Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 30 of 40

__***__

"Haba Inna yanzu kina nufin nakoma gidan nan wannan yarinyar tana gidan?"
"To ya kikeso muyi,munje wajen boka ance duk abinda zamuyi a banza ne,asiri bazai kamata ba,saboda aljanun dasuke jikinta suna shirin maidata irinsu ma"
Shuru inna ramma tayi tana jin innar tata,jiyah aka rufa mata ɗakinta da zana zata koma kafin damina,da uwaisu yazo haka ya ƙarashi jiransa taƙi binsa su koma,wai dole sai Deejah tabar gidan tukunna..
Shikuwa ya faÉ—amata da yana da yanda zayyi da Deejah,da kowa yayi maganinta shine zai fara,don ko baccin kirki bayayi tun zuwan Deejah rayuwarsa,kullum cikin fargaba yake kar a zo ace masa tayi kaza,wai duk duniyancin da yayi bai taba zuwa wajen Æ´an sanda ba saita dalilin wannan shegiyar yarinyar.
Tattara kayan inna ramma tafara,dan tasan yanda uwaisu yake a wannan halin tsaff zai ce in tana so kada ta dawo.
"Toh yanzu inna yakike so nayi ne,ko roba fah banni da ita in kika ɗauke wanda suke tsakar gida,gabaɗaya waccar ƴar ta ƙona su wai......."
"Kinga ni wannan maganar ta isheni,dama me kike dashi a dakinnaki ne banda wanann tsohon gadon da ru'be da fitsari,in zaki tafi ki tafi"
Ammi tana rabon abinci da tsakar rana taji sallamar rammah ta dawo.
Tana shigowa ko kallon ammi batayiba ta shige ɗakinnata,babu laifi an maida ginin da bulo,amma rufinne dai saidai tayi haƙuri sai a hankali.
Tsayawa tayi a tsakiyar ɗakin tana kame da kunkumi,shikenan wai ta rasa komai kenan,kuma ace tabar ƴar nan bata ɗau fansa ba,gashi inda ta cize ta har yansu yaƙi ya warke,jiyama saida taje asibiti aka yimata wanki..
Hawayen idonta ta share tareda dunƙule hannu tana cije baki,fitowa tayi wajen ammi kawai dan ta samu wanda zai tamka mata.
"Ina nawa abincin naga kin gama rabawa"
"Ban kasa dake ba,saiki bari idan kinyi na dare saki ci"
"Kutus....kina nufin kice baki zubamin ba,wlh saina ci toh"
Wani kwano ta hanga an zuba shinkafar mai kama da dawa saboda jawur da itah,kuma yafi na sauran yaran yawa.
Ammi tana kallonta ta ɗauki abincin amma ko yunƙurin hanata ta ɗauka batayi ba,har ta wuce kufayin ɗakinnata.
Bata daɗe da shiga ɗakin ba Deejah tashigo ƙofar tana wuwwula karan dayake hannunta,rarraba ido tayi akan kwanukan abincin,amma bata ga robarta ba wacce ammi tace a ita zata dunga zuba mata abinci.
"Ina robata take,dan anga na daina cinye abincin yaran gidannan shine za'a É—auke robata to kuwa saina......."
Cikin ƙaraji take magana irin ta tantiran yarannan,ganin haka yasa ammi cikin rawar jiki ta nuna mata ɗakin rammah.
"Na zuba miki ramma ce ta É—auke wai saita cinye"
"Abincinnawa?"
Da gudu tayi ɗakin rammah tana ƙaraji kaman an wullata.
Rammah wacce ta ajiye kayanta a gefe tana cin abinci sai Deejah tagani a kanta,harda matan gidan guda biyu da É—akin,wanda su Æ´an É—akin ramma ne.
Irin kallon da tayiwa uwaisu ranar kawota takeyiwa rammah,ta daddake kaman mai shirin kaiwa farmaki,magana take mai kamada ta birbiri.
"Abinci nahhh abinci naahh kika cinyemin daga dawowarki......dole saikin biyani abincina ko na cinye namanki....yunwa nakeji"
Karkarwa rammah tafara tareda ajiye kwanon Deejah a gefe,sauran matan kuwa da sukaga haka da gudu sukayi waje.
Nufar rammah tayi zata sake cizonta,wani ihu tayi tareda É—aga hannunta sama.
"Tsaya tsaya dan ya rasulullahi kiyimin rai kiyi haƙuri karki sake cizona,bansan abinci bane,amma zan biyaki idan nayi girki,wlh zan biyaki"
Tsayawa Deejah tayi tana maida numfashi jin abinda rammah ta faÉ—a.
"Zaki biyani dole saikin biyani,kuma yanzu Ma ban haƙura,kafff kashin abincin ƴaƴan ki saina cinyeshi yau,yau basuda abinci a gidannan,sannan saina kashe tunkiyarki"
Tana gama faɗan hakan tafita daga ɗakin da gudu,binta rammah tayi a baya itama a guje musamman ganin ta ɗauki wuƙa a inda ammi ta yanka albasa.
Kewayen awaki ta nufah da gudu rammah tana binta tana ihun taimako,kowa fitowa yayi daga ƙofarsa,duk da sunsan bazai wuce wata aika aikar Deejah zatayiwa ramma ba.
Tana zuwa gaban tunkiyar batayi wata wata ba ta soka mata wuƙar a wuyanta,jini ne yafara zuba abinka da dabba da lafiyarta. Faɗuwa tayi a ƙasa tafara shure shure zata mutu,a lokacin ba shiga uku ba in tara ne ma rammah tashiga,dan hannunta aka data ɗora haka ta zube wajen kaman itace.
Musbahu ne wanda yashigo daga masallaci jin abinda ake fada yasa ya nufi kewayen dabbobin,wuƙar hannun Deejah ya fisga wacce take riƙeda itah hannunta yana ɗigar jini.
Juya tunkiyar yayi gabas yayi mata yankan musulunci.
Saida ya tabbatar komai yayi kafin ya tashi ya tsaya,kife Deejah yayi da mari iyah ƙarfinsa saida ta kusa hantsilawa.
"Bance miki kada nasake gani kin kashe abu mai rai a gidannan ba,sannan kuma karki ƙara ɗauke abu ana rabawa ki cinye?"
Riƙe kumatunnata tayi tareda da nuna rammah da yatsa.
"Na kashe mata tunkiyarta meyasa ta cinyemin abincina daga dawowarta,munguwar matace zata cigaba da cutar da mutane,bazan ƙyaleta ba idan tashiga harkata"
Maganar take muryarta babu alamar nadamar abinda ta aikata a cikinta.
"Khadija ina magana kina mayarmin"
Kallonsa take idonta a tsatstsaye,yana ɗaga ƙafa tayi hanyar waje da gudu.
Tun ranar da ta jiwa yaronnan ciwo bayan ta dawo yakamata yayi ta dukanta,tundaga ranar inta ganshi take sanja hanya.
"Meyasa ke daga dawowarki kika shiga harkarta?"
"Iyee na'am ya ake so nayine kam,bani na kawota gidannan ba amma ta addabeni ta takuramin,ta ƙonamin ɗaki,ta kashemin kaza,ta cijeni yanzu kuma ƴar tunkiyar tawa da kashemin itah,ya akeso nayi toh wlh bari maigidan yadawo sai ya biyani aradu"
Bai sake bi takan rammah ba ya jijjiga kai ya bar wajen. Kai dole ma yasan abinyi,inaga a makaranta zai sakata,inaga abinnata hadda rashin sanin yanda mutane suke rayuma.
Toh shikuma mai gidan idan yazo yasan yanda zayyi da inna ramma.

Tunda Musbahu yafita daga kewayen dabbobin,rammah bata tashi daga inda takeba,sai rusa ihu take tana kallon tunkiyarta,wacce take kwance a inda yayi mata maza wuƙa. Majina kuwa ta jata babu adadi...........to ku yanzu me zamu cewa inna ramma,ita tasani koh????

Mu haÉ—u gobe mutanena a gidan malam goje,zai faracin abincin amarya Sumaimah.........

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[23]

[Sumaimah a mahangar gani]

Shinkafa da miyah nayi niyyar yi,saboda nayi amfani da naman da goje yasaka aka kawo,tun safe yaron da Tunga ya hadani dashi yazo yayimin siyayyar duk abinda nakeso..
Sai wajen shaɗaya kafin na ɗora abincin,wanke wankenmu dan kaɗan ne,tun safe na wanke komai na kwanukan da muka bata,shara kuwa in na share ƙofar inna shikenan saita goje.
Bayan na gama shuru nayi ina kallon abincin dana zuba a cikin kulolin,na tafi tunani naji muryar inna a sama na.
"Wani abune ya faru naga kinyi shuru uhm"
Ashe tana kallon tun ɗazu,so nake da ya fita daga ƙofar tasa saina kai abincin,amma yaƙi fita gashi azahar tana shirin,banaso najene ya gwaleni ya koroni,korar dayayimin ranar danazo gidan har yanzu bata bar cikin kaina ba ina tunowa.
"Inna uhm kina ganin zai yarda yaci kuwa? Baice mu dinga yi dashi ba abincin?"
Dariyar dattawa tayi min kafin tace.
"Karki damu Sumaimah Inshaallah zai karba,kuma abincin yayi daÉ—i sosai da sosai,Ba kowane zai kauda kai baiciba,musamman ma kinsan maza da son abinci kuwa?? Idan kinga yafara ci saikiyi masa maganar komawarki islamiyya da kika fadamin kinji,amma fah kada ki fada sai kinga yana cikin yanayi mai kyau,kin gane koh?"
ÆŠaga kai nayi amma kuma saina tuna naga jiya tace zata fadamasa nakoma islamiyyar meyasa ta sanja ra'ayi.
"Amma inna kince fah zakiyi masa maganar karatunnawa?"
"Uhm uhm da nayi niyyar yimasa maganar,amma inaga kiyi masa maganar da kanki zaifi,ta hakane zaku samu fahimta da kusanci a tsakaninku,sannan in kina tambayarsa da kanki hakan zaisaka ya ƙara gane cewa ke ɗin haƙƙinsa ce kuma kina ƙarƙashinsa"
Maganar da tayin ya gamsar dani sosai,yanda take yimin wasu abubuwan har mantawa nake da itah surukata ce.
Ɗaukar abincin nayi akan tire cikin sanyin jiki na nufi hanyar ƙofar tasa. Tun dawowar innan bamu tab'a yin abinci dashi ba,saboda baya zama a gidan sam,ko mai yakeyi oho. Jiyane dawowar sa yasaka yaro yashigo mana da nama kaman ranar farko.
Na buÉ—e baki zanyi sallama sai kuma naji yana wata magana...
.......Me kake nufi ne wai,jiya fah na dawo yace na fasa fita aikin,kuma yanzu kace wai na sake dawowa,hakan bazai yiyu ba sam.akwai wani aikin danake so nayi,ba iya waccanne aikina ba. Idan yin fashin ko satar daÉ—ine shiya je yayi mana,in kuÉ—inkune saina dawo muku da kayanku yana nan ban taba ba.......
Sata fashi..nashiga uku dama fashi yake zuwa idan yayi wannan tafiyar...yaushe yafara fashi?.
"Me kikeyi a tsaye a nan,ko bayan rashin kunyar harda lab'e kika fara yimin"
Saurin tura ƙyauren nayi na shiga ɗakin ina rarraba ido.
A tsakiyar ɗakin na tsugunna tareda ajiye tiren kayan abincin. Da kallo ya bini yana zaune daga shi sai singlet ruwan toka,da kuma baƙin gajeren wando. Ta gefen idona na kulada shigar da take jikinsa,hakanne yasa naƙi ɗaga ido na,fatar bakina rawa take amma kuma na kasa cewa komai.
Matsowa yayi ya dawo bakin katifar yana ƙareni da kallo.
"ÆŠago fuskarki ki kalleni"
Bin umarninsa nayi ta hanyar ɗago idanuwannawa,akan ginannen ƙirjinsa na ajiye idanuwana,ban ƙarisa izuwa fuskarsa ba,magana naji yafarayi,saidai ba irin muryar danaji yana yiwa mutumin dayake waya dashi bace.
"Me kikaji ina faÉ—a a waya?"
"Uhm....uhm zancen fashi kuke da sata"
"Dakyau dama na tsani ayimin ƙarya,to kada ki kuskura inna taji wannan zancen"
"Tohh bazata jiba"
Ɗaga kai yayi alamar ya gamsu da abinda nace. Shuru ne ya gibta,ganin baice komai ba yasa na fara bude kular abincin,a raina ina cewa karka hanani karka ce ka ƙoshi.
Ohh Allah ya amshi Addu'a ta kuwa harna gama zubawa baice komai ba,amma inajin idanuwansa a kaina. Cokali na saka a kan plate ɗin na miƙa masa. Kar'ba yayi ba musu yafara garwaya gabansa yana kaiwa baki.
Ruwa na zuba masa a kofin jug É—in danazo dashi na sake mika masa gabansa,hannunsa ya kawo zai É—auka nikuma ban zare hannuna,hannunmu ne ya haÉ—u dana juna,da sauri na zare nawa ina sake sunkuyar dakai.
"Akwai magana a bakinki meyasa bazaki furta ba,kina bani mamaki,har yanzu na kasa gane kanki,lokacin da banyimiki komai ba kina tsorona,da nayi niyyar yimiki kuma sai kika maida martani"
"Uhm kayi haƙuri a loka......"
"Ahah bance saikin bani dalilinki nayin hakan ba,me yake tafe dake yanzun?"
Dama yana magana haka ta lumana irinna sauran mutane? Tun lokacin dana ke ganinsa a gari kafin zanen ƙaddarata ya ɗinke da nasa ,nayi zaton idan an zo kusadashi kashe mutane yake. Tsaida tunanin danake nayi tareda sanar masa buƙata tah.
"Uhm dama inason komawa makarantar islamiyyah ne,amma ta matan aure"
"Tsawon sanda nake cin karo dake a lokacin baya da kayan makaranta nake ganinki kafin kifara talle,har yanzu bakiyi ya isheki ba?"
Da yayi maganar bansan lokacin dana É—aga ido na kalleshi ba,dama yasanni yana kallona.
Kaman yagane abinda nake saƙawa a raina,murmushi yayi amma ba mai tsayi ba yace.
"Ohh a zatonki bana kulada mutane ne idan suka ga zamu haÉ—a hanya suka juya da gudu,ina kulada ke duk sanda muka haÉ—a ido komawa kike da gudu kibi da wata hanyar,abin yana bani dariya da kuma nishaÉ—i idan naga mutane suna gudu"
"Babu ɗaɗi da kuma nishaɗi ace kana ɗan adam ƴan adam ƴan uwanka suna gudunka,alamar maƙiyine a gujeshi,kana kuma alamar masoyine a kusanceshi a duk inda ya gifta"
Wuuff nasaka hannuna na rufe bakina ina jijjiga kai,Sumaimah kinga ta kanki meya kaiki fadamasa waÉ—annan kalaman.
Runtse idona nayi,na É—anyi wani lokaci,jin bai dakamin tsawa ba ko mari yasa na buÉ—e idona,murmushi naga yanayimin....wannan bawan Allah menene yashiga jikinsa.
"Yanzu ma kin sake bani mamaki,kece mutum ta farko data fara faÉ—amin irin waÉ—annan kalaman bayan inna,zuciyata ta kasu kashi biyu a halin yanzu.....ki tattare kayannan maza ki fitah,batun makarantar kuma zan duba nagani"
Tashi nayi da hanzarina ba bata lokaci na tattare kayan dana shigo na dasu zan fitah,har nazo bakin ƙofa naji muryarsa,inba nasan muryarsa ba bazan ce bane.
"Abincinki yayi daÉ—i,nagode"
Ehh juyawa nayi duk da yacemin na tafin,kallonsa nayi ya saka hannayensa akan kunnuwansa,idanuwansa kuma a runtse kaman yana cikin ciwo,meyasa lokaci É—aya yakoma haka saikace bashi ba?
Nidai fitah nayi daga É—akin zuciyata cikeda mamakin ganin sabbin halayen gojen.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.