Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 16 of 40

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[12]

Hamma yayi kana yasake kishingiÉ—ewa a kan gadon ammin,kallonsa tayi da mamaki kana tace.
"Yau bakada wajen zuwane tun É—azu kake kwance anan?"
"Uhm to kusan,in ma inada shi fah? Inna fita kuce bana zama a gidan,yau kuma na zauna kinamin kora da hali"
"Ohh baban ubaidu yaushe nayi maka kora da hali dan......."
Asiyah ce ta bankaɗo labulen ɗakin ta shigo kanta tsaye babu alamar dakatawa,duk da kuwa taga takalmin babannasu a ƙofar ɗakin.
(Abinda akasari yake faruwa a gidaje kenan,musamman gida irinnamu na hausawa,kaÉ—an suke kiyaye wannan. Sai kaga yaro ya shigo É—aki da gudu kuma iyayensa suna ciki,shin kozai iya arba da abinda bai kamata ya gani ba duk bai dameshi ba sam. Allah yasa mu gyara.)
Fasa cigaba da maganar tayi tana kallon Asiyah.
"Kekuma menene kika shigo kan mutane kaman doki?"
"Uhm wai ana sallama da baba a waje"
"Waye ko halliru mai gerone,dan munyi dashi dama zaizo ya karbi guntun kuÉ—insa"
"Ahah bashi bane,wannan wani bafulatani ne da wata yarinya"
Hantar cikin uwaisu ce takaÉ—a dayaji ance yarinyah,yau kwana huÉ—u kenan da faruwar lamarin tskaninsa da jauro,tun yana tsammanin ganinsa washagarin ranar har ya daina,kwatsam sai gashi.
"Baban ubaidu ƙalau kake kuwa,yanaga kayi wani fayau kaman wanda yaga fatalwa?"
"Ahah bakomai barinaje naji damai yazo"
Daga haka bai sake cewa komai ba ya fita daga É—akin.
Cikin sanɗa kaman wanda kura ke jiransa a zauren yake tafiyah har ya isa ƙofar gidan.
Da jauro suka haɗa ido,saikuma wata yarinya a bayansa butu butu da ita kaman ƴar tashe,wani wandone a jikinta mai kamada ƙanzo,sai wata yagyagygyiyar riga,kanta kuwa ba kitso ba,wani irin gashine kaman sumar mahaukaci.
Ƙiru idonsa ya sauƙa akan ta,aikuwa lokaci guda ta sauya kallon idonta,kamar girarta zata haɗe,wani gurnani take fitarwa daga maƙogaronta kamar kare,ga haƙoranta kamar na kifi saboda tsini. Yanda ubannata yafaɗa kuwa hancin saikace na 'baunar,dan a manne yaka a tsakiyar kumatunta.
Wani jirrr uwaisu yaji daya daÉ—e yana kallonta,ransa kam baya hango masa alkhairi a jikin wannan halittar.
"Kai hauka kakeyi,caca mukayi zaka bani Æ´ar ka ba wannan aljanar ba,dan haka tun dare bayyi maka ba ka tattara ta ku koma inda kuka fito"
Har uwaisu ya juyah zai koma gida jauro ya biyoshi cikin gidan. A filin da matan gidan suke taruwa suka tsaya,da anata hayaniya kowa sai yayi shuru yana kallon uwaisu da kuma É—ab fulani wanda ya biyoshi,ga kuma yarinya a gefensu.
"Dakata uwaisu,mun riga munyi yarjejeniya dakai,kanason É—iyata in kaci cacah,nikuma zaka bani gona idan naci. Yanzu kuma kace bakashon É—iyah,wannan zancen bazai yiyu ba. Ga É—iya nan na kawo maka,koka so kokuma ka so anan zata zauna. Tacemin tanaso ta zauna yanzu koni ban isa fiddata cikin gidanna ba"
Sakin baki uwaisu yayi yana kallon jauro cikeda takaici.
"Ohh a zatonka wannan abun zan aure kenan"
"Niban ce maka ka aureta ba,amma yanzu a wajenka zata zauna,itama dukiyarka ce daka ciyo a cacah. Sannan saida zan faÉ—amaka tanada matsala na aljanu ,ba rayu a cikin mutane ba,amma kace bakason jin komai daga bakina. Yanzu kuma nakawo maka É—iya kace ba haka ba?".
FaÉ—ane ya kaure tsakanin jauro,yana sai ya tafi uwaisu yace saidai ya tafi da Æ´ar daya kawo.
Gurnani sukaji a bayansu irin wanda uwaisu yaji Deejah tayi É—azu a waje.
Kowa idonsa kanta ya koma,in ka ɗauke uwaisu da jauro sauran mutanen gidan basu san ma itace tayi ba,saida suka ga tana buɗe baki,idonta akan kazar inna rammah,wacce aka kawo mata a haihuwar danta na ƙarshe,maimakon ta yanka taci saita barta tana yimata ƴaƴa.
Wata super Deejah tayi akan kazar ta tumurmusheta a ƙasa,kaza tana ihu tana komai haka ta saka bakinta ta tusge kanta,jini faca ya 'bata gaban rigarta.
Jefah kazar tayi a ƙasa tana kallon tana dariyah,wuta ce buuu ta fara babbake kazar. Bayan ta gama babbakewa daukarta tayi ta murmushe gashin jikin,sai turiri take amma ko zafi bataji. Yagar cinyar kazar tayi ta zuge a bakinta,suna nan tsaye suna kallonta har ta gaigaye jikin kazar ta jefar da kayan cikin.
A lokaci ƙalilan Deejah tagama da kazar inna ramman,kowa a gidan ya sandare a tsaye yana kallonta,iya jauro ne kawai abin bai dameshi ba.
"Ke bani ruwa"
TafaÉ—a tana kallon inna ramman,dan dama itace ta kusada ita a zaune. Bata yi motsi ba kana batace komai ba,dan har yanzu abinda ya faru baigama jeruwa a cikin kanta ba.
"Nace ki bani ruwa na sha,ko kema saina babbakeki na cinye kai,wannan ƙaramin naman ba wani ƙoshi nayi ba dama,baba ne yace zai kaini gidan sabon babana shiyasa ban fita farauta ba"
Maganar cikin msifah take yinta kaman tana ganin hanjin mutum.
Da rawar jiki inna ramma ta tashi ta nufi ransa ɗebo mata ruwan,baƙin ciki biyu,an kashe mata kazarta da ko korarta mutum yayi sai taji haushi,ga kuma ƴar ƙaramar ifiritiyar yarinya tana aikanta.
Fizge ruwan Deejah tayi daga hannun inna rammah bayan ta kawo mata,ƙwatt ƙwat take zubawa a cikin harta shanye shi.
Miƙa tayi kafin ta kuma sake kallon inna ramman.
"To kaini ɗakinki zanyi bacci,kece mamata daga yau,ina son mutum mungu naga wani baƙin ɗauri yana bin ruhinki,dan haka ke munguwa ce"
Zaro ido inna rammah tayi,wai anya kuwa ba mafarki take ba,wannan wacce irin aljanace,duk biye biyenta bata taba tunanin zata gamu da aljani ba a ido da ido sai yanzu.
"Bazaki kaini ɗakinnaki bane da kanki,zatonki inna bi baƙin zarenki bazan gano inda kike kwana bane,na miki mutuncine danace ki kaini dakanki"
Sake razana inna rammah tayi da tsawar da Deejah ta daka mata,wuce gaba tayi tana binta har suka je shige ƙofar tasu.
Kowa sauƙe ajiyar zuciya yayi,yayinda kallo kuma yakoma kan jauro,wanda shine silar kawo musu wannan masifah. Ammi ce tayi ƙarfin halin yin magana ganin kowa yarasa bakin cewa uffan.
"Baban ubaidu mai yake faruwa ne,wannan bafulatanin fah,sannan itama waccar aljanar wacece"
Shuru uwaisu yayi yana kallon ƙasa,ta ina zai fara kenan?
Ganin bashida tacewa yasa jauro gyara murya ya jiye musu labarin abinda ya faru,tundaga A har Z,sannan kuma ya ƙara da cewa.
"Da yayi zaton wayo yayi min,ni daka ganni nan nasan caca fiyeda yanda kake zato,da nayi niyyar cinyeka na ɗau gonarka,amma daka naji ɗiyata kakeso da aure saina gano bawai cacar ce a ranka ba,so kake ka cuceni. Nikuwa saina barka kayi nasara saboda na rabu da Deejah. Tunda aka haifeta bamu taba hutawa ba,saboda tsabar ta lokaci guda na tashi naga innarta ta gudu,matar dana auro ma daga baya tace zata zauna,ganin abin yafi ƙarfinta itama ta gudu. Ko yaushe cikin gina bukka muke,bama bacci sabo kar takasa mana wutah,nasha guduwa na barta idan ta shiga daji,amma dayake aljanunta ne suke taimaka mata take tsiya saidai kawai na ganta ta biyoni. To yanzu tunda tace zata zauna a wajenka watan hutawa ta yakama,zanje na ɗau matata da ƴaƴana mucigaba da zama"
Yana gama faÉ—ar haka yafita daga gidan hankalinsa kwance.
Cikeda takaici ammi ta kalli uwaisu bayan jauro ya tafi.
"Yanzu wagari ya waya baban ubaidu,munyi munyi dakai ka daina wannan cacar,manyan unguwa sun yi maka magana,amma kaƙi ji sam. Wato da ƴar kyakykyawace ɗiyar fulani saidai muji zaka aure ya koh,a sanadiyyar cacar nan ka ɗauki ƴar ka ka bawa wancan shashan,kaikuma da a tunaninka saika auro wacce ranka yakeso? Saboda kai kanaso kaga daidai?"
Haɗiye wani abin baƙinciki tayi bayan tayi masa kallon takaici tabar wajen.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.