Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA.txt
Chapter 39 of 40
Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[31]
Nice nafara takawa zuwa inda gadon yake,yana kwance an nannaɗe kansa da bandeji da kuma ƙafarsa ta hagun,ganin fuskar tasa nayi kaman mai bacci,amma nasan ba haka bane,a sume yake da babu dama nayi ƙiransa ya amsamin.
Hawayene yake jirarowa a cikin idona,na É—an samu lokaci a hakan kafin inna ta janyeni suka wuce dashi zuwa motar asibitin..
Bayan an sakashi a ciki nice na shiga sai inna,sun turamu asibitin abuja,bayan mun saka hannu a takardar yarda da hakan.
TH suka turamu inda za'ayi masa aikin akannnasa,biyan kuÉ—i kuma yana garemu kenan.
Tafiya muke a cikin motar asibitin,idona yana kan goje wanda yake kwance kaman gawa,ban san wanne lokaci muka É—auka muna tafiya ba,domin ba wannan ne a rainaba,sai jin nafito naji kawai.
Fuskata tayi shabe shabe da hawaye,da suka turashi neurology department É—in ji nayi kaman nabishi mu shiga tare,amma nasan bazasu barni ba.
Waje muka samu muka zauna,a duk cikin mu ukun babu wanda yake cewa komai.
Shikam yah Musbahu tunda yaji cewar abuja zamu taho bai biyomu ba,sai ya koma faÉ—awa sauran yan gidanmu. Tunga ma a halinda yake ciki bazai iya biyomu ba,saboda jikinsa bai hutaba tukunna,saidai yace zai taho gobe da kuÉ—in aikin,wanda nasan a cikin wannan jakar kuÉ—in gojen zai É—auka.
Kaina na kwantar a jikin inna,duniyar tayimin zafi na rasama abinyi,banda bugawa babu abinda zuciyata takeyi,kowanne daƙiƙa tunani nake shin zasuyi nasarar yimasa aikin kokuma ahah.
"Kiyi haƙuri ki saka tawakkali aranki Sumaimah Inshaallah zai tashi kaman bayyi ba,abin kam zai taba miki zuciya,musamman yanda kuka shaƙu dashi a wannan lokacin"
Abinka da wanda ya ciko an rarrasheshi,kuka na rushe mata dashi tareda ƙanƙameta,itama ganin hakan yasa ta juyo tana bubbuga bayana.
A hakan a wajen muka kasance har goshin magriba,in lokacin sallah tayi muyi musake dawowa mu zauna,Addu'a kuwa nayi har bansan abinda nake faɗa ba.ina cikin yin Addu'o'i bayan na idar da sallahr magriba naga sun buɗe ƙofar wajen tiyatar sun fito dashi,da gudu na tashi har ina tuntube na nufesu,dakatar dani sukayi kafin nakai ga inda yake,wata nurse ce ta tsayar dani,tareda yimin alamar nayi haƙuri ba'ason hayaniya kusada shi.
Ɗaga mata kai nayi ina binsu kaman raƙumi da akala har zuwa ɗakin da za'a kwantar dashi ɗin.
Kana ganin yanda suke kasan a cikin nutsuwa suke saboda tsaro,nidai nida inna kallo kawai muke binsu dashi har suka gama.
"Yawwa kece matarsa koh,munyi nasarar janye jinin daya shiga cikin kansa,amma zai ɗau ɗan lokaci kafin ya tashi,kafin sannan muna buƙatarki a office,mama kekuma zaki iya zama a wajensa kafin ta dawo,amma fah banda yin motsi mai sauti sosai.
Toh inna ta É—aga musu kai tareda zama akan kujera a É—akin,yayinda nikuma na bisu office É—in..
Yawanci dai bayanai sukayi tayimin na abinda yafaru,naji daɗi sosai da suka ce aikin yayi kyau zai tashi babu wata matsala. Murmushi nakeyi har haƙorana suna fitowa da sukace zai tashi nan da kwana uku..
"Yawwa sai biyan kuɗin aiki a ƙa'ida saikun biya a fara aiki,munyi muku ne saboda asibitine suka turoku,amma ku tabbatar kun biya xuwa gobe"
"Inshaallah zamu biya doctor mun gode sosai da sosai"
Tashi nayi da murnata zan rafi,sai naji yayi magana ƙasa ƙasa..
"Nikuwa ina nasan wani mai irin fuskar wannan mutumin?"
"Ehh doctor kace me?"
"Ahah bakomai zaki iya tafiya wani hasashe kawai nayi"
Ban kawo komai a raina ba nakoma wajen inna,inaga ba dani yake bama.
Nida ita muka kwana a ɗakin gojen,duk da ma ba motsi yakeba ballantana ya buƙaci wani abun.
Washagari da safe Tunga suka taho shida Musbahu,sun taho mana da kaya wanda zamu buƙata a zaman.
Sannan a lokaci kaÉ—an suka gama cuku cukun biyan kuÉ—in aikin,daÉ—in abu dana miji kenan.
Rayuwar asibitin muka kama gabagaɗi ba kama hannun yaro,a kwana uku dukka munyi su ne ba gajiya,da tunanin goje zai tashi ya buɗi ido kaman koyaushe yacigaba da hidimar sa,saidai me.....anyi kwana huɗu daren na biyar yana shirin shiga ko motsi bayyi ba,wannan abu ya saremin gwiwa fiyeda yanda mai tunani zai tuna. Tun ina kuka a gaban inna ganin tana shiga damuwa yasa nake shiga banɗaki nayi naƙoshi.
Likitoci abu kaɗan su shigo su dubashi,in sun gama gwaje gwajensu saisu ce mana lafiyarsa ƙalau yanzu,ko yaushe zai iya tashi,tun ina yarda dasu yanzu na gane ƙarya suke tunda bai tashin ba..
Jiya naje gida na dawo,damma munyi hutun makaranta,yau kuma inna ce ta tafi gidan gobe zata dawo,sannan tare zasu taho da kawunta daya keso yazo yaga jikin gojen.
Maganganu take bani na ban baki,tareda ƙarfin gwiwar cewar zai tashi,itama yanzu jinta kawai nake tareda cewa toh.
"Ni zan tafi Sumaimah dan Allah kada ki sakashi a gaba kin wannan kukan da daddare ki ƙiyin bacci,shima kin san bazai so ganinki cikin damuwa ba"
"Shikenan inna saikin dawo"
Ban amsa mata yin kukan ba,saboda nasan konace bazanyi ba sai nayi ne"
Bayan ta tafi banÉ—aki na shiga na É—auro alwala,karatun kur'ani nayi na tsawon lokaci kafin bacci ya kwasheni,saida naji muryar wata nurse kafin na farka. Sister Fauziyya ce mai zuwa duba goje,a satin da mukayi a wajen har munyi sabo da itah.
"Ahhh baccine haka kikeyi,ko kin kishingiÉ—a ne bayan kinyi magriba,dan gashi har tara ta kusa"
Zaro ido nayi tareda miƙewa ina kallon gaban wayata,tara saura na dare,nida na kwanta tun huɗu da wani abu.
Wannan wanne irin bacci ne nake haka kaman marar lafiyah,cikeda mamaki nashiga banÉ—aki na sake dauro wata alwalar domin yin sallolin.
Kallonsa nake nayi tagumi,ciwon dayake jikinsa har sun fara warkewa saboda yana samun kulawa,amma shikam yaƙi tashi har yanzu,na daɗe idona biyu har cikin dare.
___***___
A hankali ya buÉ—e idonsa ya daidai hasken yanda zai iya É—auka,kallon farin cilin yake da tunanin mai kuma ya kawoshi nan?.
Tashi yayi ya zauna yana kallon É—akin,asibitine mai ya sameshi aka kawoshi asibiti,koda yake inaga lokacin da motarsa tafaÉ—innan yaji ciwo shiyasa suka kawo shi asibiti.
To amma ina mommah take da Madeena ko hajiya maryam batazo ba yasan su zasu zo.
Gefensa ya leƙa inda wata mace ke kwance ta kifa kanta da gadon tana bacci. Da alama ƴar aikice,ya faɗa a ransa yana yatsine fuska,amma waye zai kawo yar aiki harta zo kusada shi haka..
Tafiya yake a hankali har ya fita daga ɗakin,kasancewar yasan asibitin shiyasa baisha wahalar zuwa bakin titi ba,da sasafene kuwa taxi sai wucewa suke. Wani ya tsayar tareda yimasa kwatancen inda zai kaishi. a cikin motar kallon jikinsa yake tayi ganin yanda yayi baƙi fatarsa tayi tauri,ko yana tsaka da mission iya kaci,haushi abinda yabashi,hakan yasa ya yiwa mai taxi ɗin magana.
"Am malam please ko zan iya ganin wayarka yanzunnan"
"Ranka ya dade wlh ba caji"
"Mts kaga kaini security headquater daga nan"
To yace masa tareda karya akalar motarsa,bayan ajiyeshi shuru yayi saboda bashida kuÉ—i,ganin haka yasa mai taxi É—in cemasa ya barshi kawai,tunda wajen ma ba nisa.
Kai tsaye cikin wajen yashiga office É—in Sadeeq abokinsa,shi anan yake aiki.
Baizo wajen aikin ba,amma dayayi bayani Æ´an wajen sun barshi ya shiga.
Yana nan zaune akan kujera yaji alamar buÉ—e kofar,yana É—aga Kai sukayi ido biyu da Sadeeq,wanda yayi saurin jefar da wayarsa tareda cewa.
"Gen Ahmad Aliyu Hamma"
Cikin rawar murya yana nunashi.
"Kai Sadeeq wai lafiyarka kuwa,ko kaima kaga yanda jikina ya koma kai?"
"Dagaske kaine AA Hamma a gabana wai,duk tsawon shekarunnan a ina kake toh"
YafaÉ—a yana zare idanuwa kaman yaga aljani,duk da sanyin safiya amma gumi yake zubawa.
"Shekaru wanne iri?"
Sadeeq bai bashi amsaba sai nuna masa calander da yayi,wannnan karon Ahmad ne yashiga razanin,saurin riƙe kai yayi tareda saka wata ƙara ta wahala.
"Sadeeq mai yake damun kaina ne,tunda na tashi nake jin kaman zai tsage"
Yana gama faÉ—in hakan ya kwanta a kan kujerar kaman ya suma.
Ganin hakanne yasa Sadeeq ɗaga waya ya ƙiran Abban su Ahmad ɗin,saboda ya sanar dashi abinda yake faruwa..
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.