Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA.txt
Chapter 37 of 40
__***__
"Wayyo Allah nah"
Wani yaro yasaka kuka ana cikin karatu a aji. Malaminne ya tsaya da karatu tareda juyowa yana kallon yaran ajin,wanda yayi kukan ya kalla tareda tambayarsa mai yafaru.
"Kai tashi,miye kake yiwa mutane kuka a aji?"
"Malam Deejah ce ta sokamin wani abu a wuyana"
Tun kafin malamin yayi magana tayi caraff tace.
"Malam bacci yakeyi a aji kana karatu"
Jijjiga kai yayi tareda riƙe kai,ya akeso yayine da wannan tantiriyar yarinya,duk ajin yarane masu shekaru biyar zuwa bakwai,amma ita shekararta kusan sha uku,dukka tafi yaran aji girma. Shi ba abin yace akaita aji sa'anninta ba babu abinda ta iya,in yayi kokarin cewar a koreta kuma abokinsa Musbahu ne ya roƙeshi akan ya barta a ajin.
"Zo nan kizo ki tsaya a gaban aji"
Yafaɗa a zuciye,tahowa tayi tana kallon ƙasa kaman wata ta Allah.
"Karanta min Kul'azubi rabbin nass naji,tunda shi bacci yakeyi ke ai idonki biyu ina"
Wuri wuri tafara da ido alamar bata ma san mai yakecewa ba,sai wuss wsusss takeyi kawai ta bakinta.
Bulalar hannunsa ya É—aga ya zambaÉ—a mata a gadon baya,sake zura mata yayi,aikuwa take ta kwarara ihu.
Ƴan ajinne suka sheqe da dariyah ganin yanda take tsalle tana dadare.
"Malam aradu ya isheka,dan kaga abokaina basa biyoni cikin wannan makarantar taku ne ina ko,wlh zaka fito daga ciki ai saina ƙona ka kurmus mungu kawai,ku kuma ni kukeyiwa dariya koh,idan na dawo gobe sai nayi muku shegen duka"
Tana gama faÉ—an hakan ta fita da gudu daga ajin.
Hanyar gidnasu tanufah tana ihu,duk inda ta shige sai an kalleta,amma ko a jikinta..
Tana yankowa kwanar gidan turuss tayi da suka haɗa ido da Musbahu a zaune a ƙofar gidan.
Raragefe tafara zata shige gidan taji muryarsa.
"Zo nan wato da girmanki kika zagaye anguwa kina kuka kaman mahaukaciya koh?"
Dawowa tayi gabansa ta zauna a ƙasa,har sannan bata daina kukan ba,wanda yasan na iskanci ne bakomai ba.
"Menene me aka miki,iyanzu ba'a tashi daga makaranta ba,meyasa kika taho"
"Haka kawai wannan abokinnaka mai gemun bunsuru sai yayi ta dukana ban masa komai ba,ai aradu dan yaga abokaina basa bina cikin makarantar ne shiyasa yakemin abinda ya dama,da duk saina ƙone makarantar naga tsiya"
Shuru Musbahu yayi yana nazarin maganar tata,tunda yake da ita bata taba maganar wasu abokanta ba sai yanzu.
"su waye abokanan naki?"
"Uhm uhm kona fadamaka baka sansu ba,sannan sunce kada na faÉ—awa kowa waye su.....nidai bazan koma makarantar nan ba"
"Zaki koma mana khadija,makaranta ai yanzu kika fara,saidai in kinaso nayi fushi dake na daina saya miki shayin safe toh,idan nasiyo abuna da daddare ma na daina baki"
Zaro ido tayi,da alama batason aikata abinda yace É—in.
"Zan dunga zuwa toh,amma wlh ni na tsani wajennan banasonsa,nafison wannan ta safen,saidai ita daÉ—ewa ake ba'a dawo gida ba. Kuma ma in gaskiya ne naga Æ´an gidan basa zuwa makaranta,kowa in yace bazaije ba barishi ake saini za'a takurawa"
Kan gari ya gari take maganar tana kuka kaman ance sai ta faÉ—a dole.
"Yau bakiyi wanka ba ko"
"Uhm taya ka gane baka gidan,nasan ma faɗamaka akayi banyi ba,gidannan akwai ƴan baƙin ciki buhu"
Dariya Musbahu yayi jin tambayar tata lokaci guda.ba wai sanin yayi ba,kawai dai yasan idan ya tambaya zaigane tayi ko batayi ba
"Tun bakiyi wanka ba yau babu abin daÉ—i,kuma kika gudo daga makaranta,tashi ki shiga gida."
"Nashiga uku ka bari yanzu zan shiga gida nayi wankan,makaranta kuma bazan sake gudowa ba,amma kacewa abokinnan naka ya daina dukana toh"
Tana gama faɗan hakan tashige gidan da gudu. Dariya Musbahu ya dungayi ganin wauta irinta Deejah. Haka kawai yake tausayinta,yarinyar tana buƙatar tallafi na gyaran rayuwarta,wanda in ba'a taimaka mataba zata tashi kaman gara.
Allah ya gani yayi niyyar inganta rayuwarta daidai ƙarfinsa,gashi kuma wani satin yake shirin tafiya interview na shiga soja,dama ya daɗe yana son tafiyar,sai yanzu yasamu nasara.
Ga kuma wani abu daya gano a wajen Deejah,aljanun da take tareda su ba ajikinta suke ba,zaman ta a jeji ita kaÉ—ai da rashin kula yasa suka zama makusanta fiyeda mutane Æ´an uwanta,shiyasa mutane ke ganinta kaman itmaa ba mutum bace.
Dan haka Maganin dayake tunani bazayyi wuyar yi ba,muddin tana shiga cikin mutane tana alaƙa dasu akai akai,sannan tafara yin karatu musamman na addini akwai alamar zasu iya barinta.
Wanda yasan babu mai iya yimasa wannan aikin sai Sumaimah,indai tana tareda itah zata iya taimakonta,amma ta yaya.
Tana gidan mijinta yaushe zai É—ora mata wani nauyi da bai shafeta ba,duk da yaji ana labarin rayuwar gidan ba kaman daba,shikansa mijinnata yanzu yanada nutsuwa sosai,wanda shima yaga hakan da idonsa a tattare da itah lokacin dataje asibiti.
Ganin abun kaman bazai yiyu ba kawai barin zance yayi a ransa.
Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[29]
[Sumaimah a mahangar gani]
Tun lokacin da Goje ya fita har dare yafara kafin ya dawo,ina kwance akan gadona na ɗakin inna najiyo muryarsa yana ƙirana.
Shuru na É—anyi saida inna tace
"Sumaimah ba ƙiranki yake bane?"
"Uhmm eh"
Kaina a sunkuye naje bakin kofar ɗakin,saidai ban ganshi ba da alama ya yi ƙofarsa.
Dan haka hijabina na saka akan doguwar rigar jikina na nufi ƙofar tasa.
ÆŠakin a bude yake amma baya ciki,da alama yana bandaki,dan haka zama nayi akan katifa ina jiransa.
Ganin yaÉ—an daÉ—e yasa nayi tunanin inaga wanka yakeyi,hakanne kuwa dan shigowa yayi dagashi sai gajeran wando.
Bai min magana ba ya fara shafa mai,nima bance masa komai ba ina nan zaune. Sai bayan yagama kafin yazo inda nake ya zauna,kallona yake kaman mai nazari yakasa cewa komai.
Duk da cewar babu wani wadataccen haske iya na wayarsa ne daya kunna amma ina ganin fuskarsa.
"Meyasa baki bude wannan abunba da kikaga ina wanka?"
Saida yayi magana na kulada ledar da take tsakar É—akin,sakkowa nayi na buÉ—e,tsirene a cikin yaki albasa.
"Lahh ban gani bane shiyasa"
"Uhm toki É—ibama inna kema kuma in zaki ji sai......."
"Wai anya kuwa inna zataji yanzu,dan yanzu muka gama cin abinci,nima kuma gaskiya ba lallai ba,amma barina tafi dashi koh?"
Nafada inason barin ɗakin,danna kula babu wani abu dayake buƙata,kawai ƙirana yayi,sannan yasamu sauƙi sosai bare yace da wani abun zan taimaka masa.
"Ahah tunda kun ƙoshi shikenan ajiyeshi kawai sai kuci da safe"
Na ajiyeshi,ba tafiya zanyi ba sai na tafi dashi kawai ai.
"Uhm naga nima tafiya zanyi to...."
Dariya yayi min tareda cewa.
"Ki tafi inaaa,aikin dawo É—akin mijinki kekam,daga yau ban yadda ki dunga kwana a É—akin inna ba,nan ne É—akinki"
Dumm gabana ya buga,ban taba tunanin hakan nan kusa ba.
Hannuna ya zawo ya zaunar dani a gefensa,wanda hakan yasakani ajiye ledar da take hannunnawa. Kallona yake cikeda sigar damuwa da neman taimako wanda bansan na menene ba.
Hannayennawa yahaÉ—a dukka biyun a cikinnasa,tareda tattaro dukkan wani sauran nutsuwarsa,nima ganin hakan yasa na kafeshi da ido.
"Sumaimah nine na koreki da ɗakinnan a zuwanki na farko,a yau kuma na buɗe baki ina rokon daki zauna a cikinsa,ko kaɗan bawai tilastaki zanyi ki zauna dani ba,illah iyaka ina son hakan. Kiyi haƙuri da abubuwan dasuka faru a baya waɗanda nayi miki,bazan ce ki manta dasu ba,amma please kada ki ƙullaceni akansu. Dan Allah ki zauna dani ƙarƙashin inuwa ɗaya,idan kin amince dani kaman yadda kika faɗa,ki bani damar shiga a rayuwarki a yau ɗin,idan kinga kuma abin yayi miki sauri ki faɗamin zan barki kiyi nazari akai"
Bayan yagama maganar shuru yayi domin yaji mai zance,ganin nayi shuru yasa ya murza hannaye na.
Ajiyar zuciya na saki tareda cewa.
"Ba....bansan mai zance ba takamaimai akan wannan maganar,abinda ya faru da baya ya riga ya wuce wanda dama hakan ake fata a manta dashi. Batun nadawo kwana ɗakinnan kuma idan hakan ka buƙata to dole shi zanyi,saboda gidanka ne kuma ikonka ne,inda kaga dama ka sakani matuƙar bawai cutarwace ta shigaba dole anan zan zauna.
Sannan kana alaƙar aure kuma haƙƙinka ne daman,kaine da baka biɗa ba tunda. Zan iya hanaka idan da a bayane baka ciyardani ba baka tufatar dani ba. Amma a yanzu idan nace baka ɗaya daga cikinsu nayi ƙarya,dan kayimin wanda ban tsammata bama. Dan haka ka buƙaci samun nutsuwa dani na hanaka saboda wai kayimin ba daidai ba a baya bai tasoba"
"Hmmm naji daɗin bayananki,sannan ina jin daɗi a duk lokacin dakika faɗomin matsayin da nake dashi a wajenki,amma a yanzu ra'ayinki na buƙata ba wai matsayina ba,na yanke shawarar son fara rayuwa dake,sannan banason batun musgunawa ko cutarwa yashigo ciki. Shin kina ji a ranki nayi cancantar da zaki iya miƙamin amanar kanki?"
Wannan tambaya ta taba zuciyata sosai,ni wacece da bazan amince ba. Zare hannuna nayi daga cikin nasa tareda saqalasu ta bayan wuyansa,kuka na fara na farinciki,ganin lokaci guda kaman almara Allah ya karkato da hankalinsa gareni,ya kasance namiji mai nutsuwa da ban taba tunani zai zama,idan wani yace a lokacin baya zan kasance a tsakanin kafaɗun goje to zan iya rantsewa ƙarya yake. Amma yanzu sai nake ganinsa kamar yafi sauran mazan garin ma sauƙin kai.
Hannunsa naji yasaka yana bubbuga bayana,mun dan ja lokaci a haka kafin nazare hannayennawa,a yanzu kuma ina kan cinyarsa a zaune.
Naso kafin na bashi kaina kona shirya yin mu'amala ta aure dashi sai yaƙara nutsuwa da kuma sanin addini sosai,amma tunda ya buƙata ɗin zan amince masa,wataƙila hakan yaƙara tasiri wajen gyaruwar tasa.
Ina cikin tunanin naji bakinsa akan nawa,bansan lokacin daya iso kusa har haka ba.
Kwantarni yayi akan katifar a hankali,tareda ƙoƙarin maidani cikin sahun jerin matan aure masu albarka. Lokacin danaji mai afkuwa tana shirin afkuwa saurin buɗe bakina nayi tareda karanto Addu'ar da ma'aiki muhammad (SAW)ya umarcemu dayi,dan nasan gogan koda ya iyata ma bata ita yake ba a lokacin,abune dama da bai dameshi ba yanzu ake ƙoƙarin ganar dashi.
Nasha wahala ba kaɗan ba a wajensa,duk da cewar yayi iya ƙoƙarinsa wajen ganin bai min ta ƙarfi ba,amma halitta ta da tasa ba ɗaya bace.
Bayan komai ya lafah shuru naji yayi lokacin daya gangara É—aya barin katifar,zato na idonsa biyu,saida naji minsharinsa kafin na jijjiga kai,wato a wannan yanayin najasar shi bacci yayi abinsa.
Tashi nayi da ƙyar ina cije baki na ɗaura zanina,jikina banda tsami babu abinda yakeyi,abinka da ban saba wannan dambarwar ba.
Randarsa na leƙa naga akwai ruwa a ciki,godiya nayi ga Allah kafin na ɗiba na nashiga banɗakinsa domin tsaftace jikina.
Lokacin dana fito har baccinsa yafara nisa,ruwan dayake hannuna na yarfa masa,nayi sa'a kuwa ya juyo yana kallona.
"Ka tashi ka tsaftace jikinka,bai kamata ka kwanta da najasa ba,ina ka iya wankan tsarki ko"
Tashi yayi ya zauna yana kallona,ba fuskata yake kallo ba,dan haka sai na bi inda yakalla,kan kirjina idonsa yake,kasancewar iya zaninne kawai jikina..
Hannuna na saka a wayance na tare saboda kunyar data kamani..
"Uhm badai wannan wankan bane da ake wanke bangare bangare na jiki,na iya shi mana,na kanyi innayi mafarkin wata......wanann kam maza dayawa ai sunayinsa..
Meyasa kike kare jikinki,bayan yanzu naga......."
"Am na bar maka ruwa a banɗaki,wataƙila zai isheka"
Da sauri nayi maganar ina nuna masa ƙofah,dariya yayi tareda dan jan hancina,dan ya kula so nake yabar zancen..
Kafin ya dawo kayana mayar tareda yaye zanin kan gadon naÉ—auko wani na saka,duk da yanda jikina yake min magiyar zai kwanta.
Ina kwanciya naji alamar shigowarsa É—akin,yi nayi kaman bacci nake saboda in yayi magana ma bansan mai zance ba..
Ina jinsa ya hawo kan katifar tareda jawoni jikinsa,daga ƙarshema ya ɗora kaina akan kafaɗarsa.
"Saida safe matata,nagode sosai da kyautarki"
YafaÉ—a a hankali tareda sumbatar goshina.
Zanyi ƙarya idan nace hakan bayyimin daɗi ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.