Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna
Reading file: SANADIN CACA.txt
Chapter 4 of 40
___***___
Tafiya yake kansa tsaye zuwa cikin dajin,duk da dare da kuma rashin haske,da kuma hanyar duk ciyawa da itatuwa,amma haka yake jefah ƙafafunsa ko jikinsa,kana gani kasan yasan hanyar da yarda ƙafafunsa su kaishi.
Yaɗanyi tafiya mai nisa kafin yafara haɗa hanya yana dafe kai,wani numfashi yafara saki daga cikin ƙirjinsa wanda yake bada sauti mai diri.
A haka yana tafiyar da ƙyar cikin jarumta har ya isa gaban wata bukka ita kaɗai a cikin dokar ɗajin. Buɗe ƙyauren yayi ya faɗa cikinta,ɗakin vaƙiƙƙirin yake anyi masa yabe da baƙin fenti, na shuni,wani buzu ne a tsakar cikin bukkar shima baƙi,bayan haka babu komai a cikin ɗakin.
Faɗawa yayi kan buzun yana riƙe kai,tareda fitar da wani ƙaraji kaman na karshiyah.
Ya daÉ—e a wannan yanayin yana birgima kafin ya fara fitar da wani numfashi mai nauyi.
BuÉ—e idanuwansa yayi wanda sukayi tamkar garwashi saboda jan da sukayi.
Ɗakin ya zubawa idanuwan kaman mai nazari,can kuma sai ya tashi ya zauna. Buzun ya ɗaga ya ɗauki tabar wiwi ya kunna mata wuta,zuƙar hauka yakeyi mata tana shiga cikin kansa na tsawon lokaci.
Kaman an tsikareshi yasake jefar da itah yana riƙe kai,da alama dai wata ƙarace yakeji wanda kunnuwansa basason hakan sam.
Sakin kunnen yayi ya faÉ—i a wajen tamkar matacce,ko numfashi bayayi na kirki...........
Ku nima na shiga ruɗani,mai yasameshi haka,suwaye suka fara yarda da maganar Ragarus🤣🤣🤣.
Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[03]
[Sumaimah a mahangar gani]
Dare yayi sosai,bakajin komai sai ƙarar jemagu da kuma karnuka,wasu na gidanne na yayunmu,wasu kuma na maƙwantane. Banason haushin karnuka ko kaɗan,to amma kuma yazanyi da saurayin kakata,shikansa wanda ake shirin ɗaura ƙaddarata da tasa yafi kowa yawan karnuka a yankinnamu.
Tashi nayi na zauna ina kallon É—akinnamu,ba wani girma ne dashi ba,amma yaran dasuke É—akin Allah yayi yawa dasu,basuda wani takamaimai yawansu,saboda wani lokacin suna raguwa,yayinda wani lokacin kuma yawansu ke haura misali,kaman dai yau.
Dan duk matar gidan da mijinta yake É—akinta nan take koro Æ´ar ta ta kwana,su kwana suna birgima suna fitsari,a barni da gyaran É—akin kullum kaman ibada.
Duk cikin ɗakin nice babba,nayi rayuwa a ɗakin da ƴan matan gidan,a hankali aka fara aurensu har suka ƙare kaff sauran ni kaɗai,saikuma bazawarai wanda suka dawo daga gidan nasu auren amma su basa yarda su shigo wannan kurkukun kwana.
Ba ƙarar haushin karen ko kuma gwartin yaranne ya hanani bacci ba,bace abinda ya faru,tun ɗazu nayi nayi na runtsa amma na gagara,ko nayi niyyar baccin babu abinda nake gani sai fuskar goje mai kama da dodo,inaga kaff gidannamu babu wanda yakaini tsoronsa,bansani ba ashe dashi zan ƙare rayuwata.
Ahh anya kuwa nabari a kaini wajennasa wani satin? Zuciyata wacce take suya tayimin wanann tambayar.
Abu biyu sukazo cikin kaina,shinna gudu kokuma na na kashe kaina?. Dukkansu ba abune mai kyau ba,amma idan na bari aka kaini in shi ya kasheni shikenan na rataya a kansa koh?
Tashi nayi daga kan katifar bayan na É—auke cinyoyin yaran da suke kaina,tsakar gidan na fito ina kallon taurari da kuma farin wata,sukam sunji daÉ—insu sai haske sukeyi,ko yaushe zanga haske nima a rayuwata oho.
Hankalina yana wajen kallon saman saikuma najiyo kaman alamar matsin mutum a kewayen dabbobi na gidan.
Gaba nane naji ya buga,mai mutum kuma yake a tuken dabbobi da tsawon darennan.
Da kaman vazan ƙarisa ba karnaje aljanine nayi gamo,saikuma to zuciya da zon gulma,na dayyi ta maza na nufi kewayen.
A hankali nake tafiya ina sanÉ—a har na iso daidai wajen ta baya,tsugunnawa nayi na kara kaina tareda nutsuwa,domin naji mai ake cewa.
Muryar Inna rammah kuma matar baba ta biyu? Itada inna atika, matar kawu ÆŠahe. Mai kuma suke a kewayen dabbobi da daddare,naga dai in wajen dabbobi ma sukaje sukam babu nasu aciki,awakin ammi ne a wajen sai kuma ragunan mazan gidan da suke kiwo.
Wata zuciyar ce tabani kaddai satar dabbobi zasuyi,ko kuma suyi musu illah,,dan hakan ba wani babbane daga cikin aikinsu ba,daga su har ƴayansu ba mutuncine ko tausayine dasu ba,nikaɗai sai Allah muka san baƙar izayar dana sha a hannunsu,damma wai a hakan basamin wani abun saboda a wajen ammi baba ya damƙani lokacin daya kawo ni gidannan ina ƴar ƙarama,kuma suna shakkarta itada kayanta.
Kaina na ɗaga kaɗan ina leƙawa domin naga wacce akuyah zasu ɗauka,saidai ga mamakina ba akuya suke ɗauka ba,rami sukayi a wajen suna binne wani abu da bansan menene ba.
Can kuma sainaji inna rammah tafara magana.
"Ke wai fah hakanma munyi da gaske,da tuni ƴayan mu suna nan zaune itakuma tayi aure,da ai bamu yarda da zancen Ƴar boka ba,datace mana muddin wannan ƴa tana gidannan to ƴayan mu bazasu auru ba. Naji fah kaman cewa yake ɗazu wai inna gonarsa zai siyar ya kaiwa goje kuɗin,yafasa bashi itah,kiji kayan baƙin asirin da uwartata tayi mata na farin jini ya yaye tahana ƴaƴanmu masu tasowa aure"
"Iyi kuma fah,bare ma ni mai yara ƙanana ai dole na tashi tsaye ki gafah shekarar da muka mata maganinnan shikenan sai ƴayanmu suka fara auruwa kaman ana musu ruwan mazaje daga sama,da kuwa ita kaɗai suke gani da gashi a gidannan,kallon maza sukeyiwa yayanmu"
"Hmm yanzu dai mungama da wanann,muddin yayi aiki to Baban su Hajjo bazai sake yin wani maganar fasa aurenta ga goje ba,suje can in ma babbakata zayyi ya babbaka ta. Itama Deeja(ammi) munafuka saikace bada ita aka haɗa vaki ba lokacin yimata magani na farko,saboda taga duk samarin ƴaƴan ta ita suke so,yanzun kuma dan taga dukkan manyan ƴaƴanta sun ƙare shine tace wai yanzu ba ruwanta"
"Wlh ƙarya take kedai bari asiyanta ta taso yanda take ji da yarinyar nan,tun yaushe ta tashi tsaye idan taga bazata auru ba, to yanzu idan Baban su hajjo yaƙi aurarta ga goje ya zamuyi kenan?"
"Wlh indai wanann kam ya karye toh haukata ta zanyi,yarinya jarabbabiyah ga kyau kaman mayyah irinna uwarta,keda bamu kauda uwar ba ai da yanzu bazamu samu kansa ba,yanda yake son ta kaman zai mutu.....maza ai munafukaine"
"Ko itama mu aikata wajen uwartata ba,duk da bansan Zinarunba amma in haka take kaman ƴarata kam dole zai jauce akan ta,haka suke da ƙira kaman su sukayi kansu"
"Zakuwa mu sanja mata kamanni,ke nifah na tsani Æ´ar nan,menene bamu gani ba a wajen baban hajjo akan ta,indai wannan karon bata bar gidannan ba to kuwa zamuyi babban shiri,in ma Deejah ce yanzu takeson kareta to da ita zamu haÉ—a..........."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.