Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 34 of 40

.....Nasan zakayi mamakin ganin kana abuja amma lokaci guda ka dawo garinku,nice na kawoka,amma ba lallai sai kasan ni wacece ba,duk da niɗin nasanka......kayi ƙoƙarin komawa gidanka kayi jinya ka warke,ta hakane zaka samu damar kulada wannan akwatin da kayi nasarar ɗaukowa,shiɗin abune mai muhimmanci ga ƙasarka da kai kanka a matsayinka na.........
Wajen bai ƙarisa karantuwa ba ta yage shi,da alama wacce ta rubuta ɗin ta faɗi matsayina,amma kuma saita sanja shawara ta yage wajen.
Waiwayawa nayi da idon inda akwatin yake.Ban mantaba shine wanda nake shirin saida raina akansa.
A kwance nake ina tunani,na,rasama mai zanyi.
Cikin dauriyah na miƙe tsaye,hannu nasaka na ɗauki akwatin,amma ko kaɗan na gagara ƙara ko taku ɗaya daga wanda nayi.
Komawa nayi na zauna,wata dabara ce ta faɗomin. Rigata na fara lalumewa,anan naga wayata a cikin kayannawa,number Tunga nayi ta ƙira amma a kashe,tun inayi harna gaji.
Number Sumaimah na ƙira,tana ringing amma ba'a ɗagawa,saida nayi kaman sau uku kafinnaji ta ɗaga.
Shin meyasa na nemeta a É—aya daga cikin waÉ—anda zasu taimakeni lokacin danake neman taimako? Koma dai menene naji daÉ—i dana sametan.

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[26]

[Sumaimah a mahangar gani]

A galabice na shigo gidan,na dawo daga makaranta,kai neman ilimi kam akwai wuyah.
Uniform na fara cirewa sai naji wayar da goje tabani tana ƙara,tunda ya tafi bai taba ƙiraba,iyah Tunga kawai na taba ƙira yakawo mana kananzir.
Ɗauka nayi naga two missed call,goje?? Ni nayi zaton Tunga ne ma ya ƙira.
Tunda ya tafi hadda cewa sati biyu zayyi,abu ana shirin yin wata amma bai dawo,mai kuma zai ƙira yace. Dama yana raye kalau kenan.
ÆŠagawa nayi tareda yin sallama a hankali,yanayin dana ji muryarsa ne yasakani maida hankali kan abin zai ce,idan ba kunnena ne ya samu matsala ba toh nishi naji yana yi.
"Hello Sumaimah kin....ajinahh?"
"Ehh ina jinka mai yasameka,wata matsalarce ta faru?"
"Kinga ki tsaya ki saurareni,kinsan wannann dutsen mai kogo na bayan gari?"
"Ehh ....eh nasani"
"Toh kizo ki sameni a wajen,ki tahomin da abinci da kuma kaya,yawwa sannan ki je chemist zan turo miki sunan wasu magunguna ki tahomin dasu,sannan karki sanar da inna komai"
Daga haka ya kashe wayar,wani bugawa kirjina yayi,yayinda kaina yafara lissafomin abubuwa da dama,shin mai ya sameshi yake cikin kogo,shida yayi tafiya..
Kayan na cire a gurguje na nufi inda abincin mu yake. ÆŠiba nayi a kula na saka a kwando da,hijabi na zura na fita daga gidan da sauri..
Akan hanya chemist É—in yake,magungunan daya faÉ—amin nasiya,harda auduga,plaster da kuma bandaji acikin abinda ya turo É—in, ciwo yaji,shine abinda yafara zuwa kaina lokacin dana siya abubuwan.
Pure water na siyah a É—aya shagon,daga nan na nufi inda yayi min kwatance.
Da É—an tazara wajen da cikin gari,dan haka saida na taka kafin na isa..
Ina shiga wajen na sameshi a kwance akan kayansa,gefensa kuma akwatine da tarin auduga duk jini a jikinsu,idonsa a rufe yake yana kallon saman kogon,inda bashi yayi kwatance ba zan iya cewa bashine bane,don babu wannan gashin fuskar dana sanshi dashi,sannan yayi fari ya rame kaman bashi ba..
Numfashi yake fitarwa hankali ma wahala. Ban lokacin dana isa wajensa ba da sauri,bayan na ajiye kwandon danazo dashi..
Tsugunnawa nayi a gabansa ina ƙare masa Kallo,fuskata ɗauke da damuwa ƙarara,na tunanin shin wanne irin mummunan abune yasameshi haka,sannan kuma yaushe?
BuÉ—e shanyayyun idanuwansa yayi ya É—ora akaina masu kama dana majinyaci.
Nima kallonnasa nake da nawa idanuwan wanda suka cika da ƙwallah,fatar bakina nakeson na buɗe nayi masa tambaya,amma sai rawa suke sun kasa bani haɗin kai.
Hannunsa ya É—akko zai kawo wajen fuskata,amma abinka da dama tsoronsa nake,saina É—an ja da baya.
Murmushi yayi tareda rufe ido a hankali yakuma buÉ—ewa,dimple ne ya lotsa a gefen kumatunsa,dama yanada wannan abin a fuskarsa,amma ba wanda yasani saboda gashin fuskarsa,yanzu daya aske sainaga kaman wani mutum daban aka ajiyemin. Ashe farace fuskartasa kamar jikinsa,saidai bakinsa yayi duhu bakaman sauran fatar jikinsa ba,saboda shaye shayen dayake.
"Duk da ina cikin wannan halin amma tsorona kikeji,shin mai zan iya yimiki a yanayin danake uhm?"
Tari ya fara yana runtse ido,ban san lokacin dana tallafo kansa zuwa jikina,dama gani Allah yayini banson naga mutum a halin jinya. Bare irin wannan,tsayawa yayi da tarin tareda saqala hannayensa ya riƙo kunkumina gam,wanda nasan ciwon dayake jine yasakashi yin hakan,a nanne nima na kulada bandejin dayake cikinsa wanda yayi jajur dashi da jini.
"Sannu sannu,wayyo please ka tsaya barinaje na ƙira mai chemist ɗinnan,wataƙila zasu iya taimakawa"
Ƙoƙarin zare jikina nayi domin na tafi,amma sai naji yasake ƙanƙameni sosai.. Magana yafara cikin gajiyayyar murya.
"Ahahh kada ki ƙiramin kowa,banason kowa yasan halinda nake ciki....kin kawomin abinda na buƙata?"
"Ehh dukka na taho dasu"
"Uhm barina dashi ki gyaramin wajen,jikina ba ƙarfi bazan iya dakai na ba"
"Niiii ban ban....iya ba bazan iya gyara wannan ciwon ba"
"Uhmm zaki iyah mana ko baki iya ba zannunamiki yanda zakiyi,ba wani abune mai wuya ba,taya zaki ƙira kanki matar goje idan kina tsoro uhmm?"
Nidai kurmiya na koma da zancennasa. Saboda kallonsa nake kaman bashi ba.
Tallafah masa nayi ya jingina da jikin dutsen,jikinsa har rawa yakeyi saboda zafin ciwo.
A hakan kuma yasaka hannu ya sunce É—aurin ciwon,wanda matar data kawoshi wajen tayi masa.
Lokacin da yagama suncewar saida na rufe idona saboda yanda wajen yayi jawur kaman É—anyen nama.
"Ohh bazaki iya gani ba,taya kuma zaki iya wankemin idan kika kasa gani?"
"Ya akayi ka samu wannan ciwon haka,a wajen satar ne koh"
NafaÉ—a cikeda jin haushin yana satar,koda yake yaudarar kaina nake,zaman danayi dashine a wannan watannin nafara manta waye shi.
"Uhm a wajenne wani soja ya soka min wuƙa,ina faɗuwa dana bude ido nasamu kaina a wajennan tareda abinda muka je sata ɗin. Sannan ba sata ce wacce kika sani ba,abune na sirri da mutanena ma basu sani ba,shiyasa nace miki kada ki faɗawa kowa ina wajennan ,saidai in yayi yawane ki faɗawa Tunga kinji"
ÆŠaga kaina nayi tareda fitowa masa da abubuwan dayace na kawoÉ—in,naga yanda yake maganar na fahimci lamarin mai tsaurine.
Kaman yanda yafaÉ—a shine yake nunamin yanda zanyi har muka gama rufe ciwonnasa,gumi kuwa ya haÉ—ashi shirkif saboda wahala.
"Gashi sai wahala kakeji,da baka jeba da haka bata faruba"
"Uhm to hakane,amma ni nasamu da sauƙima,tunda abokan aikina kusan duk sun mutu,wanda sukeda rai ma suna hannun ƴan sanda. Wannan akwatin in zaki tafi gida ki tafi dashi ki boyemin,zan kaiwa ƙungiya idan na warke"
"Kace tacemaka yanada muhimmanci,amma meyasa zaka kaiwa barayi,bayan kasan hakan yanada hatsari,dan Allah karka sake komawa wajensu,duk da cewar kaima........uhm ....amma dai kafisu kasaka hakan a ransu"
"Me kikeson fada kika fasa,nima bana kirki bane koh?"
"Ahah nidai bance ba amma dan Allah karka koma,inna bataso"
Hannunsa yasaka na dama ya ballamin akan goshina,nima sai a sannan nakulada yanda na zage inata surutu.."
"Ya karatunki,daga gani dawowarki kenan bakici abinci ba..É—ebomin naji ko zan iya ci"
Ɗan murmushi nayi ina shafa goshinnawa,kafin na ɗebo abincin. Miƙamasa plate ɗin nayi amma naga ya kafeni da ido yaƙi ƙarba..
Har na fara tunanin ko bayason jallof É—in taliyar,saikuma naga ya buÉ—emin baki,wato so yake na ciyar dashi kenan.
Ɗiba nayi a cokalin cikeda kunya nakai bakinsa,ba kunya kuwa shi ya karba yafara ci. Shuru wajen yayi sai numfashinmu kawai,baici da yawa ba ya min alamar ya ƙoshi.
"Naƙoshi bani ruwa,sannan ki cinye sauran,dan naga yunwa kikeji"
Ikon Allah tun É—azu yake cewa yunwa nakeji,yaushe yafara kulada ni haka?.
Maganin dana taho dasu na miƙa masa ya balla,kafin na bashi ruwa ya kora dasu.
Bayan mun gama cin abincin alwala nayi na sallahr la'asar nazo na shimfiÉ—a É—ankwalina,yana kallona harna idar da sallahr,Addu'o'i nayi kafin na juyo na kalleshi..
"Amma tsawon wannne lokaci kayi a kwance"
ÆŠaga min kafaÉ—a yayi tareda cewa.
"Bansani ba,kawai dai abinda nasani shine ranar 23 ga watana march ne aka sokeni da wuƙa"
Zaro ido nayi tareda rarrafowa kusada shi,kenan satinsa guda a sume?
"Sati guda kenan kayi a kwance,dan yau talatinne ga wata"
"Uhm zai iya yiyuwa,kuma da alama wadda takawoni nan wajen har asibiti suka kawoni"
YafaÉ—a yana nunamin hannunsa,inda aka saka masa canular,kaman ma yau aka cireta a jikinsa,kuma wajen akwai takun sawun takalmin mace,harda robobin lemo da ledar cakes.
"Amma wacece haka in tana cikin tawagarku meyasa ta ajiye maka akwatinnan,inaga bataso ka kaiwa kungiyar nan taku"
Dan haka kawai naji banaso ya koma wajensu.
"Hhhhh da alama bakyaso na koma aikina,amma ke ruwanki ne,dan kinga bana iya komai shiyasa har umarni kike bani ko"
"Ahah ba haka bane kayi haƙuri"
Koƙarin tashi nake shirinyi daga wajen,sai kuma naga ya kamo hannuna gam ya riƙe,idonsa ya rufe yana jijjiga kan cikin sauri.
"Ciwon kaina wayyo kaina yana shirin tsagewa ahhhh,bansha wiwi ba,kibani wiwi É—ina......."
Tambayata yake,amma da alama kuma badani yakeba,sambatune kawai na ciwo.
Hannayena na saka a gefe da gefen kannasa na riƙe,Addu'o'i nafara karantowa na neman sauƙi,hannunsa yasaka yana ƙoƙarin ture hannuna,tareda ƙara sautin ƙarar dayakeyi. Yayinda nikuma na riƙe gamm na dawo yi ma a fili,kasancewar jikinsa babu alamar ƙarfi yasa ya kasa ture hannunnawa.
Can bayan kaman wasu mintuna naga yatsaya da jijjiga kan,ina dubawa naga yafara bacci daga zaunen,gyara shimfiÉ—in danaga anyi masa da kayansa nayi,tareda kwantar dashi a wajen.
Tashi nayi na tsaya ina kallonsa,daga yanda yake maganar kaman daman ya san da ciwon kan kuma ya daÉ—e yanayi.
Dannima na sha ganinsa a ɗakinsa ya riƙe kai,kenan shiyasa yake shaye shayen. Har yanzu na gagara fahimtar sa,kowacce rana sainaga wani abu sabo dan gane dashi.
Kayan abincin na É—auka domin komawa gida,zanje na dawo kada inna inna taka bananan.
Karare na gona na É—akko nayi ta jerawa saida na rufe wajen tass kafin na tafi.
Ina shiga gidan muka haÉ—a ido da inna,tun kafin nayi magana ta jefomin tambaya..
"Kekuma daga ina haka kikadawo,É—azu naji motsinki ina tashikuma na bakyanan"
To anan gizo yake saƙar ,shin mai zan faɗawa inna,gashi yace kada na kuskura tasani.Wata dabara ce ta faɗomin.
"Umm uhm inna dama wata Æ´ar ajinmu ce a islamiyya batada lafiyah,kuma ba Æ´ar garinnan bace zuwa sukayi,shine to na kai mata abinci.....sannan inaso na zauna mata kafin ta warke,tunda bakowa wajenta"
"To ikon Allah,dama rashinnaka a garinnan ba daÉ—i,kin kyauta sosai saki faÉ—awa shi mijinnaki a waya"
"Ehh na tura masa message yace ba matsala,yace yana gaisheki ma wajen aikinnasu ne ba a kiran waya ne"
"To shikenan ba matsala ina amsawa,zan shiga anguwa anyi matar É—an marka ta haihu"
"To saikin dawo inna a gaisheta"
Daga nan tabar zancen,dan dama ita macece da bata matsamaka sai tasan mai kake,musamman idan tasan abu kake boye mata.
Kuɗin na ɗauka a cikin wanda Tunga ya kawomana. Kasuwa na tafi na siyo hanta da kuma alayyahu,dama duk wani abunda nake buƙata.
Farfesunta nayi masa da É—an romo na juye a kula,saikuma shayi dana haÉ—a na zuba a flask.
Wanka nayi lokacin rana ta kusa faÉ—uwa.
Pillow na É—auka da sallaya sai butah,a cikin jakar da aka kawomana kayannan na saka su,saikuma kwandon kayan abincin.
Lokacin dana É—auki hanyar wajen ba sawun mutane sosai,Allah ya taimakeni dana É—ebi Æ´an kallo an ganni da kaya nayi bayan gari.
Yanda na rufe wajen haka naje na sameshi,saida na ture kararen kafin na shiga.
A kwance yake yanda na tafi na barshi yanata bacci,da alama maganin dayasha akwai mai saka bacci a ciki.
Ban tsasheshi ba,dana ajiye kayan hannuna wajen na fara gyarawa. Na É—ebe dattin da wanda suka kawoshi wajen suka zubar,da kuma audugar da sukayi ta goge ciwon dasu,harda wanda muka cire muma É—azu.
ShimfiÉ—a sallayar nayi gefe,kasancewar wajen rairayine,awakin mutanene masu kwana a jeji suke shiga wajen da daddare,kokuma almajirai idan suka iyo itace su tsaya su huta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.