Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 36 of 40

___***___

"Me kikace abbanku ya dawo?"
Hajiya Maryam tafaÉ—a cikeda damuwa tana kallon fatee.
"Ehh mommy yanzunnan ya shigo gidan,naga ya nufi sashensa bai shigo cikin gidaba"
Tana cikin bayanin hajiya maryam tanufi sashennasa tana tafiyar karairaya kaman wata ƙaramar yarinya.
Ƙwanƙwasawa tayi,jin shuru ba'a amsaba yasa tasaka kai cikin ɗakin.
A tsaye yake a gaban window yana kallon lambun dayake bayan É—akinnasa,kana ganinsa kasan faÉ—awa yayi cikin zurfin tunani.
"Me yasamu wannan babban jarumin naganshi a haka,kaddai kacemin har yanzu baku samu inda barayin sukeba,kuma sun gudu da akwatin baku kamasu ba?"
Tafada kaman mai jin tausayinsa,amma kanaki kasan ta biyu take zancen.
Zan ajiyar zuciya A.M Aliyu yayi tareda cewa.
"Maryam,waishin yaushe zaki girma ki daina wannan abunne kam iyeee,Æ´aÆ´an ki ma bazasuyi abinda kikeyi ba,yanda kikeyi haka kikeso Æ´aÆ´an ki suje gidan mijinsu suyi ne? Ace tsawon sati guda ba nan ina office,duk akan wani abu daya shigemin duhu,amma daga dawowata babu magana mai daÉ—i sai ta izgili? Shiyasa fah banshiga gida ba bare ki ganni,amma saida kika biyoni kina murnar na faÉ—i koh ?"
"Uhm dagajin yanda kake magana baku kamasu ba da alama,kenan wannan akwatin dayake É—auke da bayanai masu hatsari yana hannun 'baya gari"
Juyowa yayi yana kallon hajiyah maryam,wacce take tsaye ta dan goce irin tsayuwar celebrity É—innan.
"Shin wai tukunnama taya kikasan cewar kundin a akwati yake,a tunani na dai bamuyi wannan zancen dake ba,kuma ko a kafar yaÉ—a labarai ba'a faÉ—a ba,taya kika sani?"
Tsareta yayi da ido tareda yimata kallon tuhuma,wanda hakan yasaka jujjuya ido tareda cewa.
"Ehh dama zaka fara yanzu,dan kasamu ma na kula dakai nazo ina tambayarka shine zaka faramin wannan kallon rashin yardar,tun batan Ahmad kakemin irin wannan kallon na rashin fahimta"
"Ohh dama 'bata yayi ba mutuwa yayi ba?"
Gum tayi da idonta tareda nemo abinda zatace.
"Mutuwa nakeso nace,kaima ai kasan mutuwar yayi tunda har gawarsa an kawo maka. Nida wannan abinda kakemin na ƙin raba sirrinka dani kokuma kana tuhumata ka daureni mana kawai ka huta iyee. Kaje cibiyar bincike kace zaka ɗaure matarka dayafiye maka"
Masifah ta cigaba dayi,ta inda take shiga ba tanan take fita,saida tayi mai isarta ta fice daga ɗakin tareda buga ƙofar.
Runtse ido AM Aliyu yayi tareda É—ora hannunsa a kansa.
Yana jin takun tafiyarta har tayi nisa.
Shin me yayi mata kuma wai itace dayin fushi,shine ya kamata ya ɗau mataki amma duk sanda yayi yunƙurin yin hakan sai yaji ya kasa.
GabaÉ—aya gidan mutane uku ne za'a ce daidai,daga Mammah,saleem sai Noor,su kaÉ—aine zaka gansu da sanyin hali. Amma Sameer kam da fatee kana gani kasan ita suka iyo. Shikuwa Ahmad lokacin dayake nan gwanda kowama dashi,domin ko sashensa a can gefe yake,bayason ana yimasa katsalandan,saidai kaima bazai maka ba.
Sannan yanada basira da sanin mai yake,komai shine yake zuwa a fari kafin sauran ,hakanne yasa kullum hankalin hajiyah maryam yana kansa,in za'ayi masa abu ma ita ke shiga da fita ta hana,shikansa yasan da hakan. Shiyasa ko sashenta baya taba zuwa sai yakama dole.
Kaman yadda AM Aliyu bai yarda da ita ba hakama Gen Ahmad,don daff da mutuwarsa ya buÉ—e wani file akan ta,tunda ta tafi kuma babu wanda yasake bi ta kan zancen har yau.
Tsohuwar lauyace mai zaman kanta,duk da yanzu bata aiki,amma kuma tasan takan binciken abinda take son sani sannan kuma da yanda zata gujewa mai son bincikarta. Tana da son mulki da son ganin ana mata hidima,don ko shi kansa AM Aliyu dayake shugaban sojoji bai kaita juya sojojin ba,kuma tanada mutanenta a cikinsu,wanda ko mai tace karsu faÉ—a babu wanda ya isa ya sakasu magana harda shi kansa uban gayyar.
Wannan abubuwan su suka sa kowa hatta Æ´aÆ´an ta suke shakkarta inta juyo ta kansu inka cire Ahmad shikaÉ—ai ne baya tsoronta,kuma shine ciwon idon dayake hanata bacci lokacin dayake raye,yanzu kuwa da baya nan baccinta take sha harda minshari.

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[28]

[Sumaimah a mahangar gani]

Yau kimanin sati guda kenan da zaman goje a bayan garin,kwana uku nayi ina jinyarsa sosai,dakuma kwana dashi. Dagan nanne ya hanani zama sosai,sai Tunga ne yake kwana dashi.
A iya satin kawai har yasamu sauƙi yana tashi dakans,kasancewar dama jikine yasan wahala.
Yau banje wajensa ba,gyaran ƙofar tasa nakeyi,dan jiya da naje yake cemin yau zai dawo gida.
Inna batasan yana garin ba,ita a zatonta daga can wajen aikin zai dawo,dama kuma bayason tasan halinda yake ciki.
Kayan É—akin na fitar dukka wannan tarkacen,iyah katifarsa na bari sai sallaya da kuma akwatin kayansa,sauran shirgin da baza'ayi amfani dasu ba zubarsu nayi,wasu kuma nakaisu É—akin gefen inna..
Wani kuwa nashashi tun safe nake har rana tayi,dana gama na É—ora girki. Yau ba makarantar safe weekend ne sai islamiyya kaÉ—ai,itakuma banje ba.
Saida na gama abincin rana nayi wanka nayi sallah kafinnasamu na zauna,inna sai sannu take jeramin.
Kursiyyah ce ta shigo ƙofar tamu hannunta ɗauke da ɗa kwano,wanda nasan awara ce.
Bayanta ajiye kwanon abincinsu wanda muke zuba musu ta ɗauka,dan dama sun saba yanzu ko magana basayi ɗauka kawai suke....shuru kowa yana ƙofarsa ta ciki na ciki.
Sai bayan la'asar na ɗauko qur'ani kenan zanyi tilawa naji muryar Tunga shida goje,har yanzu duk sanda naji motsinsa ko kuma muryarsa sai gaba yaɗan buga ɗinnan,wanda bansan menene dalilin ba. Tun da rana nake jiran dawowar tasa,har na haƙura tukunna suka shigo.
Ban tashi daga inda nake ba inaji har suka shigo cikin É—akin innan.
Akan kujerar da take ɗakin ya zauna,yasaka kayansa wanda yatafi dasu baƙaƙe.
Gaisawa suke da inna amma kana ganin kasan yasha wahala a tafiyar da suka iyo É—in,yana daurewa ne kada ya nuna rauninsa.
Shi Tunga tun a tsakar gida ya koma,wanda nasan goje yace masa ya tafin.
Ido muka haÉ—a dashi ya kashemin ido guda É—aya ,É—auke idona nayi tareda ajiye qur'anin nafita daga É—akin.
Kofarsa na nufah nasake gyara komai,ruwa na kai a jug mai sanyi wanda shine dama bankai ba kada yayi É—umi.
Hucin numfashinsa nafara ji a bayana,dan dama najiyo takun sawunsa.
A gadon bayana ya kwantar da kansa tareda saƙalo hannayensa ta cikina,tsayawa nayi daga tashi tsayen ina sauraran numfashinsa wanda yake fitar dashi kaman mutum yayi gudu.
"Kinsan nagaji meyasa kika taho kika barni a ɗakin inna,daƙyar fah na iso wajennan"
"Hhhhh sannu toh,a mashin kukazo ne daga can?"
"Uhmm a gashi duk gonakin mutanene a hanyar,sai jijjiga ni Tunga yake tayi a hanya,wajen ciwo yakemin kaman yanzu nayi raunin"
Jin abinda yafaɗa yasa nafara ƙoƙarin cire hannunsa daga kunkumina,amma kuma sai ya sake riƙeni kaman zai maidani ciki.
"Kace wajen yana ciwo,yakamata a duba kar ko ya buÉ—e,sannan ka haÉ—a gumi yakamata kayi wanka kaci abinci,saika sake shan maganin"
Cikin nuna damuwa nake maganar,ai yayi ƙoƙari ma da nice da wannan ciwo bazan iya tashi ba.
Tashi yayi daga bayannawa ya dawo kan katifa ya zauna,ɗakin yake ƙarewa kallo baki buɗe.
"Wow dama É—akinnan yanada girma kaman haka,ban taba saniba saboda shirginsa,gaskiya kinsha aiki sosai na gyarashi"
Ƴar dariya nayi tareda matsawa na cire masa canvas ɗin ƙafarsa.
"Tohh yanzu abinci zaka faraci kokuma wanka zakayi?"
"Uhm bari naci abincin,dan yunwa nake ji sosai,sannan inason shan magani,saboda tafiyar danayi wajen yana min ciwo sosai"
Yaƙarisa maganar harda lumshe ido yana maida numfashi. Ganin yanda yake bansan lokacin dana kai hannuna ba na bude maballin rigar,wajen da ciwon yake nake kallo,hatta fatar cikinsa ma tayi ja,saidai bayyi jini ba alama yafara kamewa kenan.
"Uhm take it easy mana madam,sauri kike har haka ne?"
Yanayin magana na kulada yanda na É—ora hannayena akan cikinsa,saurin janyewa nayi tareda matsawa baya. Me yake damuna ne haka,yaushe na fara É—aukar taba jikinsa ba komai bane ba.
Dariya yakeyimin tareda ƙarisa cire rigar gabaɗaya ya ajiye a gefe.
"Uhm nagode da kulawarki,hakan yana yimin daÉ—i idan naga kin damuwa da halinda nake ciki,sannan karki damu bazan É—auki komai ba dan kin taba jikina,ya hallata a garekine ba shiyasa kika taba ba uhm?"
Ohh kunya ce takamani naji kaman na nutse a ƙasa,maza fa daman sun iya zarar zance.
"Yawwa yanzu naji kayi turanci dama ka iya ne?"
Nayimasa tambayar dan ya manta da waccar maganar,kaman hakan kuwa yayi tasiri,dannaga ya tafi tunani.
"Turanci kikaji nayi,uhm zai iya yiyuwa,dan wani lokacin mutane kan faÉ—a cewar inayi,ko karanta rubutu danake kawai gani nayi ina rubutawa,amma ban tuno makarantar danayi ba kuma"
"Taya ya hakan zai kasance toh?"
"Uhm ta haka mana,zubamin abincin naci inason shan maganinnan"
Zancenne yaƙare a haka na zuba masa abincin kaman yanda ya buƙata.
Har yashiga wanka ya fito ina zaune a ɗakin,dan cewa yayi kada na tafi na jirashi,daga shi sai gajeran wando ya shigo yana goge kansa da,wani ƙaramin ƙyalle.
ÆŠauke kaina nayi,amma sai naji ya zauna a kusadani har muna gogar juna...ohh wannan sabon hali na goje na kasa gane kansa sam.
Mai yasaka na miƙo masa yafara shafawa,shuru mukayi dagani harshi babu wanda yace komai.
Tashi nayi zan tafi ya riƙo hannuna,
"Ina kuma zakije,ni kaÉ—ai zaki tafi ki bari a É—akin?"
"Uhn zan É—ora girkin dare,Sannan ba kace bacci zakayi ba?"
"Oh na tuna,to ki dunga zuwa kina leƙowa akai akai harna tashi"
"Hhhh to shikenan yanzu na tafi?"
ÆŠaga kai yayi kaman baya so,wai dama wannan bawan Allah haka yake ne,kokuma yanzu ya koyi waÉ—annan abubuwan..
Bayan na fito inna tayi mamakin daÉ—ewata a wajen gojen,amma batace komai ba,nima kuma banyi maganar ba.
Ina cikin jajjaga kayan miya naga ya fito daga ɗakinnasa ya fita,ƙananan kayane a jikinsa yana tafiya normal ba wannan bubbuɗawar. Ko ciwonne yasakashi oho..
Tsayawa nayi daga abinda nake na zubawa bayansa ido yana tafiyar,saida yaje saitin zaure ya juyo muka haÉ—a ido.
Kunya ce ta rufeni ganin yakamani ina kallonsa,da hannu yayi min alama nazo,fuskarsa É—aukeda murmushi.
Zatona wani abu zaicemin,sai kawai ji nayi ya sumbaci goshina,tareda É—allamin yatsarsa kuma a wajen duk lokaci guda.
Shafa wajen nayi tareda turo baki.
"Meyasa dana juyo kika É—auke idonki kaman wacce nakamaki kina laifi?"
"Dama zaka iya fita ne?"
"Silly girl na kula wani lokacin idan bakyason bani amsa saiki yimin tambaya koh"
Hannu yakawo zai sakeyimin É—all amma wannan karon na koma gefe ina dariyah,shima murmushi yayi tareda cewa.
"Zanje wajen su dunga ne karsuga shuru bayan sunsan nadawo"
"Banda bawa mutanen gari tsoro"
NafaÉ—a ina komawa cikin gidan da sauri,yanda nasan bazai dawo ya kamani ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.