Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA.txt
Chapter 27 of 40
___***___
*Overall military security headquarter division in barrack*
...ABUJA...
Tashi yayi tsaye cikin bacin rai ya buga hannunsa akan desk É—in,wani tafarfasa zuciyarsa takeyi na bacin rai. Ga girma yazo masa amma common case É—aya ya gagara gamawa dashi ya huta?.
Runtse ido yayi tareda cije fatar bakinsa ta ƙasa..
Kallon Gen Saeed yayi wanda yake gabansa a Tsaye.
"Kana nufin kacemin har yanzu baku gano sansanin Wannan ƙungiyar BC ba"
"Eh ranka ya daɗe,har yanzu bamu gano daga inda suke ba,Banida cikekken bayani sosai akan su har yanzu,gashi cibiyar tsaro ta ƙasa Civil security headquarter tana buƙatar karban aikin,saboda wannan a harinnasu na ƙarshe a gwagwalada sunyi babban ta'adi sosai"
"Ta bincike akan su yana tafiyah normal,meyasa yanzu ake samun matsala akai?"
"Ranka ya daÉ—e kafin na karba Gen Ahmad Aliyu Hamma ne yake jan ragamar binciken,to tunda ya rasu kuma......"
Shuru yayi yana kallon fuskar Air mershall Aliyu Hamma,saboda ambaton É—an sa dayayi kar abin ya kasance cikin matsala,saidai kuma ya kula hankalinsa baya kansa sam.
"Shirya min koma gida David,kafin na dawo Ka tabbatar kaida jami'anka kun samo wani abu gameda su,domin banason wanann aikin yabar Military ko kaÉ—an,Civil security bazasu iyah da wannan abinba sam,zan nemi yin magana da president akan lamarin"
Yana gama faɗin hakan ya dashi ya fitah. Babban mutum ne yafara manyanta,amma kuma kasancewar a ƙuruciya ba'a zauna ba,jikin yana nan kaman bana dattijai ba,duk da daman bawai tsoho bane ba.
Combo ɗin motocine a ƙofar office ɗinnsa,yana fitowa ta tsakiyan ya shiga,suka ja zuwa gida.
Babu nisa gidannsa dan haka da wuri ya isa katafaren gidannsa wanda yake da kwarjininsa kaman an jefoshi.
Motocinsa suna shiga gidan na Mrs Aliyu Hamma wato Hajiyah Maryam kuma suna shirin zasu fita daga gidan.
Har an tada motar da take cikin suka tsaya,fitowa tayi daga cikin motar tana kallon A.M aliyu ta cikin farin glass É—in idonta.
Farace tass ƙirar fulani,sannan kuma tanada kamammen jiki,duk da ta ɗan ga jiyah amma jikinta sam bai nuna ba,kana kallonta batayi kama da iyayen da za'a ƙirasu masu sanyin rai ba,dan ko a gidan kowa yasani hatta barrak ɗin,daka shiga shirgin Hajiya Maryam kwanta kaje da kanka ka faɗa hallaka,domin bata barin kota kwana,kowa abinda taga dama take fesa masa,ciki kuwa har shi kansa mijinnata bai isa ba.
Ƴaƴan ta huɗune a gidan Saleem Da Sameer ƴan biyune,saikuma Maimuna da fatima itace ƴar auta. Duk duniya su kaɗai take gani da gashi a rayuwarta,duk da cewar basune kaɗai ƴaƴan A.M Aliyu Hamma ba,yanada wani ɗan Wato Ahmad Aliyu Hamma,shine babban dansa kuma mahaifiyarsa ta rasu. Saidai shima ya rasu sanadiyyar hatsarin mota,shekara biyar dasuka wuce. Wasu sunce a garin ba hatsari bane haɗashi aka akayi,saidai babu wanda ya isa ya ɗago zancen har a yanzu....
Sameer soja ne kaman Ahmad sanda yakesa rai,saidai shi ba'a bangaren bincike yake aiki ba.
Saleem kuma Medical lab scientist ne,yanada sha'awar nazari akan abinda ya shafi bincike,musamman abinda ya haÉ—a da yanayin rayuwar mutane.
Sai kuma Maimuna lawyer ce,saidai ita ba wani cikyakykyiyar lafiya ce da ita ba,tayi aure amma batayi sa'ar miji ba,Allah ya haɗata da shashasha,gata da sanyin hali itada Saleem. Ita kuma fatima wacce ake ƙira da fatee,karatu takeyi,sannan ita halinsu ɗaya da sameer wajen zafin rai,sune suka iyo mahaifiyar tasu wato hajiya Maryam........
Ƙwasƙwas take tafiyah harta iso kusada shi.
"Abban fatee yana ganka ka dawo da wuri haka?"
Shuru yayi baice komai,dan indai abune daya shafi tsaronsa bayayin maganar da itah,saboda shi kansa yasan bai yadda da itah ba sam.Kawar da tambayartata yayi ta hanyar cewa.
"Ina zaki bayan Mammamah batada lafiyah"
"Taro zanje na manyan matan ƙasa,yanada muhimmanci,kar kace komai dan bazan fasa tafiyah ba ma,sai kace kana magana da ƙaramar yarinya,zazzabi ne fah zata iyah kulada kanta ai"
Tana gama faÉ—in hakan bata tsaya tambayar mai ya dawo dashi ba ta yi gaba.
Jijjiga kai yayi ya ƙarisa cikin gidan,shima dama yasan dole sai tayi maganar banza ga mahaifiyar tasa,yarasa meyasa taƙi jinin Mahaifiyarsa,bayan ita kuma kullum cikin son Maryam ɗin take,duk sanda yayi yunƙurin sakinta itace take hanashi har aka kawo wannan lokacin,tun abin yana damunsa har ya daina ma.
Ba sashensa ya nufah ba,sashen mahaifiyar tasa ya nufah,daÉ—in yanada uwa kenan,tunda mata bazatayi aikinta ba....
Sorry amin afuwa kunji labari yayi tsallen kurege ko?? Karku damu zan haÉ—ashi waje É—aya,kuma da sannu zaku gane......
Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[21]
Saida A.M Aliyu yaje kusada sashen Mammah kafin ya yiwa masu take masa baya alamar su tsaya,dan tasha faÉ—amasa batasan yana shiga mata da wasu masu tsaron lafiyarsa wajenta.
Tafiyah yake shi kaÉ—ai har ya shiga falonnata na farko,gabaÉ—aya wajen idan mutum yashiga sai ya É—auka cewar a cikin faÉ—ar gargajiya yake,amma ta faÉ—a a gani. Kasancewarta daman ita Æ´ar sarautar Zaria ce.
Hadimai ne suke ta kai kawo wajen ganin wajen ya kasance tsaff kuma mai ƙamshi da daɗin gani.
Tun a wajen ya cire takalmanta yana taka carfet É—in daya shimfiÉ—e wajen har zuwa bakin turakarta.
Mai aikinta ce ta hannun damansa tayi masa iso kafin ya shiga. Dama da itah sukazo gidan tunda akayi aurenta,kusan itace ma tayi rainon A.M Aliyu.
"Ranka ya daÉ—e tace zaka iyah shiga"
ÆŠaga kai yayi daga nan yasaka kai zuwa cikin É—akin,a zaune take da farin mayafi a jikinta ta lullube ko ina da shi,da kaÉ—an kake gano jar doguwar rigar da take jikinnata. Akan sallayah take hannunta É—auke da carbi,da alama lazumi takeyi..
Tsugunnawa yayi a gabanta tareda kama hannunta ya riƙe,yana masifar son mahaifiyar tasa,sannan baya tunanin akwai ranar dazai daina alfahari da ita,kasancewarta mai dattako dakuma tausayin na ƙasa da itah,shi bai san meyasa matarsa takasa godewa Allah da irin wannan suruka data samu ba.
Murmushi tasakar masa mai taushi tareda dafa kansa,duk da kana ganinta kasan dattijuwa ce,amma kuma a yanayin kallonta bazaka ce ta haifi A.M Aliyu ba.
"Mai samu wannan gwarzon jarumin haka?"
"Mammah wannan case ɗin na BC ya dameni,tsawon shekara bakwai tun Ahmad nada rai shima yayi iya ƙoƙarinsa,amma har yanzu abu ya gagara,mun kasa gano sirrinsu da kuma inda suke"
Murmushi tasake sake masa wanda yakesa yaji duk damuwar sa ta kau.
"Karka damu Abban Saleem komai na duniya a sannu ake binsa,sannan da sannu lagonsu zai karye kuyi nasara akan su,naga a labarai wai sun kai hari Local govt É—in gwagwalada koh?"
"Hmmm haka fah,Gen Saeed ne akan aikin,amma da alama shima abun yafara gagararsa,gashi gwamnati na shirin ɗauke case ɗin daga wajenmu ta maidashi ƙarƙashin Civil security,wanda kuma nasan bazasu iya da aikin ba,yanada hatsari sosai"
Cikeda damuwa ya ƙarisa magana,duk da shi jarumine kuma wanda baya juya ƙasa da wuri,amma ga mahaifiyar tasa shi mai raunine dayake buƙatar tallafinta.
Tausarsa ta dungayi da kuma bashi baki har hakan yayi tasiri a ransa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.