauran abinci bata sayar ba to koh......."
"Babu na yara ne,yau banyi dakai ba"
Tafaɗa a daƙile cikin fushi,duk da Sumaimah ba ƴar ta bace amma abin yabata haushi sosai,duk abinda akewa Sumaimah a gidan bai wani dameta sosai ba indai ba ƴaƴanta aka taba ba,amma kuma na yau ya ƙona mata rai,musamman yanda tasan ƙoƙarinta da kuma son iliminta,yanzu duk yatashi a banza saboda rayuwar daza'a jefata.
Ita kanta Sumaimah abin yaso bata mamaki yanda ammin ta tsaya mata a wanann karon,kuma hakan yamata daɗi sosai,yau dai kam taji tanada uwa,duk da dama ba mugunta take mata ba tun tana ƙarama.
"Kaman ya yau babu nawa,wai dan wannan abin daya faru ne,laifina kika gani a ciki,so kike na barshi ya kasheni bayan inada abin bayarwa,ko kin manta Æ´a tace kuma ikona ce,duk kiwonta danayi tayi a gidan menene amfaninsa in bazata yimin rana ba uhm"
"Kiwonta,harkana da bakin cewa kai kayi kiwonta ma,to naji ikonka ce bance kuma ba ikonka bace,in abinda mutum yakeyi daÉ—ine ya cigaba dayi maza,batun abinci kuma nima ikona ne shi,sannan kuma wanda naga dama zan baiwa ina ko"
Daga yanda yaga take magana yasan ranta ya baci da abinda yayi,tabb inaga kuma Æ´ar ta yabayar,yasan ma bai isaba ai,Sumaimah dai itace karkatacciyar kukar tasa mai daÉ—in hawa.
Sakin labulen yayi yai waje yana kumbure kumbure kaman wani zaki.
Dama daga masallaci ya nufi cikin gidan,daga nan kuwa majalisarsu kai tsaye ya wuce.
Sallama yayi zauna a kusada Manga aka fara taÉ—in duniyah.
"Yadai Baban amarya naga kana tsuka"
"Uhm kaidai bari kawai,Deejah(ammi)ce ta É—auremin fuska tamau abinci ma ta hanani yau,wai dan saboda nabada auren Sumaimah"
"Ahhh to Æ´arta ce,ba ikonka bace,lamarin babu daÉ—i amma in sun kula kaima ai ba yanda zakayi ne,yau jimin mata da kilaroro.....amma dai Uwaisu zata daÉ—e bakaje gidan caca ba koh"
Manga ya faÉ—a dan yaji mai uwaisu zaice..
"Bazanje gidan caca ba? Akan me saboda wannan ƙaramin lamarin da mukayi da yaro,abinda yafi wannan ma ai yafaru munje ballantana kuma wannan,ai gobe ma banda ranar kasuwa ce zamuje sana'a da zuwa zanyi,amma ka taimayeni jibi zaka ganni"
Dariya Manga yayi kafin kuma yasake É—ago masa wani taÉ—in.
"Toh ya maganar kuma kayan É—aki dazakayiwa ita amaryar,kasan dai baka kaita haka ba ko"
"Saboda ni wani abun zai bani inna bashi ita komai,ai yanda take haka zata bishi babu abinda ya dameni,karka manta bazai bada sadaki ba fah kaman ko wanne,wannan kuÉ—i daya hau kaina shine sadakinta,kaga kuwa haka zan kaita,dan inba aman kuÉ—i zanyi ba to bana maganinsa daka ganni nan,innarsa da kuma ita deeja da take tada jijiyar wuya suyi ruwa sannan suyi tsaki,babu abinda ya dameni."
Yafada yana kaÉ—e rigarsa.

___***___

ÆŠaga cinyar kazar yayi a hannunsa yana juyawa,Taska ya kalla wanda yake ta aikin ciro gashashshen naman daga cikin wuta.
"Kai taska a ina kuka samo kaji nan"
"Uhm ogah goje a sansanin wani É—an fulani ne nan gefe da gari"
"Dama akwai kaji kuka gasa mana zomo jiyah,hadda cemin babu komai cikin garinnan banda waÉ—ancan karashiyoyin?"

Cikin bacin rai yayi maganar yana hararar taska,wanda yake mazari yana sunne kai. Al'adarsu ce dama a babbaka wuta a gasa kajin mutane da kuma awaiansu idan sunyi dare a waje basu koma gida ba,duk garin kowa yasan yaran goje da cinye dabbobin mutane,gashi babu wanda ya isa cewa kanzil,kaima da ana ci babbaka zasuyi su cinye. Yaran su samari masu tasowa duk ya maidasu yaransa sai abinda yace,wani abun takaicin kakai ƙara wajen sarki babu abinda za'ayi,dan in dukane ko ɗauri yanda kasan ka ɗaure itace haka zaka gani,shikansa sarkin ƴaƴansa uku duk yaransa ne,sai abinda yace shi zasuyi bana ubannasu ba,idan aka masa horo haka zai hanasu zuwa gida har tsawon wata guda,matansa haka zasu ɗaga masa hankali dole sai ya janye abinda yace.
A zaune yake akan wata kujera a tsakar dajin ta fatun awakin mutane,da ba shine shugaban dawar ba,wani mutum ne mungu baƙiƙƙirin dayazo daga sudan. Gabaɗaya duk ya takuramusu komai shi sai kansa,goje ko shekara biyar baiyyi da zuwa garin ba shida iyayensa.
Tunda farko dama bai É—auki rainin hankalin Damazau ba,shugabansu a lokacin.
Kullum cikin sa'insa suke,har goje yayi nasarar yanke maƙogaransa wata rana yazama shine sarkin dawar,shekara biyu baya. Abubuwa da dama sun faru lokacin,kowa a garin banda kama sunan goje babu abinda yake,matsi da takuri ya ƙara yawaita a cikin garin,yayinda su kuma yaransa suka fara fantama sunayin yanda suka ga dama,saboda yanda goje yabasu lasisin yin yanda ransu yake so a duk sanda sukaga dama.

Tura cinyar kazar yayi a bakinsa ya zuge tsokar kafin ya wullar da ƙashin.
"Shege dama yanada kazi bula bula haka muke cin zomaye,indai bayyi ƙara ba ku dunga ɗebo mana uku a kowacce rana,in yayi magana kuce yazo yasameni,ƴan kare da jajayen kunne sai suyita tara dabbobi yawun mutum yana cinƙewa in yagani,su basuci ba basu bawa mutum ba."
"Angama ogah goje,ai saima ka gansu da rai,manya manya fah,naji ance wai kawun Ragarus neh"
Yafaɗa yana kallon wani saurayin bafulatani a gefensa riƙe da kwari da baka a hannunsa.
"Ragarus kace dukiyarku ce muke shirin hawa kai,kaji nace bakwa ci koh,to yazanyi hakan kuke saika saka sorry fah"
"Ogah kenan ai bai daÉ—e da dawowa ba ne,dani kaina saina fi haka,dan a bayan kwanaki kam dole zan more"
"Sheege ɗan kawu,to tsugunna ka dangwali arziƙi"
"Ai ogah wani dangwalar arziƙin ma sai matar ogah tazo gida,zamuyi shagali"
Dariya suka saka da shewa,amma lokaci É—aya goje ya turbune fuska yana muzurai,wani kallon tsare rai yayiwa taska,har hakan yakasa sakashi haÉ—iye naman daya saka a baki.
"Taskaaah ka iya bakinka fah in kana son kwana da fatar bakinka,yaushe raini yafara shiga tsakani da har kake haɗani da mace, harda wani zakuyi shagali......hmmm ai naji haushi ɗazu,wai me yasaka ma ban cirewa wannan tsohon ƴan maraina bane,kamanni yayi caca dani bashi ko sisi,kuma har yana saka ran cinye saniyata wai,kutt Sailuba fah yakeson cinyewa wai a caca,kuma ma harda fansar saniyata da wata gajarabil ɗin ƴar sa,kai ya jawo mata ma aradu,zataci ƙaniyar tane muddin da taka gonata"
"Ayi haƙuri ogah bazai sake faruwa ba"
Taska yafaÉ—a yana sunkuyar dakai.
Jefah naman dayake hannunsa yayi kan ganyen dayake gabansa,tashi yayi daga kan kujerar tasa yana gyara zaman wandon jikinsa. Ta saman wutar ya tsallaka maimakon yabi ta gefe.
Bai waiwayo ya kallesu ba har ya ƙule cikin jejin.
Dukkan sauran yaran kowa taska ya kalla yana jiye masa.
"Kai taska wlh jagos ne,kalli fah yanda ka kunnashi,kasan fah yau ya juƙi hayaƙi dayawa a sama yake over. Da alama tunda ya nufi gidansa na cikin jeji to saita Allah kenan,ranar fah dana fishi gurnani naji yanayi a cikin ɗakin,anya kuwa ogah goje mutum ne kuwa?"
Dukkansu mai bayanin suka zuba ido,saboda jin abinda yafaÉ—a.
ÆŠaya daga cikinsu ne wanda tun É—azu bayyi magana ba yana gefe,wato Tunga,kuma shine na hannun daman goje,yafi sanin sirrinsa fiyeda su.
"Kai Ragarus kafiye fah surutu,da alama so kake yasaka shuru na har abada,kuma inna sakejin kana bibiyar sawunsa na abinda yake saina faɗa masa tamm. Mazaje mugama mu tafi gida,ogah nasan bazai dawo ba sai gobe,kunsan kuma munada ƴar tsamar da zamu buga da ƴan solo gobe,tunda sun ƙalubalance mu."
Dukkansu shuru sukayi da zancen,amma daga yanda Tunga yayi magana to akwai ƙamshin gaskiya a maganar Ragarus kenan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.