Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 2 of 40

Haka yagama yiwa Uwaisu tass yashuri wasu takalmin fatarsa yabar wajen yana bobboƙarewa kaman wani mutumin itace. Sudai kowa na wajen ajiyar zuciya yayi,komai yasaka Uwaisu ma yin caca da wannan oho,mutumin da sai yayi wata churr a jeji ba'a ganshi ba idan suka iyo sata ko fashi.
Kowa a wajen masu cewa Allah yakara sunfi yawa,yayinda wasu kuma tausayin Sumaimah sukeyi,baiwar Allah tana ganin rayuwa ta wani irin uba da Allah yahaɗasu dashi,abin takaicin dama sauran yaranne aka bawa gojen da sauƙi,amma Sumaimah ya mahaifiyarta zataji,ita kadai ce kaff cikin yayansa ta fitada zakkah na hankali. Kodan yasan ita ba uwarta a gidan,in badan haka ba taya zai fara wannan abun.
Bagazan bagazan babu kunya bare nadama Uwaisu ya shuri shima nasa takalman yana baza uwar riga yayi hanyar gida,lokacin cin abinci yayi,zaije duk wacce takeda girki tagama yimasa tujara ta zuba masa.

_***_

Leƙawa tayi ganin yamma tayi sosai yasa tafara tattara robobinta na abincinta duk da kuwa bata siyar ba da sauran, dama hakan yakasance al'adar ta ne,bata yarda koda wasa tayi dare a wajen siyarda abincin,yau shakararta ɗaya kenan da fara tallen,tunda akayi auren ƙanwarta Shaheedah itace takeyi yanzu,lokacin da tanaji tana gani tabar karatunta tafara talle tayi kuka sosai da sosai,saidai kuma shin ya zatayi ne,idan bataje tallenba wanene zai bata abinci taci a gidan,ammi ce dama kaff cikin matar mai ɗan dama dama,itace kuma take riƙe da ita,taji daɗi ma da bata gaji da ita ba ai. Sa'arta ɗaya bata tsangwamarta amma kuma bata sakata a zuciyarta kaman sauran ƴaƴan nata. Hmmm wannan jinkirin aurennata yana damunta sosai.
A yanda aka san yanayin dai wacce taƙi kama kanta itace bata auruwa,amma ita kuma anata kaddarar kama kanta da tayi tafita zakkah a cikin gidannasu shine ya hanata auruwa.
Sallama tayiwa abokan tallennata wanda sukam yanzu ma suka fara siyarda abincin,dukkan su ƙannen bayanta ne sosai da sosai. Saboda kowa cewa yake ta rako mata tayi kwantai,amma kuma tasan hakan baya wuce nasaba da tuggun dasu inna lami ke yimata a gida,kasancewar tafi sauran yaransu kyau da kuma soyuwa a wajen kakarsu wacce ta rasu waccar shekarar.
Tafiya take da tunani fal a ranta,haka kawai takejin faɗuwar gaba wacce tarasa dalilin faruwar hakan. Botikin shinkafane akan ta saikuma na miya hannunta ɗaya,gefen kunkiminta kuma ta saƙale bahon data zuba plate da cokala a ciki.
Tazo daidai saitin anguwarsu taji yara sunayi mata magana,amma kuma yafi kama da tsokana,tohh ita kuma ba mahaukaciya ba kai yakawo haka,ko duk rashin aurennata da wuri ne yazamo haka.
Waiwayawa tayi ta kallesu,ba wasu yara bane ƙanana da hankalinsu sarai.
"Yee ga matar goje nan tadawo,ohh kowa yaki aurenta sai goje,shima biyansa kuÉ—in cacarsa akayi da ita wooo"
Gabanta ne yayi dummm,wannan karon har yafi wanda takeji ɗazu,duk da bazata ce ta gaskata maganar tasu ba,amma kuma tasan hakan abune da zai iyah faruwa,tunda ita kanta tasan halin ubannata,babu wanda bai masa shedar caca ba,hattah kayan ɗakunan iyayensu duk ya ƙararsu a cacah,sunyi kukan sunyi bakin cikin harsun gaji,babu ma ya ita Kaman duk abin ya fi damunta.
Cikin sanyin jiki kaman babu laka a jikinta taahiga zauren gidannsu,gidane na iyaye da kakannu mai ɗauke da ƙofofi da dama,dan su kansu ma sunkusa su talatin yayan vabannasu,banda ƙannen babanta da kuma ƙannensa da kofofinsu.
A gidannsu akwai tsakar gida mai matsakaicin faÉ—i,duk anan kowa ke fitowa dashi da yaransa yayi harkarsa.
Tana shiga gidan da idanuwa barkatai tayi arba dukka sun watso mata shi,kana gani dai kasan wani abun tabbas yafaru ko kuma yana faruwa.
Sauƙe idanuwanta tayi tai ta maza ta wuce ta gabannsu zuwa ƙofarsu,dan tunda taga dukkan matan a wajen iya amminta ce bata nan,kuma dama itace mace ɗaya a gidan da bata shiga harkar mutanen gidan sosai,badan bataso ba saidan hakan ba halinta bane.tasan duk yanda akayi tana ɗakinta dan haka can ta nufah. Tanajin ƙananan maganganu a cikin kunnenta daga bakunan ayarin matan wajen,amma tayi saurin toshesu a cikin kunnenta,dan a halin da takeji batada ƙwarin wannan zuciyar najin abinda suke faɗa ba yanzu badai tukun ko zataji ma.

Babu kowa a ƙofar tasu,dan haka kai tsaye ta ajiye shirgin hannunta ta nufi ɗakinnasu.
A durƙushe tasamu durƙushe ta ammin ta kifah kanta akan katifar da ita kaɗai ta rage a cikin ɗakin.
Ko ba'a faɗawa mutum ba yasan kuka takeyi na takaici da kuma baƙinciki.
Cikin rawar murya da duk wanda yajita yasan saida akayi jarumta wajen furtata Sumaimah tayi sallama a bakin É—akin.
Saurin É—agowa Ammi tayi tareda goge hawayen idanuwanta ta kalli Sumaimah É—in.
"Ohh har kindawo ne"
ÆŠaga mata kai tayi kafin itama ta jefeta da tata tambayar.
"Am...mmi ddd....dagskene baba ya badani ga goje a wajen cacah?"
Shuru ammi tayi tareda runtse idonta,shin taya zata bata wannan zazzafar amsar tayaya? Saidai kuma hakane dagaskene bazata iya cemata ba haka bane,dukda kuwa abinda zuciyarta keson faÉ—a kenan.
ÆŠaga mata kai tayi tareda saurin kawar da kanta,dan a yanda takeji duk da ba ita ta aikatawa Sumaimah hakan ba kunyar haÉ—a ido da ita takeji, ji take da tanada iko to zatayi koma menene wajen ganin hakan bata faru ba,saidai wacece ita,tayi magana a goranta mata kan cewar Æ´ar tace,kawai dan ta reneta.
Shuru Sumaimah tayi itama tana nata tunanin.
Wani abin ma Ita data kame kanta daga dukkan munanan ɗabi'u,yanda dan iska bazaizo yace yana sonta ba,to shikuma ɗan kirki koda yana sonta bazaizo ba saboda halayyar mahaifinta da kuma gidansu da bana mutunci ba. Wannan sai taji ma da kwanda tunda ta amince da wani sakaran ba wannan dodon da ake shirin ƙulla rayuwarta da tasa ba.

Siraran hawayene suka zubo daga kuncinta,bata taresu ba bata kuma tsaida su ba,barsu tayi lokacin su ne suyi ta zuba kawai dan in akwai wata ƙofar ma da wani hawayen zai zubo da ta barshi ya zubo........
"Kiyi haƙuri kawai Sumaimah,hakika banji daɗin abinda ya aikata ba,amma kuma banida tacewa akan hakan,dan har yanzu ma ni ban ganshi ba bare yamin bayanin abinda ya aikata,saboda yasan banida matsayin da dole saina sani ne inaga. Kije madafa abincinki yana can,barina yi sallah.

Kashh akan zamu dagata a sabon littafin na sanadin cacah.... Ya kukaji to kuna so?

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[02]

Duk da cewar tabi zancen ammin ta tashi ta É—auko abincin,ta daÉ—e tana rike dashi bata ajiye ba ballantana kuma tafara ci.
HaÉ—a ido sukayi da ammi wacce ta idar da sallah,itama ita take kallo. Maganar bata wuce ba koda yake sannan aka fara,maganganun da suke yimata yawo akai tafara fitarwa.
"Ammi amma meyasa baba zaimin haka,yanzu duk abinda yakeyi bai isaba sai ya wargaza rayuwata,meyasa saini ammi uhm. Kinsan kuwa ma wanene gojen koda yake waye kaf garinnan bai sanshi ba ma. Ammi kaman mahaukaci fah yake in kika ganshi,wlh ko lungun danaga yabi bana bi saboda tsoronsa,shine fah ya yankawa Ubaidu kafaÉ—a suna faÉ—an daba,ku.....kuma yanzu ace da wanann zan zauna a matsayin miji?"
Kuka ta rushe dashi tareda gyara zamanta a tsakar ɗakin,ta dade danayi ammi bata hanata ba,ina takeda ƙwarin gwiwar hanata kuka,itama kanta kukan take toh.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.