Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 21 of 40

__***__

[Goje a Mahangar gani]

Daidai misalin ƙarfe 8:00pm na dare na shirya cikin kayan da suka aikomin,wanda shine unform da kowa zai saka na fita aiki.
Bayan nagama saka kayan ɗaya jakar na ɗakko,bindiga ce a ciki sabuwa dal babba mai babban aiki,sai kuma wasu ƙannan bomb guda biyar,sai kuma hula mai tare poison gas guda biyu da kuma wuƙaƙe ƙanana wanda ake sakawa a jiki saboda kota kwana.
Jinjina kai nayi ina mamakin ƙaurin suna irin na wannan ƙungiyar,dole manyan sojojin ƙasa da jami'an tsaro su bazama neman ganin sun wargaza ya kam. Makamansu ko wasu sojojin basu da su. Anya kuwa babu hannun wani babban ƙasa a cigaban ƙungiyar nan. Oho koma menene su suka sani,ni ina ruwana.
Daukar jakar nayi na lanƙaya a bayana,yayinda nake duba agogon hannuna naga lokaci shima duk yana daka cikin abubuwan da suka aikomin dashi.
Bayan na fita daga gidan hanyar bakin gari na nufah,inda jan jira motar dazata É—aukeni.
Banyi minti talatin ba kuwa sai gata tazo,baƙace dal mai numfashi,kota chairman ɗin garinmu bata kaita ba.
BuÉ—e gidan baya nayi na shiga,drivern yaja muka nausa wata hanyar da tayi jejin.
Wannan karon basu rufemin idi ba har muka isa sansani wancan lokacin.
Shiga mukayi cikin wajen,wannan karon ba hanyar da mukabi wancan lokacin muka bi ba,watace daban.
Mutumin daya tabeni a karon farko yauma dashi nayi arba,saidai yanzu suit ne a jikinsa yana hakimce a wata jar kujera,wajen ya ƙawatu kam sosai,babu yanda za'a yi mutum yasan akwai wannan daular anan wajen haka.
Mutanen wajen na kalla mun kusa mu goma sha huÉ—u dukkanmu sanye da kaya iri É—aya.
"Uhm uhm to abokan aiki barkanku da isowa,sabin zuwa kuma muna yi muku barka da shigowa. Dukkanku sabine tunda baku taba haÉ—uwa da ogah na uku ba,saidai wasu a cikinku ba wannan ne aikinsu na farko ba,wasu kuma yanzu zasu fara.
Mun taraku ne saboda akwai aikin dazamu fita yau,saidai inaga bazayyi ba,dan har yanzu jirgin da muke jira ya kawomana kayan aiki da kuma bayanan yanda abin zai kasance bai iso ba.ÆŠaya yaranmu dasuke dajin Kaduna su sunfita aiki,ku kuma sai munga taku alamar."
Zancen banza kenan,dama kawai taramu sukayi su ganmu,shiyasa fah na tsani zama a ƙasan wani.
Tashi nayi na tsaye zan fita daga wajen batareda nace wani abunba.
"Kai goje ina kuma zakaje,inkana shugaba a sansaninka kayi abinda kaga dama,har ka ture wani daga kujerarsa ka hau,to anan karkayi wannan tunanin sam,in mutum a cikinku yana cin ƙasa to nan ta shuri ce"
Juyowa nayi na kalleshi,ohh tsoro yake karna yi wani abun na karbi kujerar sa komai? Har yavani dariya ma.
"Hmm haba ogah da gimanka kafara wannan maganar tun yanzu? Gida dai zantafi,tunda abinda nazo dominsa bazai faru ba"
Sauƙe ajiya yayi ganin ba abinda yake tunanin bane,wanne wawa ne zaizo waje lokaci guda yakai farmaki,ai sai yaga kamun ludayin kowa tukunna.
"Ba tafiya kowa zayyi ba,munada wajen motsa jiki da horo,a can zaku zauna har zuwa lokacin dazaku fita aiki"
Toh hakan bai wani batamin rai ba,dama ina buƙatar hakan,sannan nariga na sallami yarana ma kafin nazo ɗin.
Har mun tashi zamu bar wajen wani ya shigo wajen da sauri.
Gaban wanda ake ƙira da ogah na huɗun ya nufah,ƙusƙus sukayi magana,daga nan sai ya fitah.
"Toh da alama ma basai munyi jiran ba,mission É—inku a yau sai fara,an kawo kayan aiki da bayanan"
Yana faÉ—an hakan ya fitah,kayan aiki kuma,bayan waÉ—anda suka bamu hadda wasu zasu sake bayarwa..
Muna dai nan zaune suka fara shigowa da wasu jakakkanuna daban.

Wasu motocine dogaye masu tafiyah irin cikin sirinnan a jeji,su zamu shiga zuwa garin gwagwalada. Daga nan kuma a sanar damu wa zamu ƙwamushe.
A yanda naji ana faÉ—a wai zamu kai sati biyu kafin mu koma gida,na fadawa Tunga sati guda kuma zanyi,nasan zasuyi ta jiran dawowa ta,gashi babu dama in ana cikin aiki mutum ya yi waya gida.

Littafi na É—aya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na É—aya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[17]

"Kufitar dani a wajennan nagaya muku,akan me banci sisin kowa ba kuce zanyi kwannan cell"
Jijjiga ƙarfen ɗakin uwaisu yake yana ihu maganganu,tunda rana yake wannan abin har dare yayi,ɗazu kamma abinnasa yafi yawa dayaga lallai a nan wajen zai kwana.
Ƴaƴan sa basu tabayin abinda zai kawoshi nan wajen ba duk iya shegensu,sai gashi wata can daba jininsa ba tasaka shi shiga wannan ɗakin.
Wari da zarni duk sun isheshi,tun yana toshe hanci har ya daina yafara zage zage. Abincin da aka turo masa a kwano tunda rana ko kallonsa bayyi ba,dan rainin hankali yana cikin wannan abinma zasu kawo masa abinci. Cigaba yayi da maganganunsa,ganin har yanzu babu wanda ya kulashi a cikinsu,sai kace ma basu san yanayi ba.
"Nace muku ku buÉ—eni na tafi gida,meyasa zaku rufeni anan wajen banyi laifin komai ba,wacce tayi hakan ai yakamata ku kamo bani ba"
"Dama da bamu ganta bane ai muka kamaka,ƴar ka tayi ayyuka laifi a gari ta gudu,a ƙa'idar kame kuma dama idan ba'aga ƴa ba ana iya kama uba ko uwa,in ba'aga miji ba ana iya kama mata. Dan haka bazamu sakeka ba sai ka an biya beli kokuma mun kama ƴar ka tukunna,domin laifukan da tayi da yawa.ta karya jari,ta ƙone ɗaki,ta nakasa yaro,sannan kuma ta kaji da dama"
"Wai inji uban waye yace muku Æ´ata ce ne? In banda munafurci kowa a garinnan yasan kan yawan Æ´aÆ´ana,yasan babu wannan abar a cikinsu,haka kawai ga can ubanta a jeji baza'a kamashi ba saini,da girma na da komai,dan rashin adalci"
"Kaga dan Allah kayi mana shuru,wanne girma gareka,duk garinnan babu wanda baisan irin abinda kake aikatawa ba,naga a irin waɗannan laifinnaka ka tura ƴarka auren goje saboda ka hallaka rayuwar ta. Duk da haka baka saduda ba kake ƙoƙarin cutar ɗan fulani ka aure ƴar sa. Dayake Allah ba azzalumin bawa bane sai ya nuna maka ƙarshenka,indai baka daina abinda kake ba ai bakaga komai bama. Kuma kayi shuru ka cika mana kunne,su wanda suka jigaka a cacar su zo su karbeka mana"
Shuru uwaisu yayi tareda samun waje ya zauna,duk abinda Ƴan sandan suka fadamasa babu ƙarya ko ɗaya a ciki. Taya zaiga laifinsu gaskiya suke faɗa,ƙanana dasu suna cimasa mutunci. Inda yakama girmansa kaman sauran sa'anninsa na anguwa duk haka bazata kasance ba.
Tunowa yayi lokacin da aka kai wani dattijo a unguwarsu gidan kurkuku da É—ansa yayi sata,a ranar muganen anguwa aka haÉ—u harda É—ansa Musbahu aka fito dashi. Amma shi dayake babu wanda yake daraja shi dashi da babu duk É—aya,ko mutum É—aya bai gani ba yazo wajensa. Duk mai yajawo masa banda budurwar zuciyarsa.?
Cikin sanyin jiki ya koma ya zauna a ƙasan cell ɗin,abincin da aka kawo masa ya buɗe,jallof ce cakwaɗaɗɗiyah,baka bambamceta da farar shinkafah inba kaga abin taruhu a jikiba.
Haka yasaka hannunsa ya yasa yakai bakinsa,saida ya runtse ido kafin ya hadɗiye,saboda yanda take faɗa da maƙogaransa kan bazata shiga ciki ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.