Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA.txt
Chapter 14 of 40
__***__
"Audu ya dai wajen aikin,naji ance wai ka dawo kenan bazaka komaba"
Uwaisu ya tambayi Audu baffan goje.
"Inakuwa komawa,waccar yarinyar ta rabani da samun arziƙina,tabarni da zaman majalisa da shan lofe"
"Yarinya kuma wacce kenan?"
"Ƴar wajena mana Atika,matar gidance takamata da mijinta,shine fah suka yi mana korar kare gabaɗayah"
"Hhhhhh hoÉ—an kace tayi gado kenan,ka manta yanda kake lokacin da muna matasa,yayanka yayi ta fama dakai,yanzu ma nasan ba sanja sani tayi ba saidai ya ragu kawai,kai anyi yawan duniya fah"
"Jiya ba yau ba ba,ai wannan yarinya uwaisu inaga da damani ta shanye,dan ita bayan halina hadda na uwarta tahaÉ—a ma,nida zan samu na bada itah a cacar ma wani ya É—auka wlh inaso"
"Ahh ba saika jarraba ba,inda mai rabo ai sai ya É—auka,amma kana ganin zata yarda kayi biyan caca da itah,tunda kace gaji ta iyoo to ba fah kasan sai ankai ruwa rana"
"Ehh to kuma kace wani abun,amma dai uwaisu tundaga wannan lamarin ka daina caca koh?"
"Ina kuwa ina nan inayi,yau ma inada wata caca da wani É—an fulani,naji ance bai iya ba so yake ya gwada,wayo zanyi masa muyi,idan nayi nasara saina tambayeshi yabani Æ´ar sa,kasan su fulani da kyau,yanda na rabu da tawa Æ´ar nima saina auro wata a sanadin caca Audu"
"Kai car uba,amma uwaisu kai maƙurane,kana da dabara sosai,kuma kaman wannan sanadin cacar na aure abune mai daɗi da sauƙi,kana cinye mutum saiya baka ƴar sa,babu ruwanka dayimata wata wahala,tunda anriga anyi yarjejeni ya. Muje nima zanga yanda zata kaya,baza'a barni a baya ba sam"
Tashi sukayi da hnazarinsu zuwa sansanin da suke cacar.
Kamar kullum a cike yake da mutane kowa na sha'anin gabansa..
Bayan sun isa wajen da goje uwaisu ya haÉ—a ido,saidai yau ba caca yake ba,a gefe yake da a zaune yana duniyar tunani. Bayan sun haÉ—a ido kowa kawar da nasa yayi kaman baiga É—ayaba,saikace ba surukai bane.
Manga ne a zaune shida dan fulanin suna ta surutu da hausarsa wacce bata fita.
Suma zama sukayi a wajen aka fara dasu.
"ÆŠan fulani so kake kafara caca?"
"Ehh fah,naga abun tana kawo Cede sosai,wani daya ci jiya kawai sai ya É—ebe dukka,nima inason na É—ebe dukka yau"
Kallon kallo sukayi a tsakaninsu su uku,kafin uwaisu yafara magana..
"To shikenan karka damu,idan kayi nasara zaka É—ebe dukka,amma kafinnan mai zaka saka wanda in an cinye ka aka bayar?"
"Uhm zan caka komai amma banda sanuwa,bama bada sanuwa a wannan wasan"
"Ehh to naji,ni zan saka gonata,idan kayi nasara ka É—auka takace"
"Dagaske kake,gona noma babba zaka bani inna yi nacara?"
"Ehh amma kai mai zaka saka,kana da Æ´aÆ´a mata ne?"
"Eh inada Æ´aÆ´a mana,huÉ—u mata sai maza biyu,sauran basa nan suna gurin innarsu,tare muke kaÉ—ai da Deejah,itace kuma babba"
"Uhm to zaka saka Deejah idan nayi nasara ka bani aurenta?"
"Na baka Deejah kabani gona inna ci,kaikuma ka ɗauki deeja inka ci,amma Deejah ƙarama ce,aurenta sai shekarar gaba. Bazatayi aure yanzu ba,amma zanbaka ita wajenka. Saidai Deejah tanada......."
"Kaga tunda ka amince a fara kawai,koda tanada wani masoyin babu shi yanxu sai ni"
"Ba masoyi gareta ba tanada......"
"Bar wannan zancen kayi shi daga baya,yanzu dai a fara"
Mutane kowa hankalinsa wajensu ya koma lokacin da suka fara,ana haka har cinye ɗan fulani a caca,kowa a gun dama yasan uwaisu wayo yayiwa ɗan fulani dan ya auri ɗiyarsa,ko kunya bayaji yarinya ƙarama gashi tsofai tsofai,tausayin ɗan fulani ne ya kamasu ganin cutar da uwaisu yayi masa,saidai kuma babu yanda zasuyi tunda yayarda.
"Yanzu ka cinye Deejah,a wajenka zata zauna kenan?"
Dariyah uwaisu yasaka tareda shafa gemunsa cikin shauƙi,ehh yanzu nine mijin Deejah,zan riƙeta a wajena a nan da shekara ɗaya takai aure"
"Ohh kada ma kayi alƙawarin auren Deejah,nidai tunda na baka ita kanada ikon kayi duk abinda zakayi da itah........uwaishu ya ɗauki Deejah,jauro ya rabuda Deejah,yau zanyi barci na more babu Deejah.....heeho jauro yaji daɗi yau ya rabu da Deejah"
Kokararsa yaja a ƙasa yayi ihu kana ya sheqe da dariyah.
Da mamaki kowa a wajen yake kallon jauro,wanda yake murna da farinciki kaman anyi masa albishir da kujerar makkah.
"Kai jauro Æ´ar ka cefah zaka rabuda itah,amma kuma kake wannan murnar?"
Manga ya tambayeshi cikeda mamaki.
"Ahah Deejah ɗiya ta ce amma nasan Altine wayo tayimin tabani Deejah ta gudu,ni nasan ba jini na ba Deejah,don batayi kama da mutane ba wanga ɗiya,Hoɗan hanci kaman 'bauna fah take,kullum jeji take wuni saboda fitinarta,gata da aljanu masu saka wutar nan,mun take musu gidansu da shanu suka shiga jikin Deejah,sannan uwarta tana duba ƙasa suma suka sake shiga jikin Deejah,kai Deejah dai ba mutum ba kawai,kows ya gudu ya barni da Deejah fah. Nima yanzu na rabu da Deejah shikenan,uwashu ni zani gida na shaida mata,gobe zan kawo maka Deejah,dama kuwa tanason zaman birni. Yanzu saina ajiye jakar kuɗina a ko ina tunda babu Deejah. Hoɗan caca ta rabani da Deejah nikam naji daɗi"
ÆŠora sandarsa yayi a kafaÉ—a ya tafi yana faÉ—a. Wani suman tsaye mutanen wajen sukayi,banda shi uban gayyar dayake jin abin kaman a mafarki.
Bayan wajen yayi tsitt na wani lokaci dariya sukaji an kwashe da itah a bayansu,suna juyawa suka ga ashe gojene.
"Ohh dama wannan baban Deejah da take yawo cikin dare a daji,muma kenan zamu huta masu zaman daji da gamuwa da itah,babu dama karenmu yakama zomo saita tumurmusheshi ta É—auke. Tunda zata dawo cikin gari da zama mayi farauta cikin kwanciyar hankali"
Yana gama maganar ya tashi shima yabar wajen yana dariya,tunda kuwa goje yayi dariyah to abin mai muni ne sosai......
Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[11]
[Sumaimah a mahangar gani]
Kwanci tashi hausawa kecewa a sarar mai rai,yau satina a guda kenan a gidan aurennawa.
Abubuwa da dama sun faru,wanda duk yawancinsu na rashin daɗi ne. Mutanen gidan kaman dama jira suke nazo,kowa ya daina komai a gidan na aikace aikace,inka ɗauke awara kawai da gaji takeyin kayarta. Itama wani lokacin nice ke haɗa wutar,ko dolene ma in mutum yaga abinda nake ya tausayamin kuma yaji haushina,nima haushin kannawa nakeji,to amma ya zanyi. Yanda gaji ta faɗa hakane ita ke ciyar da gidan kusan,nima ta wani wajen inaganin ƙoƙarinta akan hakan.
Dan haka dolene nayimata aikace aikace,duk da kuwa sunyimin yawa,ranar dana gwada cewa bazanyi ba zage zage tafara da gori,wanda duk akan inna mairo ya ƙare. Nikuma tausayin dattijuwar nake sosai,shiyasa nakeyin komai da jikina zai ɗauka indai gaji zata ƙyalemu.
A bangaren goje kuwa bazance lafiya ba,har yanzu babu abinda dai ya haÉ—ani dashi,tunda ba zaman gidan ma yake sosai ba,in ya shigo ma iya karnukansa ne a gabansa. Abinda nake masifar tsoro kenan,hakanne yasaka inna tace ya fita dasu waje.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.