Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA.txt
Chapter 24 of 40
[Goje a mahangar gani]
Kwana goma kenan tunda muka tafi wajen aikin,fasa banki mukaje yi a gwagwalada,to bayan munyi da alama Æ´an sanda da sojoji sun sani da wuri,hakanne yasa aikin ya baci,aka kashe wasu daga cikinmu,wasu kuma aka kamasu. Mudai bamufi mu huÉ—u ba muka tsira a cikin mutum sha biyar .
Jeji muka furma da guda har sannan kuwa bamu jefar da kuÉ—in da muka É—ebo ba yana wajenmu.
A jejin muka buya tsawon wannan lokacin,saboda neman da jami'an tsaro suke mana.
Munsha baƙar wuyah muka dawo sansanin ƙungiyar.
Masu jiran ƙofar ne suka buɗe mana muka shiga,bayan sun gama bincike mu tukunna.
A gajiye muka wuce inda ogan yake muka jefa masa jakunkunan kuÉ—in.
Saida ya ƙaremana kallo saikuma ya tuntsire da dariyah yana nuna mu da hannu.
Yayi kaman daƙiƙa biyar yana wannan dariyah kana kuma yayi shuru yana goge hawayen da dariyar ta sakashi.
"Ku kalleku sai kace birirrika,da kyau da kyau,ni banyi zaton ma zaku tsira ba wlh,danaga baku dawo ba inace na kasheku ne"
Numfashina sama sama yakeyi saboda baƙinciki,yayinda zuciyata ke rayamin na kasheshi kawai ya daina numfashi. Saidai haka na danni zuciyata nayi masa tambaya.
"Meyasa kake tunanin zamu mutu?"
"Saboda nina ƙira ƴan sanda da sojoji na faɗamusu zakuzo yin fashi a banki. To ya kaji toh,duk lokacin dana ɗebi sabin yara haka nakeyi musu,tahaka nake gwada jarumtar su,shiyasa bamuda mutane dayawa sai jarumai. Ya kaji salo.........."
Tun kafin ya gama maganar nakai masa wani farmaki,fitt na so yanke maƙogaransa,saidai dayake ya san dabarun faɗa yagoce da sauri na sameshi a jijiyoyin wuyan sa na dama.
Ihu yasaka yana dafe wajen,yayinda jini yafara tsartuwa yana wanke rigar jikinsa..
Yaran dazuke wajen da gudu suka ɗaukeshi zuwa wani wajen da bansan inane ba,yayinda nikuma wasu suka rirriƙeni zuwa wani ɗaki mai kama da prison.
Idona a tsaye yake gamm babu alamar tsoro ko kuma nadamar abinda nayi masa,hasalima takaici naji da ban yanke maƙogaronsa ba.
Ina nan a cikin cell É—in har tsawon kwana uku,waÉ—anda suka kawoni wajenne suka fito dani.
Kaya suka miƙomin iri ɗayah da wanda ogan yake sakawa,cikin girmamawa suka miƙamin kayan tareda yimin alamun na biyosu.
Wani É—aki suka nunamin nashiga,akwai gado a ciki da kuma banÉ—aki,ba laifi yayi kyau kam.
Wanka nayi na wanke wannan É—auÉ—ar jejin,duk da ma ni ba gwanin tsafta ba,amma naji daÉ—i sosai.
Kayan da suka bani na saka kana na fito.
Cigaba da sakeyi da binsu har mukazo wajenda aka taramu da farko.
Maimakon ogannmu yanzu wani mutumine sanye a suit akan kujerar.
Bashida suffar ƙarfi amma kuma yana da suffar sanin duniya akan fuskarsa,sannan kuma kana ganinsa kasan kuɗi ya zauna masa.
Murmushi yayi kana ya min alamar na matso,ba musu kuwa cikin nima nuna isata na ƙarisa wajen.
"Goje kake da suna koh? Ka burgeni sosai ka burgeni da jarumtar daka nuna jiyah,wanda hakan yasa na baka matsayinsa,shiyasa ka ganka da waÉ—annan kayan. Saidai ba tsallen da kayi ya kawoka tabb da rijiyah,idan ka sa ke yin wani to zaka jika a ciki tsundummm,wanda zaka iya yin dubu baka fito ba.
Nine shugaba na ukun da ake cewa zaku haÉ—u dashi in kuka tsallake aikin farko,a samana akwai shugabanni biyu,ni nabiyun nasani bansan na farkon ba,shigaba na biyune yasan wanene na uku. Dan haka barkanka da zamowa na hannun damana"
Tafi yafara yayinda sauran Æ´an kungiyar ma suka fara,lallai wajennan akwai haÉ—ari,jiya na lahanta shugabansu har sun maidani a matsayinsa??.
Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[19]
Gyara tsayuwa ta nayi bayan sun gama tafin.
"To nagode shugaba da wannan karramawar,amma batun rijiya ni dama dana so yin tsalle ba nufina zuwa wajen rijiyah ba,kaine ka kaini wajen rijiyar,dan haka yin tsallena na faÉ—a rijiyar ma duk yana wajenka. Mun tafi akan zamuyi sati É—aya,gashi munyi sati biyu bamu koma gidaba"
"Karka damu da wannan zaku kowa zai iya tafiya gidansu,aikinnan ya gamu saurna kuma nagaba idan yataso.
KuÉ—in da kuka samu nasarar É—akkowa kungiya bazata karba ba an bakushi ku raba,su É—au kashi É—aÉ—É—aya su baka kashi biyu."
Naji daÉ—in kuÉ—in tunda dama abinda yakawoni kenan ,amma nayi mamaki da banjisu a cikin raina sosai ba.
Mota DON3 É—in yabani kyauta,saidai nace masa banaso,danna kula a É—an tsorace yake dani karna yi masa tawaye kaman oganmu,amma ni bashine a gabana ba sam,so nake naje naga wacce wainar su Tunga suke toyawa.
Madadin haka wani na ɗauka a mutane wajen ya tuƙoni zuwa garinna mu wanda yake district ɗin gwagwaladanne.
Da daddare na iso,ban wuce gidaba sai kawai na nufi madakatarmu,babu kowa dan haka kai tsaye É—akina dayake cikin jejin na nufah.
Jakar kuÉ—in na ajiye kawai nayi kwanciyata,saboda narama baccin wahalar da banyi ba kwana da kwanaki.
Hasken ranar daya hudo ta rufin ɗakinne ya haske ido na,wanda hakan yasakani yin miƙa na tashi na zauna.
Fitowa nayi daga cikin bukkar na nufi kogi,wanda yake a É—an gangare idan mutum yayi Æ´ar tafiyah.
Wanka nayi kana nayi alwala,salloli biyu ake bina,isha asuba da kuma azahar wacce akayi yanzu..
Ina cikin yin sallahr Tunga ya shigo bukkar,ganin ina sallah yasa ya tafi.Nasan abinci zaije ya kawomin.
Bayan na gama jakar kuÉ—in danazo da itah na buÉ—e buzun dayake tsakiyar É—akin,kuÉ—in na zuba a ciki sauran kuma na barsu a jakar.
Jakar kayan aikina ma bazan koma da itah gidaba duk anan zan barsu.
Shigowa yayi yana cikin rarraba kuɗin a kan buzu,kallo ɗaya yayi musu ya kawar idonsa tareda miƙamin kwanon abincin daya riƙo.
"Ogah ga abinci,ka dawo kuma babu magana sai kawai naganka a jeji"
"Kamawa tayine,a gajiye nake shiyasa banshiga garinnan ku ba,ya aikin dana barku dashi ya tafi?"
"Yatafi yanda ake so,kawaidai kuÉ—inne bai bamuba,ana wannan matsalar sanjin kuÉ—in"
"Ga wannan ka bi kan kowa da rabonsa,ni barina wuce gida na sanja kaya"
Kuɗin na miƙa masa dami masu yawa,cikin fara'ah da washe baki kuwa ya karba.
"Ogah ta samu kenan,shiyasa fah mukeyinka,inka samu kana yaga mana,ba kaman tsohon kwarkwaroncan ba daka gama dashi"
A ƙaramar jaka na saka sauran kuɗin wanda zanyi amfani dasu na fitoh.
Hanyar gida na nufah,kaman kullum kowa ya ganni sai ya sanja hanya.
Ina shiga ƙofar tawa na ganta kaca kaca,yanda na tafi haka na dawo na sameta babu abinda aka taba.
BuÉ—e É—akin nayi na shiga,shi da alamar anyi masa shara kaman sau É—aya dana tafi,cije baki nayi ina jijjiga kai,lallai ma yarinyar nan ta rainani.
Cire kayan jikina nayi na zubasu gefe.
Gajeren wandona da singlet nake nema,amma banga waÉ—anda nake son sakawar ba,nan na tuna su na cire lokacin dana tafi.
Fitowa nayi na nufi kewayen saniyata,tana kallona tafara jujjuyawa,gabanta ƙwaraff babu abinci ko kaɗan. Saidai kuma amma babu rama a jikinta,to yaushe kenan take bata abinci,kodai ba ta bata kai?.
Ƙofar innan nashiga a zuciye,mai zan gani kaya nagani a cikin bokiti an jiƙasu. Kuma indai ba gizo idanuna yakeminba kayana nagani a jiƙe a cikin bokiti,wannan kuma wanne wari suke fitarwa haka.
Nasan dai kayana duk dattinsi bazasuyi wannan warin ba.
Dan takaici bansan lokacin dana bankaÉ—a labulen É—akin innan ba na shiga.
A kwance take sai sharar bacci take hankalinta kwance,wani cije baki nayi tareda runtse ido,zuciya ta tafarfasa take,yayinda ƙwaƙwalwata ke kwaranyomin wanne nau'in hukuncin dazanyi mata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.